Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Tuesday, 12 December 2017

RUWAN KASHE GOBARA! 24



_24_

Wani irin bakin ciki take ji yana ratsa cikin zuciyarta,
"Wannan wacce irin masifa ce ta sameni? Daga fyade sai ciki, innalillah hakika bazan taba yafewa wanda yayi sanadiyyar shigata cikin wannan bakin cikin ba" tafadi hakan acikin ranta,
Hankalinta ne yadawo jikinta sakamakon jiyo muryar abbanta da tayi yana cewa,
"Likita ka sake bata wannan maganin mana irin na dazu ko zamu yi nasara cikin ya zube"
"A'a Alhaji yin haka komai zai iya faruwa saboda kaga shi wannan maganin aka'ida ba ashan fiyeda guda biyu ita kuma kaga har guda takwas nabata, over doze din yayi yawa gaskiya"
"To yanzu likita menene shawara?
"Yawwa ni ina ganin akyaleta yanzu ta huta zuwa nanda kwana biyu inyaso idan har lokacin cikin bai zubeba sai nasake bata wasu kwayoyin"
"To shikenan dr nagode"
"Yawwa sannan yanada kyau abata abinci taci"
"Hajiya Nafi kawo mata abinci"
Fita dukkaninsu suka yi daga cikin dakin hajiya Nafi tawuce kitchen ta zubowa ikhlas tuwon shinkafa miyar agushi, lokacin data shiga cikin dakin ikhlas ta tashi zaune tana tunani idonta yana zubar da kwalla,
"Ai bakiyi kuka ba tukunna har sai ubanki yayi miki korar kare daga gidan nan, yanda uwarki tabar gidan nan dole kema sai kin barshi wlhi"
Dagowa ikhlas tayi tana kallonta, hakika dama tunda jimawa tasan hajiya Nafi da yakumbo basa kaunarta amma wannan abin da yafaru ya sake tabbatar mata irin kiyayyar da suke yi mata, abincin hajiya Nafi ta gara mata ta juya tayi tafiyarta,tana cin abincin tana kuka har ta gama,daren ranar kuwa duk iya sata ta bacci haka yaganta ya kyale.
Kwananta biyu acikin mawuyacin hali na lalura domin har yau jinin dake zuba ajikinta bai tsaya ba, aranar dr yadawo,
Shida abbanta ne suka shigo cikin dakin da take, ganinsu yasata tashi zaune,
"Dr kaje ka dubata idan cikin yana nan har yanzu to kayi duk yanda zakayi ka fitar dashi da karfi"
Arazane ta dago ta kalli abbanta, "Abba na rokeka da girman Allah ku kyaleni haka ni nadauki kaddarar da Allah ya doro min, nasan abinda kake tsoro abba tsoron kar maganar nan tafita gari yan adawa suyi maka dariya kake, abba ka taimake ni ka sanar dani inda mahaifiyata take wacce ka rabani da ita tun ina yar shekara 5 aduniya, kasanar dani inda take zan tafi nabar maka gidanka ta yanda ma babu Wanda zai san abinda yafaru da yarka"
Kuka take wiwi kamar ranta zai fita,
"Dr wai me kake jirane? Kayi abinda na umarceka"
"Yallabai ka duba maganar da yarinyar nan take yi" Dr yafada,
Juya baya abba yayi "da narasa kujerata da nake nema gara kin tattara kin bar gidan nan tabbas, ikhlas yau zan fada miki inda mahaifiyarki take, mahaifiyarki tana jihar Borno acikin miduguri a unguwar zumar, indai kikaje nan to duk wanda kika tambaya gidan shuwa babu wanda bai sani ba domin duk unguwar gidansu ne kadai shuwa Arab"
Saukowa tayi daga kan gadon tana hawaye,"abba kayafe min dan Allah nasan nasaka bakin ciki amma kayi hakuri ka gafurceni, sannan nagode yau da sanar dani da kayi inda mahaifiyata take zanje zan nemeta ita da sauran yan uwana"
Ba karamin tausayi tabawa dr dinnan ba, kayan aikinsa ya hada yayiwa abbanta sallama ya fita,
Akwati ta jawo tafara loda kayanta aciki tanayi tana kuka har ta kammala taja akwatin bayan ta yafa mayafinta,
Rafar yan Dubu Dubu guda biyu abbanta ya watsa mata ya juya ya fice daga cikin dakin,
Akwatinta taja har zuwa falo tana share kwallar idonta, yakumbo tagani da hajiya Nafi tsaye suna kallonta,
"Allah ya raka taki gona dangin munafurci da bakin rai, irida maita" yakumbo tafada tana harararta,
"Allah yaraba lafiya, ayi rainon ciki da goyo lafiya sai munzo suna" hajiya Nafi tace da ita tana shewa,
Akwatinta taja ta kara Sauri tafice daga falon tana kuka, bata sake koda waiwaye ba har tabar gidan tafita gate ma'aikatan gidan da jami'an tsaro sai kallonta suke tana tafe tana kuka,
Abakin titin kofar gidansu tayi sa'a ta samu taxi nan ta saka jakarta aciki ta shiga tace da mai motar ya kaita tasha, har lokacin kukan bakin ciki da bacin rai take yi wanda ji take inama ta mutu ta huta da wannan takaicin rayuwar.
Tafiyar minti ishirince ta sadasu da tashar mota tana zuwa ta samu motar da zataje Borno dama motar ta cika yanzu mutum daya suke jira dan haka koda taje aka saka kayanta a motar shirin tafiya kawai driver din motar yayi nan da nan suka harba titi,
Kanta ta kwantar akan cinyoyinta tana kuka marar sauti sakamakon halin data samu kanta aciki, abbanta yana sonta yana kaunarta kuma yana nuna mata soyayya akoda yaushe amma yanzu ya juya mata baya sakamakon kaddarar data afka mata ya kasa hakuri ya rungumi kaddarar da Allah ya aiko musu domin yana gudun kada takararsa ta lalace.

No comments:

Post a Comment

Pages