Jonathan bai ceto 'yan matan Chibok ba - BBOG.
Iyayen daliban makarantar sakandiren Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace a 2014 sun musanya ikirarin Reuben Abati, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, na cewar Gwamnatin Tarayya karkashin tsohon shugaban kasar ta kwato da yawa daga cikin ‘yan matan.
A ranar Laraba ne mai magana da yawun tsohon shugaban kasar ya bayyana a wani shirin talabijin tare da Femi Adesina, mataimakin shugaba Buhari na musamman kan sha’anin kafafen watsa labarai cewa, an tura ‘yan matan da gwamnatin Jonathan ta ceto zuwa kasar Amuruka da Burtaniya bayan da aka ceto su.
Ya ce: "A lokacin mai tallafawa tsohon shugaban kasar kan fannin tsaro, Sambo Dasuki ne ya shawarci Jonathan akan kin bayyana ceto ‘yan matan da kuma fitar da bayansu ga al’umma." Ya bukaci Adesina da ya tabbatar da ikirarinsa ta hanyar tuntubar hukumar jami’an tsaro ta farin kaya DSS da kuma sashen tsaro na jami’ai na musamman. Sai dai a jiya shugaban kungiyar dake fafutukar ganin an kwato ‘yan matan na Chibok wato BBOG, Yakubu Nkenke, ya musanya ikirarin cewar an ceto ‘yan matan Chibok din ne a gwamnatin baya.
Ya ce a wannan gwamnati mai ci ne aka kwato yan matan 107 daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram. Nkenke sai yayi kira ga gwamnati mai ci a yanzu data kokarta wajen kwato sauran ‘yan mata 112 da har yanzu ake tsare da su, yana mai cewa da yawa daga cikin iyayen ‘yan matan sun shiga cikin dimuwa biyo bayan mutuwar yara 32.
Iyayen daliban makarantar sakandiren Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace a 2014 sun musanya ikirarin Reuben Abati, mai magana da yawun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, na cewar Gwamnatin Tarayya karkashin tsohon shugaban kasar ta kwato da yawa daga cikin ‘yan matan. A ranar Laraba ne mai magana da yawun tsohon shugaban kasar ya bayyana a wani shirin talabijin tare da Femi Adesina, mataimakin shugaba Buhari na musamman kan sha’anin kafafen watsa labarai cewa, an tura ‘yan matan da gwamnatin Jonathan ta ceto zuwa kasar Amuruka da Burtaniya bayan da aka ceto su. Jonathan bai ceto 'yan matan Chibok ba - BBOG Ya ce: "A lokacin mai tallafawa tsohon shugaban kasar kan fannin tsaro, Sambo Dasuki ne ya shawarci Jonathan akan kin bayyana ceto ‘yan matan da kuma fitar da bayansu ga al’umma." Ya bukaci Adesina da ya tabbatar da ikirarinsa ta hanyar tuntubar hukumar jami’an tsaro ta farin kaya DSS da kuma sashen tsaro na jami’ai na musamman. Sai dai a jiya shugaban kungiyar dake fafutukar ganin an kwato ‘yan matan na Chibok wato BBOG, Yakubu Nkenke, ya musanya ikirarin cewar an ceto ‘yan matan Chibok din ne a gwamnatin baya. Ya ce a wannan gwamnati mai ci ne aka kwato yan matan 107 daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram. Nkenke sai yayi kira ga gwamnati mai ci a yanzu data kokarta wajen kwato sauran ‘yan mata 112 da har yanzu ake tsare da su, yana mai cewa da yawa daga cikin iyayen ‘yan matan sun shiga cikin dimuwa biyo bayan mutuwar yara 32. KU KARANTA: Tunda na bar APC ni ke ta fuskantar matsaloli - Inji wani gwamnan Arewa A bangaren Abati kuwa, ya tsaya a kan bakansa na cewar a gaban idonsa aka kai ‘yan matan da aka kwato gaban tsohon shugaban kasa Jonathan don ganawa da su. “Mun samu nasarar ceto da yawa daga cikin ‘yan matan, sai dai mai tallafawa tsohon shugaban kasar ta fuskar tsaro, ya bada shawarar kin bayyana bayanan ‘yan matan. A gaban idanuwana hakan ta faru. An kawo wadan nan ‘yan matan gaba shugaban kasa,” a cewar Reuben Abati.
No comments:
Post a Comment