_44_
Da haka Lamido ya samu ya kammala jarabawarsa amma ya dan rame yayi baki, aranar da yagama washe gari ya dawo Nigeria,
Murna wurin ihsan da fadila tamkar zasu cinyeshi, kowacce nuna masa soyayya take hakika ya tabbatar shi dan gatane,
Dawowarsa babu yanda yayansa baiyi dashi ba akan yaje su gaisa da ikhlas amma yaki zuwa,
Kullum yana rufe acikin daki sam baya walwala amma ahakan yana daurewa yabawa matanshi kulawa, ganin yanayin da yake ciki yasaka innah zaunarshi ta tambayeshi damuwarsa amma fur yaki sanar da ita, duk wanda ya ganshi yasan yana cikin damuwa da bacin rai,
Ganin abun kullum gaba yake yasa baffanshi saka malamai aka fara yi masa rokon Allah,
Yadan samu sassauci acikin zuciyarsa amma damuwa kam har lokacin yana tattare da ita, ga tsananin ciwo da kanshi yake yi masa.
*
Zaman ikhlas da Abubakar sadiq abin gwanin ban sha'awa kullum cikin faranta ran junansu suke, watansu daya da aure ikhlas ta fara laulayi, koda sukaje asibiti gwajin farko likita yace tana dauke da juna biyu, murna wurin Abubakar sadiq abin ba acewa komai, wata sabuwar kulawa ya shiga bata alokacin yaje borno ya dauko mata abdallah domin yayi mata hutu amma Hussain dakyar ya bari aka taho dashi dan yayi mata sati biyu kacal, tunda abdallah yazo Abubakar sadiq yake fita dasu wuraren shakatawa har ya gama yi mata sati uku yatafi saboda kullum sai Hussain ya bugo waya yana cewa adawo dashi,
Gidan barrister elmustapha Abubakar sadiq ya kaita ta wunarwa ni'ima wacce tana nan dauke da yarta Ikhlas, wuni sukayi suna hira ita dai ni'ima duk kunyar abubuwan da ta yiwa ikhlas abaya yanzu take.
Cikin ikhlas yanada wata uku Abubakar sadiq ya samu sauyin wurin aiki inda aka mayar dashi bauchi alokacin ya shirya yaje yayi report ya dawo, dawowarsa da sati biyu ya shirya tafiya, rigima ikhlas ta saka masa adole sai ya tafi da ita, dakyar ya rarrasheta yace next time idan yazo tare zasu koma,
Rakashi tayi ta dawo tana murmushi, ko minti talatin ba ayiba da tafiyarsa kaninshi lamido yazo gidan idonsa jajur, wannan shine karo na farko da yazo gidan,
Tana dakinta tana nunke kayanta taji sallamarsa cikin daddadar muryarsa duk da mganarshi tana dan shigen kama da irin ta Abubakar sadiq amma ta lamido tafi dadi,
Hijab tasa ta fito tana amsa sallamar, sai da gabanta ya fadi lokacin da suka yi ido biyu domin ba karamin kyakkyawa bane ashe ganin da tayi masa ahoto kyansa bai bayyana ba,
"Am dama brother sadiq ne yace nazo mutafi tare dake" yafada ahankali yana kallonta,
"Yana ina? Lafiya? Ina zamuje"
"Lafiya lau, kizo muje yana can gidan uwar gidanshi"
Babu abinda ta dauka tabi bayanshi ko gidan bata rufeba domin jikinta yabata babu lafiya,
Motarshi suka shiga amma agidan baya ta zauna yatashi motar suka nufi titin asibitin makama,
Koda suka isa tuni harsu baffa da uwargidan Abubakar sadiq sun karaso, innah da uwargidan sai kuka suke ga yaranshi ma sunata kuka abin tausayi,
"Lafiya? Meya faru? Meya samu sadiq din?" Ikhlas ta tambaya agigice,
Rungumeta uwar gidanta tayi tana kuka "hatsari yayi,over taking akayi masa tifa tabi ta kansa, shikenan zamu rasaka..." Tafashe da wani sabon kukan,
Lamido ne ya mike yabi bayan likita domin za adebi jininsa akarawa sadiq,idanuwansa sunyi jajur daga gani hankalinsa atashe yake,
Wunin ranar ba abarsu sun shiga inda yake ba sai da daddare suka samu ganinsa, yana kwance ko ina na jikinsa an nannade da bandeji kansa ya kumbura mutukar kumbura kamar an hura,ko ina jini ya firfita ajikinsa,
"Sannu.. Sannu sadiq" ikhlas tafada tana kuka,
Hannun uwargidanshi ya kamo yarike ahankali yafara magana wacce ba aji har sai an kasa kunne,
"Allah yayi miki albarka, Allah ya raya mana yaranmu, kiyi hakuri zan tafi nabarki da nauyinsu akanki, kiyi hakuri ki basu tarbiya yadda ya kamata, Allah yayi miki albarka"
Rushewa da kuka uwargidan tayi tafita waje, hannun Lamido ya kamo ya kamo hannun ikhlas,
"Lamido kai Kanina ne hakika nasan zaka iya rike min amanar iyalina, ga ikhlas nan ka aureta ka riketa kabata kulawa da duk wani gata kamar ina raye, Lamido ka aureta saboda bana son ikhlas ta auri bare wanda ba jinina ba ina jin tausayin ikhlas saboda zan tafi nabarta daidai lokacin da take bukatata..." Take yafara wani tari mai ban tausayi,
"Tana dauke da juna biyu, nabar maka amanarsu itada abinda ke cikinta...." Iya abinda ya iya fada kenan tari mai sarke kirji yaci karfinsa take yafara aman jini, kuka wiwi ikhlas take rerawa dakyar innah ta kamata suka fita itama tana kukan,
Dawowa cikin dakin innah tayi nan tasamu Baffa Abubakar sadiq yana yi masa jawabi irin wanda yayiwa ikhlas da Lamido amma kuma yakasa fada sosai saboda tarin da yaci karfinsa, shi kansa sadiq din kuka yake yi sosai,
Lamido kam sarkin kuka tun dadewa hawaye suka balle masa, shigowar likita ne yasasu fita waje dukkaninsu suna fita suka iske yaran sadiq suna kuka suna cewa akaisu suga abbansu,
Wannan kadai ya isa saka mutum kuka, tsit wurin yayi baka jin komai sai kukansu, alokacin babban yayansu lamido da yayarsu suka karaso nan wuri ya sake barkewa da kuka,
Dare suka raba suna koke koke duk cikinsu babu wanda yayi bacci suna zaune suna jiran tsammani har asuba tayi alokacin Abubakar sadiq yayi shahada ya cika,
Likitan ne ya fito fuskarshi daukeda alhini ya shaida musu cewar Abubakar sadiq ya rasu,
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un" shine abinda kowannensu ya furta, nan kowa yafara kukan zuci wanda yafi nafili ciwo, lamidone suka shiga shida babban yayansu suka fito da gawar,
Gida dukkaninsu suka dunguma suka tafi, suna zuwa labari yafara yaduwa cewar Allah yayiwa Abubakar sadiq rasuwa nan gida yafara cika da yan uwa da abokan arziki, innah ko hawaye batayiba tana zaune rikeda cazbaha a hannunta,
Ita kuwa ikhlas hawayen ma har ya kafe tana kwance ajikin bango ta takure,
Tun asuba aka yi masa wanka aka shiryashi gari yana wayewa misalin karfe tara aka yi masa salla aka tafi kaishi bayan yan uwa sunje sunyi masa addu'a,
Ikhlas tana kwance ta rike kanta takasa koda motsi rabonta da abinci tun jiya da safe kafin sadiq yatafi, tana nan kwance yan gidansu suka zo daga Maiduguri lokacin karfe 12 narana,
Ko ruwa bata iya shaba innah tayi tayi da ita tasha koda tea ne amma takasa sha, tana daga kwance tana kallon kowa ciki harda matan lamido ihsan da fadila.
Misalin karfe 4 na yamma tana inda take a kwance innah tazo tana kiranta cewar tayi baki, tashi tayi ta fita jiri yana daukarta, ni'ima matar elmustapha tagani sunzo yi mata gaisuwa.
No comments:
Post a Comment