Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Tuesday, 12 December 2017

RUWAN KASHE GOBARA! 21



RUWAN KASHE GOBARAšŸ”„
_21_

 "Kiyi hakuri kinji ikhlas, babu komai duk abinda yafaru dake daga Allah ne,
Bayan tafiyarki babu irin cikiyar da banyi ba amma Allah baisa ansameki ba, ko wanda ya ganki ma ba asamu ba"
Kallonsa tayi yana share kwalla daga idonsa,
"Abba haka Allah ya aiko, shekarata 5 ahali na lalura sai yanzu nasamu lafiya"
"Allah yasake baki lafiya ikhlas"
Amsawa tayi da "amin" daga nan suka cigaba da hira wacce ba arasa ba amma ikhlas ta boye masa maganar anyi mata fyade.
Sai da suka raba dare suna hira har wurin karfe 12 domin ko ada lokacin da tana gida kullum haka take zama atare dashi suyita hira har sai dare yayi nisa sannan takoma dakinta, yau dinma hakance ta faru sai da taji garin tsit sannan tayi masa sallama tatafi.
Dakinta ta koma tayi shirin bacci ta kwanta, Allah Sarki sabo turken wawa inji bahaushe nan kuma taji kewar elmustapha da ni'ima ta kamata tasan da tuni yanzu suna can tare ko ana hira ko kuma an kwanta,
Baccine mai mutukar dadi ya dauketa wanda bata shirya masa ba.
Washe gari tunda asuba ta tashi tana yin salla ta shiga kitchen domin dama tun da can haka ta saba itace take shiryawa mahaifinta abincin da zai ci,
Tana kitchen din tana soye soyenta yakumbo ta shigo afusace,
"Allah ya kawo mu kuma kin dawo zaku fara rabon girki keda matar gida sai kace wasu kishiyoyi, ohhh ni Hadiza ina ganin ikon Allah agidan nan, to bari kiji kina jina? Komai akwai muhallinsa wai an sakawa kuturu sarka ta cire, kibari kije naki gidan sai kiyi wannan ikon amma ba anan ba, shasha kin gama yawon barikinki kin dawo sai da kikaga duniya tayi miki atishawarar kuda sannnan zaki jawo jiki ki dawo dayake ke mayya ce, to ahir dinki"
Duk wadannan maganganun da yakumbo take yi ikhlas bata daga ido ta kalleta ba aikin gabanta kawai take yi har yakumbo ta karaci fadanta ta tafi bata koda kalleta ba,
Girki na alfarma ta shiryawa abbanta ta kinkima ta nufi bagarensa lokacin karfe 7 daidai, akan dining ta shirya masa ta juya ta fita zuwa dakinta,
Wanka tayi ta shirya ta fito cikin doguwar riga ruwan dorawa samfarin Arabian gown lokacin har karfe 8 tayi,
Falon abbanta ta koma yana zaune yasha farar shadda mai tsada yana cin abincin data dafa masa,
"Ikhlas sannu da kokari kinji, Allah yayi miki albarka"
Zama tayi akasa tafara gaisheshi, tana nan zaune har ya kammala cin abincin daidai lokacin hajiya Nafi ta shigo fuska ahade,
"Ikhlas zan fita babu komai ko?"
"Abba babu komai amma ina bukatar phone saboda ina son yin waya"
Murmushi yayi yana gyara babbar rigar jikinsa,
"Akwai waya sabuwa tana nan adakina maza shiga ki dauko, tana nan acikin drewar din gadona"
Mikewa tayi cikeda murna domin dama tana son ta kira elmustapha yau,
"Haba Alhaji, wayar nan fa nice nayi maka sautu nace maka wayata tana bani matsala idan ina yin magana ba afiya jiba har sai na daga murya, amma yanzu shine zaka dauka ka bawa yarka?"
"Haba hajiya nafisa kici girma mana kibarwa yarki"
"Bazata ci girman ba, akan me zata ci girma? Nace bazata ci girman ba, kai amadu kaji tsoron Allah, amadu kadaina fifita wannan yar taka akan matarka" yakumbo tafada tana daga bakin kofa atsaye,
"Ina ake yin haka ya tafi mata daraja in banda awajenka dayake kai sallamamme ne sun gama sabauta ka"
Batare da yayi magana ba ikhlas tafito rikeda kwalin wayar a hannunta ta wucesu zuwa dakinta domin harda sabon sim na etisalat ta dauko Wanda tagani ajiye acikin drewar din,
Fada da masifa yakumbo taci gaba dayi sai da tayi mai isarta sannan ta fice tabar falon.
Daki ta koma taje ta jona wayar a charge, takoma gadonta ta kwanta.
Bata tashi ba sai misalin karfe 12 narana, lokacin wayarta tayi full, sim din ta cire tasaka acikin wayar ta dauko number din elmustapha ta saka ta kira,
Ringing biyu ya daga da sallamarshi,
"Yaya barrister" tafada cikin siririyar muryarta,
"Ikhlas, kece?"
"Nice nan yaya, ina anty ni'ima?"
"Tana gida ikhlas ni ina office, yagida ya mutanen gida?"
"Lafiya lau suna gaisheka, idan ka koma gida ka gaida anty ni'ima"
"Zataji ikhlas zan kiraki anjima"
Kashe wayar tayi tana murmushi domin elmustapha yazama wani mutum mai muhimmanci acikin rayuwarta.
Tun daga wannan lokacin kullum cikin kiranta elmustapha yake safe da rana, yamma da daddare, sabon dake tsakaninsu ya sake karfafa har takai ga elmustapha furta mata kalmar so,
Murmushi tayi tashafi gashin kanta wanda ke kwance akan kafadarta,
"Yaya barrister kenan, babu maganar aure atsakaninmu, ni na daukeka a matsayin yaya dan uwa, bazan taba iya hada kishi da anty ni'ima ba domin tayi min halaccin da bazan manta da ita ba"
"Halaccin me tayi miki? Wallahi ikhlas ina sonki dagaske kuma so irin na aure"
"Bawai ki nayi ba, kawai dai kadauka kamar babu aure a tsakaninmu"
Tun daga nan yashiga yimata naci akan ta yarda ta soshi amma taki tace sam babu maganar aure a tsakaninsu ganin taki yarda yasashi hakura ya kyaleta ba dan yaso ba.

No comments:

Post a Comment

Pages