Matsalolin da mate ke fuskanta ta rashin gamsuwa da mazajensu.
Aure wani tsarin zamantakewa ne da ya kunshi abubuwa da dama, musamman ma hakkoki dake kan ma'auratan.
A kan samu wasu lokutan da daya daga ma'aratan kan koka da yanayin zamatakewar, musamman ma idan yana cutuwa ta wasu bangarorin.
Duk da cewa a kan samu masu korafi kan wasu matsalolin, ba kasafai mata kan iya fitowa su bayyan matsalar rashin daga mazajensu ba yayin mu'amalar aure.
Bayanai sun nuan cewa wannan matsala tana damun mata da dama, kuma ta kan jefa rayuwarsu cikin kunci, a wasu lokutan ma har ta kan taba lafiyar kwakwalwarsu.
Kunya da kawaici da kara da kuma al'ada ba sa barin mata su fito su bayyana irin wannan matsala, kuma masana sun ce tana daga manyan dalilan da ke janyo mutuwar aure.
A wannan makon, filin Adikon Zamani ya yi duba kan wannan ta fuskar likitanci da kuma addini.
No comments:
Post a Comment