Saraki Ya Kira Taron Gaggawa Na Shugabannin Majalisa.
Saraki Ya Kira Taron Gaggawa Na Shugabannin Majalisa
Harkokin Gwamnati Za Su Tsaya Cak Idan Majalisa Ba Ta Dawo Daga Hutu Ba— Lai Mohammed
Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya kira taron gaggawa na shugabannin majalisar tarayya inda ake sa ran shugabannin za su tattauna batun karin kasafin kudin da Buhari ya mikawa majalisar.
Wata majiya ta nuna cewa, shugabannin majalisar za su yi zama na awa guda ne sannan kuma Shugaban Hukumar Zabe mai zaman kanta, Farfesa Yakubu zai yi yiwa shugabannin majalisar bayani game da Naira Bilyan 242 da hukumar ke bukata don zaben 2019.
A dayan bangaren kuma, Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya yi gargadin cewa idan har majalisar tarayya ta ki dawowa daga dogon hutun da ta dauka don amincewa da wasu bukatun gwamnati da ke gaban majalisar ba, harkokin gwamnati za su tsaya cak.
Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya kira taron gaggawa na shugabannin majalisar tarayya inda ake sa ran shugabannin za su tattauna batun karin kasafin kudin da Buhari ya mikawa majalisar.
No comments:
Post a Comment