Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Saturday, 18 August 2018

Manyan mata da kanana sunyi zanga-zanga tsirara a jihar Imo (Dalili)

Manyan mata da kanana sunyi zanga-zanga tsirara a jihar Imo (Dalili).



Tsohon shugaban majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya rasu Manyan mata da kanana sunyi zanga-zanga tsirara a jihar Imo (Dalili)

Labarai Mun samu labarin cewa wasu manyan mata da ma kanana sun fita a saman manyan titunan jihar Imo dakea a kudu maso gabashin Najeriya a tsirara domin yin zanga-zangar kin jinin gwamnati bisa cigaba da tsare Nnamdi Kanu da ake cigaba da yi. Su dai matan da suka fito da yawa sun yi ta rera wakokin kin jinin gwamnati tare kuma da bayyana bukatar su ta a sako jagoran kungiyar nan dake fafutukar ganin an raba kasar nan ta Indigenous People of Biafra (IPOB).

NAIJ.com ta samu cewa sai dai tuni jami'an 'yan sandan jihar suka cafke matan kafin daga bisani da yawan su su tsere. A wani labarin kuma, Mazauna gidaje masu saukin kuda na Sardauna dake a karamar hukumar Batagarawa, jihar Katsina sun kai karar daliban jami'ar musulunci ta Al-qalam ga gwamnatin jihar saboda rashin tarbiyyar su. Mazauna unguwar dai a ta bakin mai magana da yawun su Hajiya Hauwa'u MaiJidda sun kai karar daliban ne ga Sakataren gwamnatin jihar Mustapha Muhammad Inuwa.

No comments:

Post a Comment

Pages