ASUU Za Ta Fara Maganar Yajin Aiki Bayan Sun Kasa Cin Ma Matsaya Da Gwamnatin Tarayya.
ASUU za ta fara maganar yajin aiki bayan sun kasa cin ma matsaya da Gwamnatin Tarayya
Bisa dukkan alamu dai abubuwan ba su tafiya daidai tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya wato ASUU bayan da Kungiyar tayi barazanar za tayi watsi da duk wani shirin sulhu da ake yi da Gwamnatin kasar.
Gwamnatin Tarayya da ASUU sun gagara cin ma daidaito
Malaman Jami’a na kasar ba su yi amanna da Dr. Wale Babalakin, da aka nada a matsayin Shugaban kwamitin da Gwamnati ta shirya su zauna da Kungiyar ASUU ba.
An nada kwamiti ne domin a duba yarjejeniyar da aka yi a 2009.
A jiya Talata ASUU ta tabbatar da cewa zaman da ake yi da kwamitin Wale Babalakin ya rushe saboda kwamitin na nunawa Malaman Jami’o’i na Najeriya taurin-kai.
ASUU tace kwamitin da aka kafa bai da niyyar cin ma matsaya.
ASUU ta fadawa Ministan ilmi na kasa Adamu Adamu cewa suna iya shiga wani sabon yajin aikin idan har aka gaza yin sulhu tsakanin ta da Gwamnatin Tarayya.
Shugaban Kungiyar na kasa Biodun Ogunyemi shine ya bayyana wannan.
Tun a farkon 2017 ne ahugaba Buhari ya kafa wani kwamiti na Gwamnati da zai zauna da Kungiyar ASUU domin magance sabanin da ake samu a da.
An shirya kammala zaman ne cikin ’yan kwanaki amma har yau ba a cin ma matsaya ba.
Bayan wani taro da aka yi kwanan nan a Garin Kalaba, Kungiyar ASUU tace tabbas Dr. Wale Babalakin bai da shirin ganin an yi sulhu.
ASUU dai ta zargi Kwamitin Babalakin da kokarin nunawa Malaman makarantun kasar ba su iya ba.
ASUU tace kwamitin da aka kafa bai da niyyar cin ma matsaya.
No comments:
Post a Comment