Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Thursday, 21 December 2017

RUWAN KASHE GOBARA! 45



_45_

Falo suka dawo ita da ni'iman ta nemi wuri ta zauna ko magana bata iya yi sai dai daga kai,
"Sannu ikhlas Allah yayi masa rahma,dazu barrister ya kirani yace nazo nayi miki gaisuwa kafin ya dawo shi baya nan yayi tafiya zuwa kaduna wurin wani case"
Daga kai ikhlas tayi bata iya yin magana ba, ni'iman ta dan jima kafin ta tashi zata tafi, bin bayanta ikhlas tayi dakyar ta rakata tsakar gida suna fita ta hangi lamido tsaye shida wani mutum wanda daga gani kanin mahaifinsu ne ko wa,
Binsa tayi da kallo shi dinma yanzu duk ya zama wani abun tausayi domin har yayi wata yar rama,
Daga inda take tayiwa ni'ima sallama ta juya ciki, dakin innah taje ta kwanta domin nan babu mutane sosai tana nan a kwance har mangaruba tayi, tashi tayi tai salla tana idarwa ta koma ta kwanta,
Muryar Lamido ta fara jiyowa yana yiwa innah magana suna dosowa cikin dakin,
"Innah zaman makokin nan fa duk bidi'a ce babu ita a koyarwar annabi, dan haka ana yin kwana uku kowa ya watse yatafi yaci gaba da harkokinsa" Lamido yafada kamar zaiyi kuka domin wannan mutuwar ta sadiq ta bugeshi mutuka,
"Haka baffah ma yace domin duk wani labarin duniya agidan mutuwa zakaji ana yinsa awurin karbar gaisuwa dan haka sai kaga maimakon asamu lada sai ayita daukar zunubi"
"Ai ana yin kwana uku wallahi kowa sai ya tafi.." Daidai lokacin suka shiga cikin dakin,
"A'a ikhlas dama kina nan?" Innah ta tambayeta, kai ikhlas ta daga, kallonta Lamido ya danyi duk bakinta yagama bushewa gashi tayi wani irin sanyi,
"Innah bata da lafiya ne??" Ya tambayi innah,
"Ehh to kasan mai juna biyu ba a rabashi da ciwo gashi kwata kwata bata ci abinci ba nidai ko ruwa banga tasaka acikinta ba..."
"Kuma shine take kwance??" Yafada arazane, da saurinsa ya fita mintuna kadan ya dawo hannunsa rikeda gwangwanin maltina,
Bude gwangwanin yayi batare da ya kalleta ba yace "tashi kisha malt"
Dakyar ta tashi saboda wani jiri take ji, karba tayi tana mamakinsa domin duk maganar da zai yi mata baya kallonta asalima gani take kamar dole yayansa marigayi yayi masa wurin bashi amanarta data abinda ke cikinta, domin sam kamar bashida ra'ayinta,
Sanyi karara maltina din dan haka ta daga tafara sha tana shanyewa ko ajiye gwangwanin bata yiba taji amai ya taho mata take tafara kwarara shi wanda har kan kafar Lamido sai data wanketa da aman,
"Sannu ikhlas, sannu,Lamido ko asibiti zakuje?" Inna ta fada arude,
"A'a bari zan kira likita" yabawa innah amsa yana satar kallon ikhlas wacce ke rike da cikinta tana yunkurin amai, wani tausayinta yake ji yana ratsashi,
Likita ya kira awaya minti kadan sai gashi nan yafara dubata jin fatarta tayi laushe tayi yaushi yasashi jona mata karin ruwa,
Tare suka fita da Lamido yafara shaida masa cewar adaina barinta tana zama da yunwa saboda abinda ke cikinta,
"Likita ina fata dai cikin lafiya yake?"
"Lafiya lau yake babu abinda ya sameshi amma akiyaye"
"Insha Allah dr"
Dawowa dakin da take yayi bayan ya sallami likitan, tana kwance bacci ya dauketa fuskarta tayi wani siyau,
Tausayinta yake ji sosai yadade atsaye kafin ya juya yafita daga dakin, gidansa ya wuce saboda su ihsan sun tafi tuni,
Wanka kawai yayi ya kwanta yadaga kanshi sama yana tunani, rayuwa kenan yanzu shikenan har sadiq yayi ya gama sai dai a ambaci sunanshi amma badai aganshi ba lallai rayuwar duniya yar kalilance,
Yana nan kwance yana tunani har dare yayi nisa domin kasa bacci yayi sai aikin tunani yake tayi ciki harda tunanin ikhlas ashe da rabon sai dan uwanshi ya aureta kafin shi ya mallaketa tunda gashi nan harda rabon juna biyu atsakani,
Juyi yayi ya rungume pillow yanzu bazai iya fassara yanda yake ji ba shin kishin dan uwanshi yake ji ko sabanin haka? Shidai yasan yana jin wani yanayi wanda yakasa ganeshi,
Har asuba tayi idonshi biyu, salla kawai yayi ya sake kwanciya har lokacin dai bai samu barcin ba hakan yasa idonshi yin dan ja kuma ya kumbura,
Karfe  7 daidai ya tafi gidan Baffa, lokacin an fara fitowa da tabirmi ana shimfidawa a rumfar da akayi a kofar gida,
Cikin gidan ya shiga ya nufi dakin innah yana gaggaisawa da jama'a, yana shiga ya samu ikhlas zaune tayi tagumi akan gadon innah, batare da ya kalleta ba yace,
"Kinci abinci?"
Dagowa tayi ta kalleshi yana sanye da blue din yadi harda hula,
"Ina kwana? Ya karin hakuri?" Tafada ahankali,
"Lafiya, alhamdulillah"
Kallonta ya sake yi "nace kinci abinci?"
Kai ta girgiza "waina da miya akayi nikuma kosai da koko nake so"
Batare da ya sake magana ba ya fita, wayarshi ya dauka yakira bash yafara tambayarshi a ina za asamu koko da kosai?
Wurin 8 bash ya kawo masa koko da kosai din, tashi yayi ya shiga cikin gidan har lokacin ikhlas tana dakin innah akwance bakinta ya bushe,
"Gashi, tashi kici" yafada bayan ya ajiye mata agabanta, mikewa tayi ta dauki kosan tafara ci sai da yaga taci kusan rabi sannan ya juya ya fita,
Bin bayanshi tayi da kallo aranta tana tunanin irin zaman da zasuyi dashi amatsayin ma'aurata domin zata cikawa sadiq burinsa na auren dan uwanshi kamar yadda yabar wasiyya sai dai taga alamun shi lamidon kamar yanada jijida kai da wulakanci ko kuma dan yaga yana da kyau ne?
Tabe baki tayi taci gaba da cin kosanta. Akwana atashi har Abubakar sadiq ya cika kwana uku da rasuwa hakan tasa aka daina zaman makoki kowa ya kama gabansa in banda Lamido da baffa sai bash, acikin gida kuwa iya innah ce kadai sai ikhlas da uwargidanta, domin ko matan Lamido ma ya hanasu zuwa yace suyi zamansu baya son zaman nan na munafurci,
Ranar da Abubakar sadiq ya cika kwana biyar aranar barrister elmustapha yadawo yazo yiwa ikhlas gaisuwa, kicin kicin Lamido yayi ya hade rai yatashi ya shiga cikin gida inda ikhlas take,
"Waye barrister elmustapha?" Ya tambayeta fuskarshi adaure,
"Dan uwana ne" tafada tana kokarin tashi,
"To kizo yazo yimiki ta'aziyya" yafada tareda fita daga cikin dakin,
Bin bayanshi tayi ta samesu awaje atsaye shida elmustapha din,
Yana tsaye yana kallonsu har suka gama gaisawa elmustapha yayi mata gaisuwa ya tafi sai lokacin shima yakoma wurinsu baffa ya zauna.
Ranar da akayi sadakar bakwai aranar kowacce ta koma gidanta, ita ikhlas itada hajiya kakarta zasu zauna zata tayata zama, lokacin da ta shiga gidanta kuka ta fashe dashi domin jin mutuwar tayi ta dawo mata sabuwa saboda gani take kamar zata ga Abubakar sadiq komai nashi gashi nan hatta agogon da yacire ranar da zai rasu gashi nan ajiye akan mirror,
Kuka ta wuni tanayi har yamma, lokacin Lamido yazo gidan ya isketa tana kukan, hajiya ce tayi masa bayanin abinda yafaru cewar tun dawowarsu take kukan nan,
Dakin ya shiga ya tattaro duka kayan sadiq din yafita dasu yasa a mota,
Dakyar hajiya ta samu ta sata tabar kukan ta shiga wanka tafito tazo ta kwanta hannunta rikeda carbi tana ja.

No comments:

Post a Comment

Pages