Haka zaman Ikhlas yaci gaba da kasancewa agidan mahaifin ta, gata iya gata abbanta yana nuna mata amma tana fuskantar tsana da kyama daga wurin yakumbo da hajiya Nafi,
Gatan da abbanta yake nuna mata ne ya sake hura wutar tsanarta a zuciyoyin su yakumbo, kullum ita ke shiryawa mahaifinta abincin da zai ci, gyaran dakinsa da duk wani abu da ya shafeshi itace keyi da haka har ta cika wata uku da dawowa.
Sanye take cikin riga da wando na Pakistan milk colour, tana sanye da hular roba baka, tunda ta tashi take aikin shiryawa abbanta abin karyawa,
Wani ciwon ciki taji yana turnuketa ba tare data shiryaba, aikin ta bari ta duka tana tafiya ahankali ta shiga dakinta,
Kan gadonta ta hau ta kwanta tana murkususu, wani irin amai take jin yana taso mata dakyar ta iya tashi da gudu ta fada toilet anan ta shiga kwara amai kamar zata amayar da hanjin cikinta, amai take kwarawa sosai,
Tajima tana aman kafin ya lafa mata tasamu ta kuskure bakinta ta koma daki ta kwanta, lokaci kankani zazzabi ya lullubeta,
Jinta shiru da abbanta yayi yasashi kiran wayarta, lokacin tayi mutukar galabaita,
Dakyar ta iya daukar wayar ta kara a kunnenta,
"Yar abba har yanzu ba agama shirya abincin ba?"
Cikin muryar rashin lafiya tace "abba bani da lafiya"
"Na'am, iye? Ikhlas meya sameki? Bari nazo" wayar ya kashe cikin tashin hankali,
Ahanyarsa ta fitowa yayi kicibus da hajiya Nafi,
"Alhaji ina zaka kuma? Maganar da muka fara jiya nazo mu karasa"
"Hajiya Nafi ba yanzu ba sai wani lokacin, ikhlas ce babu lafiya"
Yana kaiwa nan yayi gaba hakan ya kular da hajiya Nafi ta nufi sashen yakumbo, tana zuwa tahau fada,
"Gaskiya yakumbo nafara gajiya da cin mutuncin da ake yimin agidan nan, Alhaji yafi bawa yarsa muhimmanci fiyeda ni gaskiya nagaji"
Mikewa yakumbo tayi daga kishingiden da take,
"Yana ina? Muje"
Fitowa sukayi suka nufi dakin ikhlas,
Lokacin da abban ikhlas yaje dakin nata tana kwance sai nishi take yi idonta ya rufe,
"Ikhlas, ikhlas, sannu meya sameki?" Yafada arude,
"Abba cikina ne yake ciwo da zazzabi"
"Bari nakira likita, ina zuwa"
Wayarsa ya dauka yafara neman dr dinshi wanda yake dubashi agida Nigeria,
Hajiya Nafi da yakumbo ne suka shigo kowacce fuskarta babu walwala,
Jin yana yin waya yasasu jiran ya gama,yana gamawa yakumbo tahau fada,
"Amadu yanzu kayi adalci kenan? Ka kyauta kenan? Matarka baka bata muhimmanci kamar yadda kake bawa yarka yanzu kayi daidai kenan?"
"Yakumbo yanzu kuma me nayi?"
"Au tambayata ma kake yi? Yayi maka kyau amadu"
Shigowar likita ce ta dakatar dasu, yana shigowa yafara bincikar ikhlas yana yimata yan gwaje gwaje,
Mintuna kadan ya dago yana kallonsu fuskarsa babu annuri,
"Um yallabai, nagama bincikena wanda ya kamata nayi, am sannan gaskiya Nagano yarinyar nan tana dauke da juna biyu na tsawon wata biyar"
Ba abbanta ba hatta ita ikhlas din sai da tayi zumbur ta mike batare da tasani ba,
"Likita ciki? Innalillahi wa inna ilaihir raji'un"
"Wallahi yallabai abinda nafada haka yake tabbas tana da ciki"
Wani kukan kura abba yayi yaje ya damketa, "ikhlas, ikhlas abin kunyar da kika jawo min kenan? Ashe dama wasikar da kika barmin cewar kin tafi yawon karuwanci dagaske kece kika rubuta? Ikhlas abinda zaki yimin kenan ina dan siyasa shahararre ki bata min suna?"
Tarin da ikhlas tafara saboda shakar da abbanta yayi mata ne ya sanya likitan yin saurin kai mata agaji ta hanyar banbare hannun abbanta daga wuyanta,
"Kabarni na kasheta likita, kabarni na kasheta tun kafin ta bata min takarata, ikhlas kin cuceni kin cuci kanki"
"Alhaji hakuri zakayi Dan Allah"
"Likita fita waje zan kiraka"
Fita dr yayi, yana fita hajiya Nafi da yakumbo suka marmatso kowacce fuskarta dauke da murmushin mugunta.
No comments:
Post a Comment