_25_
Tunda suka dauki hanya basu tsaya ba har azahar tayi alokacin ne mai motar ya tsaya domin su gudanar da salla, cincin ta siya guda biyu manya wanda dakyar ma ta iya ci saboda tsananin bacin rai ita yanzu tunaninta daya shin tayaya zata fuskanci mahaifiyarta da wannan tashin hankali, agaskiya tasan bata yiwa mahaifiyarta adalci ba domin bataje mata da wani abu wanda zai sakata farin ciki ba sai ma sabaninsa.
Karfe 6 daidai na yamma suka shiga cikin garin Maiduguri, kwatancen da abbanta yayi mata tabi dan haka bata sha wata wahala ba tasamu mai taxi din da zai kaita har gidansu mahaifiyarta,
Banda faduwar gaba babu abinda ikhlas take yi musamman ma da taga sun shigo layin da zai sadasu da gidansu mahaifiyarta,
Adaidai kofar gidan mai taxi ya ajiyeta yana cewa,
"Yawwa mun karaso hajiya"
Kudinsa tabashi ta tsaya tana kallon gidan, babban gidane wanda yasha gini irin na zamani, tabbas dama ta dade da sanin mahaifiyarta yar babban gidace domin mahaifinta yana daya daga cikin manya manyan attajiran garin sannan yayyun mahaifiyarta suma dukkaninsu masu hannu da shuni ne,
Kinkimar jakarta tayi ta tasamma cikin gidan kirjinta yana dukan tara tara, tana shiga taga bangare bangare wanda zasu kai kusan guda biyar,na hannun damanta tabi ta shiga, wata yar dattijuwa ta hango fara sol kamar balarabiya tana alwala atsakar gida,
Da sallamarta ta shiga amma duk jikinta asanyaye yake,
Barin alwalar dattijuwar tayi ta dago ta zubawa ikhlas ido kafin tayi magana da karfi tana nunata,
"Ikhlas ko?" Matar tace da ita,
"Ehh" ikhlas ta mayar mata da amsa tana dan murmushi,
"Ikon Allah, yau kece agidan, zo muje, taho taho, lale lale"
Bin bayan dattijuwar ikhlas tayi zuwa wani bangare nagaba kadan da Wanda matar take ciki,
"Shigo ikhlas yau kece, shiyasa dama nake ta fadawa maman naki tayita hakuri duk daren dadewa zaki nemeta to yanzu ba gashi ba kinzo da kafarki"
Ita dai ikhlas binta kawai take har suka shiga cikin falo anan ta hango mahaifiyarta tana salla, jakarta ta ajiye ta samu wuri ta zauna tana bin falon da kallo,
"Zauna ina zuwa bari naje nadawo" dattijuwar tace da ita tareda ficewa daga cikin falon, tana nan zaune har mahaifiyar tata ta idar da sallar ta jiyo tana kallonta,
"Ikhlas" mahaifiyarta ta kira sunanta cikin mamaki,
"Na'am ammi...." Da sauri ta tashi ta karasa inda take zaune tafada jikinta tafara kukan farin ciki, rungumeta mahaifiyar tata tayi itama tana fitar da kwalla domin rabonta da yar tata tun tana yar shekara biyar aduniya,
"Ikhlas waye ya kawoki?",
"Ammi ni kadai nazo"
Sake rungume juna sukayi, amminta tana kankame da ita tamkar wata jaririya, hawaye kawai ikhlas take fitarwa hakika uwa itace gatan danta shiyasa duk Wanda ya rasa uwa dole yayi kuka,
"Tashi kiyi salla ikhlas sai kici abinci ko"
Janye jikinta tayi daga jikin ammi tana goge hawayen fuskarta,
Daukar mata jakar ammi tayi suka shiga cikin dakin baccinta, alwala tashiga toilet ta dauro tafito tazo tayi salla duk akan idon mahaifiyarta domin tana zaune abakin gado tana kallonta,
Godiyarta tafara kaiwa wurin ubangiji da yabata ikon ganawa da mahaifiyarta,Shafa addu'ar tayi ta tashi ta matsa kusa da ammi,
"Ina wuni ammi"
"Lafiya lau ikhlas, ya mutanen gida, kinzo lafiya, ina abban naki?"
"Lafiya lau ammi"
"Sannu da zuwa"
Mikewa tayi ta isa inda kwanukan abinci ke jere ta dauko mata kwano guda biyu tazo ta ajiye agabanta,
"Ga abinci kici"
Bude abincin tayi biskine aka dafashi wara wara ga miyar kuka agefe wacce tasha busasshen kifi da man shanu nasha nasha, take taji kwadayinta ya motsa abinku da mai ciki,
Bararrajewa tayi tafara kwasar abincin tana yiwa ammi hira gamida tambayar yayunta yan biyu Hassan da Hussain,
"Sai anjima zaki gansu dazu suka fita cikin gari"
"Ammi sun gama karatu?"
"Sun gama karatu mana ikhlas yanzu aiki suke nema"
"Allah yasa su samu ammi"
"Amin"
Tana kammala cin tuwon ammi ta kama hannunta suka fita tafara bin kofa kofa ta gidan tana shiga da ikhlas tana nuna musu ita, kowa sai mamaki yake na girman ikhlas lallai akwana atashi babu wuya, kowacce kofa dake gidan sai da suka shiga hakan yasake gajiyar da ikhlas dan haka koda suka dawo dakin ammi gadonta kawai ta haye ta kwanta tana jin wani farin ciki yana ratsata domin tuni ta dade da manta damuwar da take dauke da ita.
No comments:
Post a Comment