_23_
Rikeshi hajiya Nafi tayi tana cewa "a'a Alhaji karka illatata"
"Ai gwanda ya illata ta kowa ya huta, yarinyar nan nema take ta bata masa suna agari" yakumbo tafada tana hararar ikhlas,
"Hajiya Nafi ikhlas tana neman tayi min sanadin da yan adawa zasu samu galaba akaina, labarin nan yana fita yan adawa zasu fara yimin yarfe wanda daga karshe zai janyo min rashin nasara azaben da za a gudanar"
"Kayi hakuri Alhaji yanzu kawai hanya mafi sauki ka kira likita ya zubar da cikin nan tun kafin zance ya yadu agari yan adawa su samu hanyar cin mutuncinka agidajen radiyon dake kasar nan"
Lekawa abba yayi ya kira dr, yafara yi masa bayanin azubar da cikin, ita dai ikhlas tana zaune akan gadonta tana gursheken kuka,
"Alhaji zubar da cikin nan akwai hatsari domin yakai wata biyar..!"
"Ya isa dr nidai kawai kayi abinda nasaka" abba yafada cikin tsawa,
Jiki na rawa dr ya debo wasu manyan kwayoyi guda takwas ya mikawa ikhlas,
Cikin kuka ta karbi magungunan, "hajiya Nafi Miko ruwa, miko ruwa"
Dasauri hajiya Nafi taje ta dauko robar ruwa tana murmushin jin dadi,
"Wannan yarinya baki yiwa kanki dabara ba, kin cuci kanki, koda yake banyi mamaki ba duba da irin takardar da kika bari kafin ki tafi yawon karuwancin" yakumbo tace da ita cikin isgili,
Shiru ikhlas tayi batace komai ba sai hawaye saboda tasan koda tayi magana abbanta ba saurararta zaiyi ba awannan lokacin,
Allura guda uku likita ya sake zuka ya nutsa mata, nan take taji jiri yana daukarta ga mararta ta turnuke da ciwo, babu shiri ta kwanta tafara murkususu,
"Gara ki mutu ma mu huta" hajiya nafi tafada acikin ranta,
"Dr dan Allah ka rike min sirrin nan bana son maganar nan tafita waje har yan adawa suji" abbanta yafara rokon dr,
"Kar kaji komai yallabai insha Allah babu wanda zaiji"
Ganin mutane bibbiyu ikhlas tafara sai kuma taji fitar wani abu daga jikinta, take jini ya balle kamar an bude fanfo,
Zaro ido dr yayi,
"Yallabai ina jin ansamu matsala"
"Likita babu damuwa muddin cikin zai fita toni bukatata ta biya"
"Wayyo abba, wayyo cikina" ikhlas tafada cikin nishi, babu wanda ya kulata acikinsu suka juya suka firfice daga dakin.
Falo sukaje suka zazzauna jigum yayinda yakumbo itada hajiya Nafi suka dage suna zuga abban ikhlas suna dada tunatar dashi wasikar da ikhlas din tabar masa tsawon shekaru 5 da suka gabata.
Kimanin awa daya suna zaune suna tatrauna maganar, dr ne yasake komawa dakin da ikhlas take ciki tana kwance bata ko motsi, iya tsorata dr ya tsorata nan take yafara bata taimakon gaggawa, gashi ta zubar da jini da yawa kuma hankalinta da alama baya jikinta,
Falo ya fita da sauri inda su yakumbo suke,
"Yallabai yarinyar nan tana bukatar ruwa da jini"
"Dr kaje ka samo duk abinda ake bukata nidai burina cikin nan yafita indai yafita zan iya kashe ko nawane"
Hannu yasa acikin aljihunsa ya ciro rafar yan dari biyar biyar ya mika masa,
Dasauri likitan ya fice domin zuwa samo jinin da ake bukata da ruwa,
"Wannan yarinya ta gama cin mutuncinmu" yakumbo tafada tana rike haba,
"Kanta taciwa mutunci amma baniba" abban ikhlas yafada ahargitse,
Cikin mintunan da basu wuce 20 ba dr ya dawo dauke da jini leda hudu da ruwa shima leda hudu ga magunguna cikin leda,
Dakin da ikhlas take ya shiga har lokacin bata motsi,
Ruwa ya daura mata ahannun damanta hannun hagun kuma ya daura mata jini,
Har jinin ya kare da ruwan aka sake daura wani bata dawo hayyacinta ba, gashi jini bai tsaya ba,
Yinin ranar sunyi shine cikin tashin hankali, misalin karfe 5 na yamma likitan yabar gidan da niyyar zai dawo da daddare, babu wanda ya sake komawa dakin da ikhlas take balle yaga halin da take ciki.
Karfe 6 ta bude idonta wanda ya ke dishi dishi, jinta tayi ajike, hakan ne yasata tuno da abinda yafaru da ita, wani rikitaccen kuka ta saki tana hadiyar dunkulen bakin cikin daya tokare mata makogaro,
Dakyar ta iya shiga bathroom gaba daya jikinta yagama jikewa da jini ga wani jinin da yake zuba guda guda manya manya,
Kuka kawai takeyi tana gyara jikinta, wanka tayi da ruwan zafi sannan tafito har lokacin jinin bai tsaya ba.
Komawa tayi ta kwanta tana kuka mai ban tausayi, karfe 9 sai ga abbanta da dr da su yakumbo sun shigo cikin dakin,
Rufe idonta tayi tamkar mai bacci,bincikarta dr yayi yajuyo yana duban su abbanta,
"Yallabai ni ina ganin ayi hakuri akarbi wannan kaddarar kawai domin idan muka matsa yarinyar nan tana iya rasa rayuwarta gaba daya"
"Dr ban fahimceka ba.." Abba yafada cikin rawar baki,
"Gaskiya Alhaji am sorry to say wallahi har yanzu cikin nan bai fitaba yana nan ajikinta gashi tasha wahala ba kadan ba"
"Likita babu ruwanmu da wahalar data sha kawai mu bukatarmu ka fitar da cikin jikinta kota halin yayane, waye yaturata taje tayi cikin, ba ita takai kanta ba" yakumbo tafada cikin masifa,
Sake runtse idanuwanta ikhlas tayi tana mai jin tausayin kanta tareda tsanar wanda yayi mata sanadin shiga cikin wannan kuncin.
No comments:
Post a Comment