Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Friday, 29 June 2018

Babu Abinda Kiristanci Ya Tsinanamin, Inji 'Yar Tsohon Gomnan Oyo

Babu Abinda Kiristanci Ya Tsinanamin, Inji 'Yar Tsohon Gomnan Oyo.


Sananniyar 'yar jaridar nan me yawan jawo cece-kuce kuma diya a gurin tsohon gwamnan jihar Oyo, Kemi Olunloyo ta bayyana sha'awarta da shiga addinin musulunci, tace babu abinda addinin kiristanci da take kanshi a yanzu ya jawo mata banda dimuwa da rudani.

Kemi ta bayyana hakane a wani rubutu da tayi a dandalinta na sada Zumunta da muhawara inda ta sanya hotunan ta sanye da Hijabi sannan ta rubuta cewa:

Kwanannan zata karbi addinin musulunci, kuma a da ta kasance tare da kakarta wadda ta rasu tana da shekaru dari da biyu a Duniya, makarantar da take zuwa kusa da gidan kakartane shi yasa ta koma can da zama, su kanyi sallah sau biyar a rana ba sau daya a sati ba kamar yanda take yi tare da shaidanun mutane yanzu ba, tace, suna shagulgulan sallah babba da karama tare.

Tace Musulunci addinine na zama lafiya kuma a cikinshine zata samu nutsuwa.


Ta dai karkare zancenta da cewa, yanzu babu ruwanta da addinin kiristanci, dan kuwa babu abinda ya tsinana mata a rayuwa banda rudani, musulunci zata koma kuma duk wanda baya son addinin musulunci sai ya dena bibiyarta da lamurranta, komai yana da lokaci dama, yanzu dai ta tabbata cewa a addinin musuluncine zata samu nutsuwar da take nema.

5 comments:

Pages