Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Saturday, 18 August 2018

Yadda Boko Haram Ke Samun Kudaden Tafiyar Da Kungiyar Su – UN

Yadda Boko Haram Ke Samun Kudaden Tafiyar Da Kungiyar Su – UN.




Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana hanyoyin da kungiyar Boko Haram ke bi ta na samun kudaden da ta ke tafiyar a hare-haren ta a kasashen gefen tafkin Chadi, da suka hada da Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

A cikin wani rahoto da ta fitar a makon da ya gabata, ta bayyana cewa, Boko Haram da sauran rikakkun kungiyoyin ta’addanci na samun kudaden ne ta hanyoyin da suka hada: Kwatar kudade da karfin tsiya, gudummawar da ake ba su a boye, hanyoyin fasa-kwauri, tilasta wa jama’a biyan su haraji na dole da kuma satar jama’a su na garkuwa da su.

Duk wannan bayani ya na cikin Rahoto na 22 na shekarar 2017 mai dauke da yin nazarin yadda kungiyar ISIL, Alwaida da sauran kungiyoyi irin su Boko Haram ke tafiyar da ayyukan su.

An damka wa Kwamitin Tsaro na Majlisar Dinkin Duniya wannan rahoto biyo bayan zartas da kudiri na 1267 na shekarar 1999 da kuma kudiri na 1989 na shekarar 20111 sai kuma kudiri na 2253 na shekarar 2015.

Boko Haram a Arewacin Najeriya ya jawo kisan mutane sama da 100,000, a yanzu sun takaita hare-haren su a jihohin Borno da Yobe da Adamawa.

A cikin rahoton, Majalisar Dinkin Duniya ta ce akwai kungiyoyin addini masu tsauraran akidu daban-daban masu taimaka wa ‘yan ta’adda da kudade.

Ta kara da cewa yawan wadannan kungoyoyin ta’addanci sai karuwa suke yi, sannan kuma a kasashen da abin ya shafa, ‘yan ta’addar su na ta kara cusa wa matasa kaifafen akidu a kasashen na yamma da Sahel.

“Yadda ake hada-hadar tattalin arzaki a yankunan gabar tekun Chadi ba tare da wasu ka’idoji tsaurara ba, hakan na samar wa Boko Haram wata kafar samun kudi ta hanyar tilasta wa jama’a ba su kudade, karbar tallafi daga kungiyoyi, fasa-kwauri, haraji da kuma satar mutane su yi garkuwa da su.”

Wannan rahoto dai Kodinata na Kwamitin Binciken Hanyoyin Toshe Kofofin Boko Haram, mai suna Edmund Fitton-Brown ne ya sa masa hannu tare da hadin guiwar Sakatariyar Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Kairat Umarov.

Daga nan sai majalisar ta ce ta na cikin damuwa sosai saboda matsalar tsaron da ake kara fuskanta da kuma kara kwararar masu gudun hijira a kasashen Najeriya, Kamaru da Chadi.

Ta kuma nuna damuwa saboda yawaitar ayyukan fashi da ta’addanci a kasashen yankin Afrika ta Tsakiya.

Za su yi aiki tare da kasashen da ke karkashin kungiyar ECOWAS domin dakile hare-haren ta’addanci da kuma rikice-rikicen makiyaya da manoma.

No comments:

Post a Comment

Pages