An yanke wa Ronaldo daurin shekara biyu da tarar dala miliyan 3.7
Ronaldo zai biya tarar dala miliyan 3.7, bayan daurin shekaru biyu da kotu ta yi masa. Sai dai kuma ba zai zauna gidan kurkuku ba.
Wannan ya zo karshen kiki-kakar da ake da shi a kotu na tsawon lokaci inda mahukuntan kasar Spain suka zarge shi da kin biyan haraji a lokacin da ya ke wasa a Real Madrid.
Ronaldo dai ya musanta zargin da ake masa. An yanke masa wannan hukunci ne ranar Juma’a.
An zargi Ronaldo da kin biyan haraji har na Yuro milyan 5.7
Ronaldo mai shekara 3 a duniya, ba zai je gidan kurkuku ba, saboda dokar kasar Spain ta ce ko da an yanke wa mai laifi irin wannan hukuncin dauri, matsawar a karon farko ne, to ba zai je gidan yari ba, sai dai ya biya tarar kawai.
Amma kuma maimakon dauri, zai rika biyan wani sabon haraji na Yuro 250 a kowace rana har tsawon shekaru biyun da aka yanke masa, a madadin zaman gidan kurkuku.
Bayan wanna, Ronaldo zai biya tarar dala miliyan 3.7 da kuwa zunzurutun Yuro milyan 5.7 wadanda tun da farko ya ki biya a matsayin tarar da ta sa aka maka shi kotu.
Akwai kuwa tarar wata Yuro milyan daya da zai biya, a matsayin kudin ruwan da suka taru a hannun sa, a tsawon lokacin da ya ki biyan harajin.
Gaba daya dai Ronaldo zai biya tarar Yuro miliyan 19, wadanda idan aka auna su a sikelin naira, bilyoyin nairori ne masu yawa.
No comments:
Post a Comment