Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Monday, 6 August 2018

Dan Wasan Nijeriya "Ahmed Musa" Zai Koma kasar Saudiya da Taka Leda.

Dan Wasan Nijeriya "Ahmed Musa" Zai Koma kasar Saudiya da Taka Leda.



Dan wasan gefe na Najeriya, Ahmed Musa na shirye-shiryen yin kaura zuwa kungiyar Al Nassr da ke kasar Saudi Arabia daga kungiyar Leicester City ta Ingila.

Dan wasan Najeriya Ahmed Musa da ke taka leda a kungiyar kafa ta Leicester City a Ingila zai koma kasar Saudiya da buga kwallo.

Kafofin yadan labaran cikin gida a Najeriya sun ruwaito cewa Musa zai koma kungiyar Al Nassr akan kudi fam miliyan 25 na Ingila.

Rahotanni sun ce Musa zai isa kasar ta Saudiyya a gobe Asabar domin karkare shirye-shiryen komawa kungiyar ta Al Nassr.

Idan har aka kammala cinikin dan wasan, Musa zai zamanto dan wasa mafi tsada cikin 'yan wasan Najeriya da ke buga kwallo a kasashen waje.

Kungiyar ta Al Nassr, na daya daga cikin manyan-manyan kungiyoyin kwallon kafa a Saudiyya.

Ta lashe kofuna 24 a gasa daban-daban da aka yi a kasar da sauran yankunanta.

Musa shi ne dan wasan da ya fara zirawa Najeriya kwallo a gasar cin kofin duniya da aka kammala a Rasha a wasanta da Iceland, inda ya ci duka kwallaye biyu a wasan da aka tashi 2-0.

Ya taba bugawa kungiyar CSKA Moscow kwallo a Rasha inda daga bisani ya koma Leiscester City, ko da yake, ya taba komawa CSKA Moscown a matsayin dan wasan aro daga kungiyar ta Leicester.

No comments:

Post a Comment

Pages