APC ta sayi kuri'u don cin zaben sanatan Katsina ta Arewa acewar "Kaita"
Dan takatar jam'iyyar PDP a zaben cike gurbin Sanatan Katsina ta Arewa da ya gudana a ranar 11 ga watan Augusta, 2018, Alhaji Kabir Babba-Kaita, ya bayyanawa manema labarai dalilan da yasa kaninsa, Ahmad Babba-Kaita na jam'iyyar APC ya kayar dashi a zaben.
Alhaji Kabir Kaita yace: "Duniya dai taga irin abubuwan da suka faru a zaben cike gurbin sanatan Katsina ta arewa. Anyi amfani da makudaden kudade, jam'an APC da kuma gwamnatin jihar Katsina sun sayi kuri'u don cin zaben, wai don kada su baiwa shugaban kasa kungiya ace PDP ce ta lashe zaben" Dan takarar jam'iyyar ta PDP a zaben ciken gurbin sanatan Katsina ta Arewa wanda yasha kaye da rinjayen kuri'un da suka kusan rubanya nasa, ya ce kowace kuri'a da ya samu, ya sameta ta hanyar gaskiya, ba ta hanyar biyan kudinta ba.
Ya ce: "Koda ace ina da irin kudaden da APC tayi amfani dasu wajen rudar mutane, to bazan sayi kuri'ar kowa ba, tunda dai dalilin shigowata siyasa shine yiwa al'uma aiki kamar yadda nake yi tun kafin na shiga siyasa. Tunda kuwa siyasa Ca-ca ce, shine sukayi amfani da makudan kudade, dalilin da yasa har sukayi nasara akaina kenan.
"Kamar misalin gundumar, Galadima A, na samu kuri'u 179 yayinda APC ta samu 110." Bayan da hukumar INEC ta fitar da sakamakon zaben, Jam'iyyar PDP ta shigar da kara kotu, don kin amincewa da sakamon zaben. Sai dai Alhaji Kabir Babb-Kaita, ya bayyana cewa a matsayinsa na dan takara, ba shi da kuduri na shigar da kara kotu don nuna kin amincwwa da sakamakon zaben, tunda kowa yaga irin abubuwan da suka faru a zaben.
No comments:
Post a Comment