_20_
Wata jar doguwar riga ta ciro yar kanti mai santsi dama can ita ma'abociyar saka dogayen riguna ce shiyasa ma suka fi yawa acikin kayanta,
Gaban mudubi ta karasa tafara kokarin gyara gashin kanta wanda yake kaya guda,
Tana tsaka da taje gashin natane taji alamun bude kofa, juyawa tayi ahankali, kakarta yakumbo tagani wato mahaifiyar abbanta,
Tsayawa yakumbo tayi tana kallonta cikeda tsana da bacin rai wanda hakan ya bayyana karara akan fuskarta,
"Yar gadon masifa da jaraba da bala'i ashe sai da kika dawo gidan nan? Ai mu tuni muka manta dake saboda munyi tunanin kin dade alahira ashe kina nan araye, yayi kyau idan kin san wata ai baki san wata ba, jarababbiya mai nacin bala'i indai nice wallahi sai naga bayanku keda munafukar uwarki"
Sakin baki ikhlas tayi ta tsaya kawai tana kallon yakumbo wacce a haife yanzu zata kai kimanin shekaru 70 aduniya koma harda doriya,
Kafin ta ankara tuni har yakumbo ta bude kofar dakin tafice tana huci,
Gaban gadonta ta karasa taje ta zauna agefen gadon tana jin wani irin jiri,
Hawayene suka shiga kai komo akan kumatunta, kuka tafara mai cin rai wanda ya kasance aikinta akoda yaushe domin abubuwa biyu take yiwa kukan, nafarko halin data tsinci kanta tun tasowarta sai kuma martabarta data rasa a matsayinta na 'ya mace budurwa wacce bata taba aure ba,
Tadade tana risgar kuka har na tsawon wani lokaci kafin daga bisani ta mike tana mai jin wani irin jiri yana daukarta, daurewa tayi takarasa gaban mirror ta samu ta hade gashin kanta ta tufkeshi wuri daya wanda jelar har saida ta sauko gadon bayanta,
Kan gadon ta koma ta kwanta sakamakon dan zazzabin datafara ji yana shamayarta kamar yadda ya saba.
Karfe 8:30 nadare tana zaune akan abin salla bayan ta idar da sallar isha, hajiya nafi ta shigo cikin dakin tana yan kalle kalle,
"Ikhlas kizo Allah yadawo da mahaifinki"
Tashi tayi batare da tayi magana ba tabi bayan hajiya Nafi domin ita bata san inane dakin abban nata ba,
Ta wani dan lungu taga sunbi har suka isa sashen mahaifin nata, yana zaune shida mahaifiyarshi, ido ya zuba mata lokacin da suka shiga falon,
Kusa dashi ta karasa ta zauna tana jin kamar taje ta rungume shi,
"Ikhlas" mahaifinta yakira sunanta cikin rawar murya tamkar zai saka kuka,
"Na'am abba" ta amsa masa tana kwalla,
"Ikhlas yanzu kin kyauta kenan? Tsawon shekarun nan kina ina?"
Dagowa tayi ta kalleshi tana hawaye "wallahi Abba ina yola can Adamawa state,ban san menene yakaini can ba, nidai kawai tsintar kaina nayi acan ahannun wani lawyer, shine yakaini asibiti yabani dukkan taimakon daya dace har zuwa yau da ya sakoni a mota domin dawowa gida"
Hawayene ya gangaro daga idon mahaifinta saboda tsananin tausayinta,
"Ikhlas dama tabin hankali kikayi? Hauka? Ikhlas hauka fa? Innalillahi, hakika godiya ta tabbata ga Allah wanda yabaki lafiya...!"
Shiru yayi sakamakon katse shi da yakumbo tayi,
"Ya isa haka, wai kai yanzu har ka yarda da wannan tatsoniyar da wannan yarinyar tazo ta shirya maka? Yarinyar da dakanta ta dauki sawunta tafice daga gida tace ta tafi yawon duniya amma yanzu dan ta dawo shine har kake kuka kana murna?"
"Nima dai haka nagani yakumbo" hajiya Nafi ta fada cikin makirci,
"Yarinyar nan fa ita da bakinta tace min duniya zata shiga babu irin bada bakin da banyi mata ba amma taki, sai yanzu da taje tagama barewa duniya gyada ta cinye ta sheka ta Sheka taga babu tsaba sannan zata dawo gida,to wlhi bari kiji, kinyi asara kuma kin bata sunanki Dana uwarki aduniya domin ni baki bata sunan dana ba munafuka mai bakin halin tsiya"
"Yakumbo dan Allah abar maganar nan haka ya isa"
"Iye! Dakyau mai 'ya,yanzu amadu ni kake fadawa haka akan yarka? Yayi kyau"
Mikewa yakumbo tayi tana kallon hajiya Nafi " 'yarnan tashi mu tafi kinji, tashi"
Tashi itama hajiya nafin tayi tabi bayanta suka fice,
Binsu da kallo kawai ikhlas take cikeda mamakin makirci irin nasu kodan bai kamata tayi mamaki ba tunda dama tasan hali,
Juyowa mahaifinta yayi yana kallonta cikeda soda kauna irinta uba da 'ya,
"Ikhlas labarin da kika bani gaskiya ne Kodai akwai kuskure aciki?"
Girgiza kai tayi har lokacin hawaye ne ke zuba daga idonta,
"Wallahi Abba dagaske nake babu karya acikin maganar dana sanar dakai, shi kansa lawyer din da ya taimaka min ma inada number wayarshi zan baka ka kirashi kaji"
Girgiza kai yayi "nayarda dake 'yata ubangiji Allah yayi miki albarka yaci gaba da tsareki"
"Amin abba" ta amsa tana mai share hawayen fuskarta.
No comments:
Post a Comment