_46_
Baccine yayi gaba da ita saboda ta jima bata yiba,tana nan tanata barci har hajiya ta shiga kitchen tayi musu dan wake tafito,
Firgigit ikhlas ta farka daga baccin da take saboda mafarkin da tafara da marigayi Abubakar sadiq,
"Ga abinci can nayi, sannan kina bacci makotanki na baya sun shigo yi miki gaisuwa"hajiya tace da ita,
"Hajiya bazan iya cin abincin nan ba saboda bana sha'awar cin komai yanzu gashi cikina ciwo yake yi" ikhlas tafada tana yamutsa fuska,
"Daurewa zakiyi kinji, daure"
Komawa tayi ta kwanta bata ci abincin ba taci gaba da jan carbinta.
Lamido koda ya kwashi wannan kayan gidan innah yaje ya bude tsohon dakinsa ya zuba kayan ya fito ya nufi gidanshi,
Lokacin da yaje gidan fadila ya samu a babban falo tana buga tv game tasha gayu cikin riga da wando jeans yayinda ihsan take cikin kitchen tana yin girki,
"Welcome my Lamido" fadila tafada tana kokarin kaucewa motocin da suke gabanta,
"Yawwa my fadila" yafada atakaice ya wuce dakinsa, ihsan ce ta fito daga cikin kitchen tawuce fadila tana tsaki, "mtswwwwwwww"
"Banda lokacin ki yarinya" fadila tafada,
"Aikin banza" ihsan tafada ta nufi dakin Lamido, tana shiga fadila na shiga ta jawo rigarta ta baya,
"Ke wa kika cewa banza? Ni sa'arkice?"
"Ba asaniba, sannu uwata karewar girma kenan"
Lamido yana cikin bathroom yana jinsu har yafito basu daina cacar baki ba,
"Ban taba sanin ku sokaye bane sai yau, anyi min rasuwa ko dadewa ba ayiba kunzo kuna yimin shouting aka baku barni da radadin mutuwar da dan uwana yayiba"
Fita fadila tayi ita kuma ihsan ta tsaya saboda itace dashi, tana nan tsaye har ya shirya yasaka kananan kaya bakar t shirt da jeans blue ya dauki key din motarshi zai fita,
"Darling ba zaka ci abinci ba?" Ta tambayeshi cikin tausayawa domin Lamido yanzu dolene yabaka tausayi saboda duk ya zama wani sanyi gashi ya dan rame kadan,
Kai kawai ya girgiza ya juya zai fita, hannunshi ta riko cikin nata,
"Kayi hakuri insha Allah ba zamu sakeba, dan Allah ka cire damuwa aranka pls and pls.."
"Nagode my ihsan, bari naje gidan ikhlas nadawo zanje na dubota saboda bata da lafiya"
Kallonsa ihsan ta tsaya yi batare da tace komai ba har yafice daga cikin dakin,
Masallaci yafara zuwa yayi salla sannan yatafi gidan ikhlas din, lokacin da yashiga gidan ya samu hajiya tanata fama da ita akan ta tashi taci abinci amma taki tashi,
"Ke yanzu hakan zai yimiki dadi kinada lalura amma ba zakici komai ba?" Hajiya tafada cikin fada,
Lamidone ya shiga falon bakinsa dauke da sallama idanuwansa akan ikhlas wacce ke kwance akan tiles ta tasa kanta da pillow din kujera,
"Sannu da zuwa Lamido, lale" hajiya tafada,
"Yawwa sannu hajiya" Lamido yace da ita ahankali,
Zama yayi yana kallon ikhlas,
"Hajiya bata da lafiya ne?" Ya tambayi hajiya,
"Wai cikinta ne ke ciwo kuma taki cin abinci"
Tashi yayi ya isa inda take kwance ta juya musu baya,
"Meyasa ba zaki ci abinci ba?" Yafada yana kallonta,
"Cikina ne yake ciwo kuma bana son cin yaji"
"Sai me kike son ci?" Ya tambayeta yana kallon wani wuri,
"Doya da kwai irin wacce ake sayarwa a kasuwa"
Batare da ya sake magana ba ya juya ya fita yana yiwa hajiya magana,
"Hajiya bari naje nadawo"
"To to sai ka dawo,sai ka dawo"
Fita yayi aransa yana tunanin wani aiki sai me ciki, kasuwa ya shiga layin yan doya, nan ya samu ana soyawa fita yayi ya siyo mata cikin bakar leda,
Gidan ya koma ya isketa ta rako wasu mata wadanda suka je yi mata gaisuwa,
Wucesu yayi bai ko kallesu ba, wannan yana daya daga cikin banbancin halayyarsu da marigayi domin shi mutumne marar shariya da kyaliya gashi da faran faran sabanin Lamido wanda yake marar magana gashi da rashin fara'a sam baya son yiwa mutane magana ko kallonsu ma bai damu dayi ba,
Dawowa tayi daga rakiyar da tatafi tana tunanin halin Lamido wanda tafara ganewa,
"Gashi nan ya kawo miki doyar idan dagaske kike sai kici" hajiya tafada cikin mita,
Jan ledar doyar tayi ta zauna ta bude tafara dauka tana ci,
Yana zaune yana kallonta har ta ci da yawa sannan ta ture ledar ta kwanta awurin,
"Hajiya bari natafi zanje gidan suhaima itama na dubata, bari na rubuta miki no dina idan da wani abu sai ki kirani"
"To shikenan insha Allahu ma babu komai, madalla angode"
Batare da ya kalli wurin da ikhlas take kwance ba ya wuce ya fita,
Gidan suhaima yaje itama tana sanye cikin katon hijabi da carbi a hannunta ga mamanta nan da kanwarta wadanda suke tayata zama kasancewar mahaifinsu ya jima da rasuwa,
Da gudu su hydar da faruk suka taso suka rungumeshi suna cewa, "oyoyo uncle"
Rungumesu yayi sai kuma yaji kwalla ta cicciko masa idonshi, hannunshi yasa ya goge ya dauki karamar wato Aysha ya kama hannunsu faruk zuwa ciki,
Zama yayi suka fara gaggaisawa, tunda ya shigo Xahar kanwar suhaima ta kafeshi da ido kamarsu daya da sadiq marigayi amma yafishi kyau nesa ba kusa ba.
No comments:
Post a Comment