Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Tuesday, 12 December 2017

RUWAN KASHE GOBARA! 28



_28_

Jugum ammi tayi tana saurarensu ga kuma sautin kukan ikhlas wanda ya cika falon,
"Kaga hussain kayi hakuri ka mayar da wukar, yanzu me kakeso ayi?" Hassan ya dafashi yana tambayarsa,
"Zan kira dr za azubar da cikin nan kawai" hussain ya bashi amsa,
"To shikenan kirashi" inji hassan,
Tashi hussain yayi ya fita, sai alokacin ammi ta goge hawayen idonta tafara magana,
"Shi hussain yanada wata irin zuciya wlhi,idan ma an hanashi baji zaiyi ba ni bana son a salwantar min da rayuwar ya"
"Babu komai ammi bari dai muga zuwan dr din tukunna sai muji abinda zaice" hassan yace da ammi yana kallon ikhlas cikeda tausayawa,
"Ammi ni da yaya hussain ya barni, nahakura na dauki kaddara domin na tabbatar wannan jarrabawa ce daga Allah, nayi tawakkali kuma hakika Allah yana tare da masu tawakkali domin ya fada mana hakan acikin littafinsa mai tsarki acikin suratul D'alaq, yace
_"'Waman yatawakkal alal lahi fahuwa hazbuh, ma'ana duk wanda yayi tawakkali da Allah to Allah ya isar masa"'_
Dan haka abar maganar zubar da cikin nan haka dan Allah"
Jawota ammi tayi zuwa jikinta ta rungumeta,
"Babu komai ikhlas ni bazanyi miki irin yanda mahaifinki yayi miki ba wato na juya miki baya, a'a nima zan yi kokarin tayaki karbar kaddarar da Allah ya aiko miki, Allah yayi miki albarka, hakika da yawa daga cikin wadanda suke haduwa da kaddarar cikin shege har suke kashe Kansu to ba dan gudun abin kunya suke yin haka ba suna kashe Kansu ne sakamakon kyamata,tsana, cin zarafi da suke fuskanta daga magabatansu,alhalin kuma duk wanda ya kashe kansa to ya mutu kafiri, nikam bazan taba kyamatarki ba yata"
Rungume juna sukayi suna kuka, shi kansa hassan dake zaune shima kwallar yake yi,
Suna nan zaune hussain ya dawo shida wani likita dan tsamurmuri,
Nuna masa ikhlas hussain yayi, nan likitan ya matsa kusa da ita yafara dan duddubata har na tsawon minti goma kafin ya jiyo ga hussain,
"Hussain wannan cikin yawuce ace za a zubar dashi domin yayi kwari, idan kuma muka dage akan hakan to gaskiya zata iya rasa rayuwarta"
"Dr munir yanzu babu wata dabara da zaka iya yimana?"
Girgiza kai dr munir yayi, "wallahi babu hussain domin muna zubar da cikine idan yana wata daya, biyu ko uku amma muddin yakai wata hudu ma bama iya zubarwa saboda hakan zai haifar da matsala balle wannan wanda har yakai watanni shida babu kwana kadan"
"Ok, babu damuwa munir nagode"
Mikewa sukayi da likitan suka fita tare ammi tabisu da kallo,
Hussain ne ya dawo shida mahaifiyar ammi wato hajiya kakarsu,
Ganinsu jugum yasa hajiya cewa "meya sameku ne kamar masu zaman makoki?"
Hussain ne ya sanar da ita duk abinda yake faruwa nan tafara tafa hannu tana salati,
"Kanaji hussaini ita kaddara ana gudunta ne kafin ta zo amma da zarar tazo to hakuri ake yi arungumeta hannu bibbiyu, wannan abu kaddara ce kuma zamu karbeta Allah yasa mu samu sakamakonta gobe kiyama, yanzu abinda zai faru ai duk gidan nan babu wanda yasani ko? To zanbi duk na farfada musu cewar ikhlas babanta aure yayi mata akauye gashi yanzu mijin ya sakota shiyasa ta dawo nan"
"Yawwa hajiya, wannan shawarar tayi" hassan yafada yana murmushi,
"Lallai naka sai naka duk wanda zai rufa maka asiri bayan naka zai biyo" ikhlas tafada acikin zuciyarta,
"Haka yayi Allah ya rabasu lafiya, babu komai mu zamu riketa kuma zamu rike duk abinda zata Haifa zamu zame masa uba" hussain yafada yana goge kwallar data taru a idonsa,
"Allah yayi muku albarka yasake hada kanku"
Shine abinda ammi tafada kawai, fita hajiya tayi duk taje ta farfada agidan cewar ashe ikhlas ciki ne da ita mijinta ya sakota, tun daga lokacin kowa agidan yake bawa ikhlas kulawa gashi abinci kullum ana kawo mata daga kowanne bangare na gidan.
Yanzu ta saki jikinta hankalinta ya kwanta kuma ta murmure tayi kyau sosai, cikin jikinta kuwa sai dada girma yake tamkar wacce zata haifi yan biyu,
Cikinta yanada wata takwas yayunta hassan da hussain suka samu aiki a state government, murna wurinta ba acewa komai, salary dinsu na farko da suka dauka kayan baby's sukaje suka jibgo mata suka iyo mata siyayya mai tarin yawa hatta kayan wasan babyn sai da suka siyo.
Ammi itace take kaita asibiti awu ko hajiya kakarta,duk wanda yaga cikin nata sai ya sake kallonta domin kamar wacce zata haifi yan uku haka yake dan tsabar girma, kulawa sosai ammi da yayyunta suke bata wacce bata samuba daga mahaifinta.
Watan cikin tara da kwana goma ta tashi da nakuda awata ranar juma'a,
Hajiya ammi ta kira suka kira hussain suka dauketa zuwa wani private clinic, suna zuwa ko minti ishirin batayi ba ta haifo santalelen yaronta namiji kyakkyawa dashi fari sol kamar balarabe,
Tunda akayiwa yaron wanka taji nurses din na tambayar ina abban yaron domin suyi masa albishir, gashi sai yaba kyawun yaron nurse din suke tayi, babu abinda kake ji sai,
"Woww, beautiful boy"
"Ba ataba haifar kyakkyawan yaro a asibitin nan mai kyawun wannan yaron ba"
Hawaye tafara fitarwa, tunani take yi aranta yanzu idan yaron nan ya girma ya tambayeta ina mahaifinsa me zatace dashi? Sai tace masa fyade aka yi mata tasamu cikinsa?
Barkewa tayi da wani sabon kukan mai mutukar ban tausayi.

No comments:

Post a Comment

Pages