YayaNa Miji Na page 1-10
Sarah ki rike mutincin ki na diya Mace bawai zamu tura ki makaranta dan ki dinga abin da kika ga dama bane, aa kawai dan muna so ki kara karatun ki kafin yayan ki Ya dawo sannan ina san kisa a ranki kefa matar aure ce ke matar wani ce banda kula mutanen banza danda biyewa professor ki kare mutunciki na diya mace kuma mai aure, ina fatan kin fa himta? Na fahimta baba, amma baba wannan wanne irin mijine ban taba ganiba bai taba ganina ba, murmushi yaii sarah kenan kawai inasan kisa a ranki mujinki yayanki, komai dan lokacine kina zaune wataran zakiga ko waye mujin ki dai kawai ki Kare mutun cin ki, insha Allahu baba, Allah yai miki albarka, ameen baba, gode da wuri zaku wuce kaduna saboda haka kije ki kwanta kiyi bacci da wuri dan ki sami tashi da wuri, shikenan babaa,.
Wani daki stair naga ta nufa tabi wani daki, wata mata na xaune da newspaper a hannun ta, mama sannu da aiki, yauwa yar ta har kun gamaa magana da Baban naki,?eh mama, sarah inasan kibi maganar mahaifin ki duk da nasan gidan da zaki yanzu bawai wani dadin zama zakiji da su ba aamma ki daure jara bawace Allah Ya kaddara miki,.
Mama meyasa kika ce haka, sarah bari yau zan vaki labarin family dinmu yau xakiji komai yau zan sanar miki ko wace hajiya luba,.
Shekaru asirin da suka wuce,.
.
Shekaru ashrin da suka wuce, a zahirin dangin mu ka,idace sai anwa mutun hadin gida wannan abu tun daga kakanni ne, haka muka taso muka gani ana yi, da lubabu dani Zainab uban mu daya uwa kuwa da tashi,mafiyar mu hadin gida aka mata da mahaifin mu,sunyi shekara ammaaa vabu alamar haihuwa sunje asibi aka saida musu baza ta taba haihuwa Ba hakan Ya tada da hankalinta sosai, dole tasa babanmu Ya karo aure, wacce ba dangi ba,amma kwata kwata jinin harira amaryar babanmu bai hadu dana umma Ba kwata kwata ta tsane ta kuma ba dalili,. Kuma hakan yana batawa baba raii amma umma ta nuna ba wani abu, Umma itta kadaice a gun mahaifanta, baban kuma Dan gidan yayan Baban mu ne, haka suke rayuwa tashi daya Allah yaba harira ciki, ba karamin murna mukai ba nina,haka akai ta kula da ciki har yakai haihuwa,ranar hai huwa ta haifi diya mace, ranar suna taci suna LUBABATU,habaici umma tasha ranar hakan yasa zazzabi da alhaji yaji taba da lafiya Ya kaita asibiti nan ake shida masa tna ciki basuyi wani mamaki ba tunda kanyin yadda yaso,.
Umma ranar haihuwa ta haifu ni, ranar suna naci sunan Zainab abu sosai akai shagali haka bba yai ta kula damu cikin jin dadi da godewa Allah,. Har muka girma aka samu makaranta amma lubabatu halin maman ta taiyi, kullun cikin nuna bakin ciki da kwashi, haka mukai ta rayuwa har Allah yayi muka kai mum zalin aure nan aka Tara family aka za,a hadani aure da mahaifin ku wato Aminu, lubabatu kuma da yakubutu duk yayan yayan babanme, amma me haka lubabatu ta dire itta aminu take so inda Yan uwa sukace ba wanda Ya isa sa su canza shawara, tun daga ranar tsana ta shiga tsakanin mu sosai har akai aure,.
Cikin idon Allah har shekara biyar ban sami haihuwa ba, kuma ko a jikin alhaji, a lokacin lubabatu ta haifi danta Na miji wato *ashrim* ran suna munsha guri wai dama dole inyi gado niko ko a jikina tun mijina bai damuba Maye nawa Na damuwa,. Haka rayuwa ta ci gaba .
Har shekra 7ba haihuwa nan nada da hankali sai munje asibiti,muna zuwa kai mun aune aune nan aka sanar ina dauke da ciki wata biyu, abin yaban mamaki ko irin wannan abun da akeji ni banji ba, haka muka dawo jida cikin murna, lokacin lubabatu yayanta biyu dan ittama ta daina haihuwa bisa wasu dalilai, lokacin da ashrin yayi wayo babanshi waje Ya fitar dashi karatu Dan kuwa family dinmu Allah yai musu arziki,.
Ranar da zan haihu aka kaini asibiti nasha wuya daga baya Na haifu ki, ranar suna kikace sunan Mamana, wato Aisha akan yasa muke kiranki da sarah, haka kika taso cikin kulawa, har kikai wayo muka saki makaranta, har Allah yayi gashi kin kammala, tashi daya kuma aka yanke hukuncin hada ki aure da ashrim ba yadda Na iya dole Na hakura, yanzu baxan iya gane ashrim ba ya yake ina yake ya dabi arshi take, duk ban sani ba, Amman ina mai baki hakuri akan ki kula da mujin kibi umarnin iyaye,. Sauke ajiyar zuciya tare da fadin insha allahu, .
Haka ta nufi dakinta jiki a sanyaye,.
.
Tana shiga daki taje toilet tayi wanka sannan tayi alwala tayi nafila, tayi addua game da sabuwar rayuwar da zata shiga, hakan ta kwanta a gado tana tunanin wanne irin Mijine aka Aura mata, zai so ta kuwa, jinin su zai hadu kuwa, Allah ne masani,.
A kaduna kuwa, a unguwa ta federal locas, garine iska Na tashi cikin yanani Na zafi iskarma zafi take fitarwa,. Wani haddaden gidane Na gani na fada da gani gidan masu bugun abujane wato kudi, horn yake iri karfin shi ji yake kamar Ya tashi da gate din Ma Ya huta cikin sauri cikin sauri da rawar jiki haladu Ya bude gate din, yana parking Ya fito ji kake tass Ya dauke wannan tsohun da mari, tsohun da zaiyi sa, an Dad nashi,cikin fushi Ya Fara magana wannan shine huranka inka san bazaka iya aikin kudi ba a gidan masu kudi saika kama gaban ka amma tsabar rashin mutunci kanaji ina horn baka San ka bude mun gate ba idiot, yi hakuri dannan nadan zagaya ne, wannan kai Ya dama ka kus kura ka sake mun haka I will definitely dismiss you, yana kaiwa nan Ya wuce, yo ni dannan kamin wani yare nida ba iyawa nayi ba inadai maka fatan Allah Ya shirya shine kawai,.
Ko sallama babu Ya shiga parlour, da sauri yan matan suka Mike tare da fadin welcome back broz,and happy married life, da sauri dayar tayi daki dayar kuma tayi kitchen,yan iska da ku tsaya mana da kunga rashin hankali, eyya son dina aiba su suka kar zumunba ko rataya ba,a basu ba,zauna muyi magana, OH god mom wannan wanne irin family ne su haka suke suyiwa mutun auren dole naga daii In lokacin auren nan yayi Xanyi amma dole sai ammun aure wannan wacce rayuwace,just imagine mom I don't even know the girl, how she is, is she educated or not, control son, Wlh nima bansoba Amman Ba yadda Na iya dole in hakura, kuma yarinyar da aka baka shegiya ce kawai dan kudin ka itta da iyayenka suka Aura Ma itta, kaidai kawai abin da zan fada ma kabar komai a hannuna yar aikice kawai zasu kawo mana, plz mom kuda yarinyar nan tazu I don't even want to see her face, in ta gaji saita kama hanyar gidan uban ta, weldone son good idea, ninan zan sata a gaba dolenta ta bar gidannnan, Mom zanje part dina bana san damuwa, plz kar a tashen gobe saidai inni Na tashi da kaina, and yes insun kawota gobe kawai a kaita part dinta in suka tambaya game dani kawai kice bana kasar, as you wish son,.
Lubabatu and her family kenan, babban danta ashrim, sai mai bimai, rukayya,tana da aure, then her twins daughter, Mami and minal, wadda zasu gama secondary school,.
Sai ku biyo ni dan jin yadda zata kaya muje zuwa mahaukaci Ya hau kura, mahaukaci Ya fada rigiya yace ni wankana nake
.
Washe gari,
Sarah ce a daki ta gama shirinta ta tattara all her important material, parlour ta nufa, mama, Baba, uncle Yakubu (dad na ashrim inbaku manta ba) goggo falmata, mahaifiyar su yakubu, salam alaikum, walaikumulsalam amarya babbar su goggo ta amsa, kakalle da kanki amsa sallamar wai Dan Allah yaushe zaki tafine? Bazan tafiba saida ke, aa ni sainaci tawa duniyar, gaba daya suka sa dariya, gaida su tayi, uncle Yakubu Ya fara magana, sarah karkiji komai gidana zaki koma da zama anan zaki zauna shima ashrim din yananan part dinku da ban ne duk sanda yaga dama sai Ya koma dake gidanshi, nima ki dauke ni tamkar babanki, murmushi taii tare da fadin insha Allah,.
Babane Ya cigaba, to sarah yau zaki barmu, Allah yai miki albarka sannan karki manta on Monday xaki fara zuwa lecture, duk da ina tunanin shima ashrim din anan yake lecturing,ki kama kanki sarah, mama ce ittama tai mata nasiha sosai, to sarah ga gift din dazan baki ,key motane babanta Ya mika mata cike da murna ta karba, woww dad na gode Allah Ya kara budi ameen, ameen daughter,.uncle yakubune Ya karba, nima in muje akwai nawa gift din, murmushi tai tare da fadin na gode Dad,. Haka akai ta mata nasiha,. Driver xai biyo ki da motar ki, su kuma su Baban naki a tawa zakuje driver zai juyo da itta, ina fatan kin gane? Eh Dad, haka suka mike suka fita waje,. Nan fa hankali Ya tashi kuka take sosai kamar ranta zai fita dakyar aka samu tai shiri,.
A kaduna kuwa, duk suna parlour, bayan Sun gama breakfast, Mom yau Dad zasuzo da matar broz ko? Eh sai akai ya, Wlh mom ina San ganinta ance ta hadu fara ga gashi, ga hankali ga ilimi I really want to see her, mami ce ta karbe ni kuwa bana bukatar ganinta abinda da broz na bayaso nima bana so saboda haka tasha zamanta, haba mami she now our Aunty, she is aunty daii,ke dallah rufewa mutane baki ni bansan halinwa kika dauko ba kaf yayana kice daban, yauwa mom fada mata, but Mom, yimin shiru plz, OK mom, sallamar da akai yasa suka mai da hankalin su ga kofa, rukayya ce, da gode mami tai gunta tana fadin oyoyo Aunty ruky, itta dai minal na zaune dan ranta Ya baci an mata fada, twin din Mama ya kuke ina minal, gata can fushi take wai mom ta mata fada, zamatai a kujera ta gaida mom dinsu tare da fadin akan me take fushi, nan mami ta fada mata,.
To sannu mai kanwar uwa shi wanda akabama baya so saike karan kada miya, ai Wlh bari kuji karku raga mata mutincinta zakuci, but sister ke da aka aura miki Yaya jafar su Aunty haka suke maki,ke ki kiyayen ai nidashi dama munasa juna,yaya kuwa basanta yake ba,. Mikewa minal tayi tabar gurin,.
Mom kinsan fa da goggo falmata za,a zu da kuma Dad muje ai musu girki, fushi nake da babanku ke jekiyi musu girkin in zaki iya, mikewa tayi tana fadin zan iya mom.
.
Sosai sukai gudu a hanya, saboda haka suka iso kaduna wajen 3:30 tun daga jigawa,,horn sukai mai gadi Ya bude gate din motoci uku suka danno kaii, duk suna waje, sunzu tarba, amma gaba daya ransu a hade kamar wasu macijai iya minal ce ke murmushi,.
Da kafar dama ta fito,kallan gidan tayi ta saki murmushi, tana juyawa sukai 8 eyes da lubabatu dake xabgo mata harara, murmushi ta kakalo tabisu da kallo,wowa Mom kinga aunty beautiful, harara Ruky ta zuba mata hakan yasa tai shiru da sauri twin suka karasa sunawa dad dinsu sannu da zuwa, my twin ya kuke? Qlau Dad mun dauka tun jiyan zaka dawo amma shiru, sorry dear, gun goggo Ruky ta nufa suna wasa irin na kaka da jika,gun mom sarah ta nufa tana gaidata amma kamar ba da itta take ba haka suka nufi cikin parlour,tin yanzu jikin sarah yayi sanyi, a parlour suka zauna aka kawo musu lemo da ruwa mai sanyi,ana ta hira itta dai Sarah bace komai ba, hakan yasa goggo ta Fara tsokanarta, Dad ne Ya Fara magana, to sarah ga Yan uwanki nasan baki wani sansu ba tinda bazuwa hutu kike mana ba, wannan itta ce surukar ki wato mom din ashrim, murmushi tai tare da fadin ina wuni, can ciki tace lafiya, wannan kuma kanwar ashrim rukayya tana da aure Nikita jafar kin sanshi ai, murmushi tai tare da fdin eh, ina wuni Aunty Ruky, mikewa Ruky tayi tasa phone a kunne tana fadin hello, wannan kuma my twin darling, yan autana, minal and mami, minal and mami here is your aunt, gaidata sukai cikin fara,a ta amsa, sannan sarah part dinki, shine acan yanzu zansa a kaiki akwai komai dakike bukata no need ki takura kanki, OK dad sannan gift dina nima motar ce gashi sannan in kina bukatar wani abu kimun magana, no gode Allah Ya kara budi, goggo ce ta amsa To amarya sarah a zauna da yan gida lafiya, kinsan ni yau zan koma da driver Dad dinki,.
Lababatu wai ina ashrim dinne? Bayanan, wanna ai iskancine ai yasan da zuwanmu ya fice wayrshi Ya dauko tare da calling number dinshi amma akashe, hakan yasa Ya hakura, sannan yace twin su raka sarah part dinta,.
.
Haka suka nufi part din sai hira minal ke mata itta dai Mami bace kala ba kawai suna tafiya ne, Aunty sarah kinga yayanmu shima very beautiful just like you amma fa yayan bashi da kirki saiya dinga mana tsawa kuma yadinga yiwa yan aiki rashin mutinci wai talakawa ni kuma bana so zaki ce Ya gyara ko? Murmushi taii tare da fadin eh,tunanin take indai kuwa haka halinshi yake topa da sake anya ma kuwa xa je dashi kuwa,sannan kuma kinsan yadda yan mata ke sanshi kuwa, uhmmm kinga yayun kawayena suyi tacewa in basu number dinshi kuma in fada miki ance, Abu bashi da kirki, murmushi kawai tayi minal kina da surutu nima zaki koya mun, laaaa karki koya saboda yaya baya son surutu, murmushi tai dai dai lokacin suka karaso part din a kulle, dafe goshi minal tayi ohhh god, yaya bayanan kenan gashi ban karbo key a gun mom kuma Allah na gaji,tsaki Mami taja tare da juyawa tai tafiyarta, horn din da sukaji yasa sukai saurin juyawa,da sauri mai gadi ya bude kofar, hancin motar shi Ya danno da itta, yehhh ga yayanma,jin ance yaya yasa tai saurin juya baya dan bata San ganin fuskarshima,.
Hade raii yayi a cikin motar kasancewar Ya gansu a bakin kofar ko ba, a fada maiba Ma yasan ittace, da sauri minal taje kusa da motar dashi, zuge glass yayi, yaya welcome, kaga Aunty mu can, mtwssa ce miki nai inda bukatar ganinta ne? Sorry yaya but you are lucky, kallanta yayi alamar tabar mushi gurin, sorry broz key zaka bamu, tsaki yayi tare da mika mata keys din da sauri ta karba tabar gurin, yana mota har suka bude suka shiga, tsaki yaja tare da fitowa Ya nufi wata kofar Ya sa key Ya shiga,.
Babba gidane Dad dinta Ya kashe kudi sosai hakama mom dinta dan sunaji da yar tasu, kallan ko ina tayi, wata kofa ta gani a rufe, minal ce tai magana wannan kofar part din yayana kina shiga zata sadaki da parlour shi, murmushi tai tare da fadin OK Na gane, to Aunty zan wuce in barki ki huta, OK kawai tace,.
Kallan gida taci gaba dayi, stairs ne a gabanta Ya mike, juyawa tayi tabi wani corridor, taga wata kofa kitchen ne, sai store a kusa dashi, murmushi tai tare da fitowa, wani fun ta nufa, babban dining yai mata welcome da fridge a gun, sai gefe wani daki ne,.
Stairs din ta nufa, dakuna ukune a right hand dinta, daki biyu left hand dinta sai wani a tsakiya wanda ta tabbatar nata ne, turawa tayi tare da bismillah ta shiga, wowww ta furta tare da fadin love you my parents, babban gadone na Gani na fada sai madubi dayasha kayan kwalliya sai sif, da side drowers, sai kujera ta hutu da plazma TV,. Ajjiye jakarta tayi tare da cire mayafin ta nufi toilet tayi wanka, sannan tai shiiriin magarib ta sa kayanta ta zauna a sallaya tana lazumi,.
.
Da sallama Ya shiga part din iyayen nashi suna parlour suna xaune, Mom ce ta amsa tare da fadin ka dawo son? Eh mom, Dad sannu da dawowa, yauwa Amman Abubakar kasan baka kyata bako (real name dinshi kenan )yanzu kasan yau zamukawo Ma matar ka amma tsabar rashin mutinci kasa kafa ka fice ko? Kayi hakuri Dad Wlh naje wani uzurin ne, wanne uzuri da Ya wuce ka tsaya kaga wace matar ka, Abubakar ka kiyayi duniya, in kabi a hankali maye duniyar yau in kaine wataran ba kai bane, wataran saidai kaji ana DUNIYA LABARI(NOVEL DINA NA FARKO KENAN )Dan Allah ka rike matar da da amana, insha allahu Dad,a ranshi kuwa cewa yake ta rike kanta da amana daii, Mom ce ta fara magana, Dan Allah alhaji kabi yaronnan a hankali kun mishi dole yabi sai kuma ka sashi a gaba kana mai fada aiba haka ake ba, eh Lallai Ya tabbata ke kike zugashi To Wlh ki kiyayeni luba, a nidai gaskiya nake fada kuma yarinya dole taimun biyayya in taki ta gane kurenta tana kaiwa nan tabar gurin, oho IN Ki riketa tsakani da Allah kinyiwa kanki in kuwa baki riketa da Allah ba zaki gani ai kema kina da yaya mata,.
Kai kuma ina baka shawara karka biyewa mahaufiyar ka Dan Wlh kai zatakai ta baru ni Ba ruwana, sannan ka kula da matar ka, kamaje ka dubata? Aa dad dama wai so nake sai yanzu Tom kaje sannan kuma ran Monday xata fara zuwa lecture abu makarantar kenan,ka dinga kula da itta, Tom Dad bari in wuce,.
Yau ake yinta indai har saina dubata ai kuwa saidai ta mutu, dolema inja mata kunne karta nuna ni mijinta mean skull Karma ta nuna ta sannni, amma taya danni Ba shiga part dinta zanyi ba, yauwa idea zanba minal ta kai mata,.
```washe gari```
Da asubata ta tashi tai sallah tai azukar sannan ta kuma bacci ba itta ta farka ba sai 10:00 kasan cewar yau asabar,wanka tayi, sannan ta fito tasa atamfa tai light makeup, sannan ta fito kitchen ta hada break iya cikinta tunda bata ga mujin nata ba bayan ta gama ta dauki hijab dinta ta nufi part din su mom,.
Suna parlour mom, mami minal, da sallama ta shiga minalce ta amsa, ina kwana mom ?daban kwanaba xaki ganni, bakinta taja tai shiru, minalce ta gaidata,ta amsa, Mom dad bayanan ko, oho Ban saniba, ke barifa kiji nifa bana san kini bibi kinaji banza mai halin uwarta, sannan kuma ke zaki dinga mum gyaran daki daga yau, kafin in sake nemo miki wani aikin, kuma yau zaki fara tinda nasan har yanzu ba,a zama mace ba, inma an zama nasan kwai daya za, a ajjiye mana tunda gado ne hakan aii, itta dai bace komai ba, mamice ta amsa mom kina nufi su basa haihuwa? Eh mana daga daya basa karawa, tab Ai kuwa mudai munasan ganin baby's din broz ba daya ba, yo banda abunki mamina ai saidai wata ta ajjiye mana yara amma Ba wannan Ba,. Minalce ta amsa, Aunty muje kiga dakina, murmushi tai tare da mikewa dan ta gaji daa jin maganganun nasu,.
.
Dakin minal suka wuce, Aunty sarah saifa kina hakuri mom dina haka take amma watarana zakiga ta fara sanki, mami Ma halinta ta dauko amma itta wannan Ba matsala bace zan iya ganar da itta, abun yaba sarah mamaki wai ace Ya tafi uwa hankali kodan ba wani abun mamaki bane,uhmm minal kenan inane dakin mom din, eh muje in nuna miki, haka suka fito sai surutu minal ke mata har suka karaso Sakin mom din, Aunty ga dakin ni zanje parlour nasan yaya Ya kusa zuwa yanzu, to adawo lafiya,.
Kallan dkin tayi Ya hadu komai a gyare amma wai ake cewa ta gyra itta bataga wani abun gyara anan ba,.
Da sallama Ya shigo parlour, aa dana ka tashi? Eh mom ina kwana? Lafiya qlau son, Mom ina breakfast dina? Dining tamai nuni yanaci su minal namai surutu,.
Xama tayi a dakin ta duba nan ta duba can har ta gama abin da zatai,, fitowa tayi tare da jawo kofar, dai dai lokacin mom din ta hawo saman, banza kallo ta watsa mata, na gama mom ni zan wuce part dina, uhmm sannu mai part To bacan din zaki ba kije kitchen ki fara shirin abincin rana, abincin rana mom ina ganin lokacin yayi kusa yanzu 11:00fa nadai fada miki kar ki sake kibar part dinnan har sai kinyi abincin rana tana kaiwa nan ta wuce, tabe baki tayi wannan matar fa saina nuna mata my true colors bata san koni wace ba laifin wani Na shafar wanine, wata zuciyar ce tai saurin ddakatar da itta, aa sarah kamar uwa take agunki watarana sai labari, haka ta sauko ksa dai dai lkacin ashrim Ya gama breakfast ya fice,.
Tafiya yake yana danna wayar shi cikin rusunawa mai badawa flowers ruwa yai kasa yana kwasar gaisuwa inda ruwan ya fantsala a jikin takalmin ashrim, da sauri Ya kalli tsohun mutumin, Dan Allah kayi hakuri yaronnan tsautsayine, tsaki yaja tare da mikamai takalmin wai Ya wanke sannan yaja kujerar dake gurin Ya zauna, cire takalmin Baban yayi Ya nufi fanfo,.
.
Tun daga nesa ta hango baba yana wankin ta kalmi Ya sai wani dirjewa yake makar wani mota, karasawa tayi, ina kwana baba? Murmushi yai tare da fadin lafiya, Baba lafiya kake wanke takalmi haka? Eh mai gidane danma nayi sa,a cewa yayi in wanke ba korata yayi ba, murmushi kawai tayi tare da fadin kawo in tayaka, aa barshi kinji, Ba musu kuwa ta barmai, yana gamawa Ya wuce in yake, kamar yadda Ya cire haka Ya mayar mai, itta kuwat Tana gefe Tana ganin ikon Allah itta dai kawai taga bayan mutun amma bataga fuskarshi ba,tana mamakin irin wannan hali Na wasu masu kudin kamar sarakai, tabe baki tayi tacigaba da zagaye gidan,gerden taje ta zauna Tana kallan wadda ake wakaranar da aiki a gidan, sai wajen 12:30ta nufi ciki tai musu girkin sannan ta wuce nata part din,.
Haka tai tata Xma a cikin gidan ko sau dayabata taba haduwa da ashrim ba, amma sunayin sabani sosai,.
Yau Monday da wuri ta tashi Tana da lecture na 10:00 kafin 9:30ta gama komai sannan ta murza key din motar ta sai Abu,.
Shi kuwa ashrim sai wajen, 10:00ya tafi Dan yana lecture,.
.
Parking motar tayi ta fito Tana kallan schools,school din ta hadu komai yayi kuwa yana harkar gabanshi,.
Jakarta ta dauka da phone dinta sannan ta Fara tafiya, department na mcb take nema,.
Da sauri tasha gabanta dan sarah saida ta tsorata, hiii kema new ce nima haka department na mcb, ance yau prop ash ne zai dauke mu first lecture kuma a hall na 3 by the way sunana hanifa, tunda ta fara zuba sai yanzu tasa pullstop, shiru sarah tayi tana kallanta da gani tana da surutu abinda baya gaban sarah kenan, hiii bakice komai ba, OH sorry sunana Aisha Amman ana cemun sarah, wowww nice name should we go? Yes, but amma hanifa ke waa fada miki wai wama kikace professor ash shine xaima mana lecture yau sannan kuma bshi da mutunci duk a ina kika ji wannan, Mika mata hannu tayi tare da fadin mu gaisa Dan Allah kina jaaaa Na dauka baxaki mun wannan tambayar ba, yayuna anan suke makaranta soo sunsai komai game dashi kuma in fada miki Ya hadu, Dan har fada ake a kanshi, tabe baki sarah taii,basai ka shiga harkar mutunba tukun zai rainama hankaliba, uhmm kedai ki kiyaye, dai dai lokacin suka shigo hall din, a cike hall din yake kana gani kasan yan farkon diba ne ana zumudin skull kafin kaii Ya dauki zafi sai wani jijji dakai kuwa yake ,.
Guri suka samu suka zauna, hanifa sai zuba takewa sarah itta dai saidai tace uhmm eh, aa, wata kyakykyawar duburwa ta nufu inda suke zaune, sallama tai musu tare da Xama sannun ku, sunana hakeela, zaku iya cemun Hakeey, a garinnan nake da xama, kuma ba, a hostel xan zaunaba, (uhmm fadi ba a tambayta ba)mika mata hannu sukai suka gaisa sannan suka fada mata sunan su,..
Hall dinne yai shiru kamar Ba mutane a ciki kamar ba daxun suka cika hall din da surutu ba, jin hanifa tace woww yasa sarah dagowa, yaci fararen suit, farin cover shoe, sai gashin kanshi dake kwalli, taku yake yana waya gaba dayaa har Mazanma sakin baki sukai ,inda wasu yan matan ke gyara mayafi, ana gyara hudar fuska,.
Jufitan na hall din Ya hau Sannan yace tsaya jikin speaker din, cikin harshen hausa Ya fara magana, duk danasan wasun ku Sun iya turanci amma bari in muku a cikin harshen hausa saboda wasu a cikin ku are illiterate basu canci Xama anan ba kawai kaface ta kawo su, in ka bibiya basu wani iya English ba any way, ku sabi a skull dinnan you don't know my rule and regulations, OH kuyi hakuri ku bakine sabusan dukata saboda dole in sanar daku,inna shigo lecture ba surutu in kana so kaji To in bakaso zaka iya fita sabida muddin na kamaka kana wani abun da ban gaskiya zan kuri mutun innace zan kuri mutun bazai kara shigo mum hall ba,.
.
Sannan na biyu bana San surutu a class na tsani ina lecture ana mun surutu, nsan kunsha ji ana fadin a institution Ba ruwan lectures da dalibai, to gaskiya ni da ruwana dan baxanzu in bata lokacina Na ina muka lecture kuna mun surutu ba sanna kuma inna shigo lecture all phone su kasance a kashe,.
Tsaki taja tare da fadin sai kace a secondary, da sauri Ya dago Ya kalleta inda kallo Ya kuma kanta, ittta Ma bata san maganar ta fito ba, hanifa dake kusa da ittaa tuni ta tsure, itta kuwa gabanta ne Ya fadi ksancewar kallan da yake mata, jijjiga kai yayi tare da ci gaba, zaiyi magan kenan wayarta ta Fara ringing, cikin tsawa yace get out please,ganin Tana shirin fita ko hakuri bata sshi ba yasa Ya sauko tare da fadin meet me in my office,. Yana kaiwa nan Ya wuce .
Ai tuni hall akaa fara kace nace ,da sauri Hakeey da hanifa suka nufu inda take,hakeeu ce ta Fara magana, sarah kibi a hankali mutuminnan bashi da kirki kije yana San ganinki ki bashi hakuri komai Ya yace, hanifaa ce ta karba saida Na fada miki Amman daga zuwanki xaki fara haka nidai Ba ruwana, taabe baki sarah tai yanzunma ba zuwa Xanyi ba, aicewa yayi meet me in my office, kuma yace bama jin turanci saboda haka bazan jeba, ai tuni hanifa ta kara hargitse wa, abunma dariya yaba sarah ,.
Cikin fushi yake tafiya wanna wacce yar iska ce mara hankalj take mai haka itta yar gidan uban wace ,.jin ana kiranshi yasa Ya juya wasu Yan matane,.
Da mamaki yake kallan bayanshi wato bama ta biyu shin ba Lallai kuwa indai bata biyu shibazata gane bata da hankali,.
.
Kallan matan yayi sai wani fari da ido suke kamar baru, sir dama zuwa mukayi ka duba mana wannnan assignment din, tsaki yayi bani da time yanzu plz, and yes kuje waccan hall zakuga wata yarinya tasa, purple atamfa da ratsin baki da yellow a giki sannan da coofee a jikin atamfara tasa purple mayafi kuma farace kuce inna San ganinta yanzu a office dina yana kaiwa nan ya wuce,.
Kutmar ubancan wanna wacce yarinyace har sir Ya haddace kayan jikinta kiga fa yadda Ya lissafo kamar tana nan, Hafsat kenan kina mun wannan tambayar ai yanzu zuwa zamuyi muga wacce itta ta fimu haduwa ne ko me? Kuma mu zamu kirata Ma kuma Ma niban taba ganin sir yace wai a kira masa wata ba,look muje kawai, haka suka nufi hall din, tundaha nesa suka hngo ta dan wannan kwatancen dole a ganeta tashi daya, sai hanifa sai jaaa mata kunne suke ,.
Cikin isa suka karasa gun da suke tsaye, kwashewa da dariya sukai tare da fadin jambies, wai fa ku fasa kaiii kuke level one ko, Lallai kuwa kuna da aiki,.
Hakeey ce tai magana, Ai shiyasa muka ga muda yan wasu level din duk sanmakan saboda baxaa gane Yan wanne level bane gara kaii za, a iya tantancewa wasu kuwa saidai a dauka remedial suke,.
Zaro ido sukai ke mu kike fadawq haka kinsan ko mu suwaye, koma su waye kansunne basu kamaba, any way me yakawo ku nan? Shiru sukai suna nazarin abin yiii,.
Cikin fushi suka juya suka fice,. Sai a office din ashrim,.
Ku Cigaba da Ziyartar wannan Shafi domin cigaban wannan Littafi dama wasu da dadan Littafan.
www.ArewaRulers.com
WhatsApp: 08161892123
No comments:
Post a Comment