Friday, 10 August 2018
"KannyWood" Abubuwan Ban Mamaki 5 Da Baku Sani Ba Game Da Jaruma Hadiza Gabon
Jarumar dai ta shahara sosai inda ta fito a fina-finai da dama tare da lashe kyaututtuka ba iyaka tun bayan shigowar ta harkar fim shekaru kadan da suka wuce.
Haka zalika jarumar saboda kwarewar ta da kuma bajintar ta, hakan ne ma ya sanya ake saka ta cikin jerin fitattun mata a harkar fim din da suka fi karbar kudi kafin su taka rawa a fim din. NAIJ.com ta yi dogon nazari game da jarumar, ga kuma wasu abubuwan ban mamaki da muka tattaro maku game da jarumar:
1. A cikin shekara daya kacal jarumar ta koyi yaren Hausa har ta kware don ta shiga fim.
2. Yanzu haka jarumar na jin yare hudu(4) da suka hada da Hausa, Turanci, Faransanci da kuma Fulatanci.
3. Ta ce ta shiga harkar fim ne don ta samu kudin kafa gidauniyar taimakawa nakasassu wanda tuni ta cika burin na ta.
4. Sabanin da yawa daga cikin ‘yan matan fim, Hadiza Gabon ta taba yin fim din turanci.
5. Mahaifin ta dan asalin kasar Gabon ne amma kuma mahaifiyar ta ‘yar Najeriya ce.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Author Details
Ut wisi enim ad minim veniam, quis nostrud exerci tation ullamcorper suscipit lobortis nisl ut aliquip ex ea commodo consequat. Duis autem vel eum iriure dolor in hendrerit in vulputate velit esse molestie consequat.
No comments:
Post a Comment