Monday, 27 August 2018
Home
Football
Me kungiyar Chelsea ya sakata a kasuwa a kudi mafi tsada da aka taba sayar da kungiyar kwallo
Me kungiyar Chelsea ya sakata a kasuwa a kudi mafi tsada da aka taba sayar da kungiyar kwallo
Me kungiyar Chelsean Roman Abramovic ya saka kungiyar a kasuwa inda yake neman sama da Yuro miliyan dubu 2, kafofin watsa labarai na kasar Ingila da damane suka ruwaito wannan labari kuma dama dangantaka ta dade da yin tsami tsakanin shi da gwamnatin kasar ta Ingila.
Idandai wannan ciniki ya tabbata to kungiyar ta Chelsea zata zama kungiyar kwallon kafa mafitsada da aka taba sayarwa a tarihi wanda a yanzu kungiyar Manchester United ce ke rike da wannan kambin inda aka saye ta akan Yuro miliyan 790 a shekarar 2006.
Abramovic dan shekaru 51 yaki yadda da tayin da me kudin kasar Ingila, Sir Jim Ratcliffe yawa Chelsea akan kudi Yuro biliyan 2 a farkon shekarar nan da muke ciki. Kuma yana da kudi da aka yi kiyasin cewa sun kai Yuro biliyan 9. Saboda maganar hanashi biza da kasar ta Ingila tayi, Abramovic ya zabi ya zama dan kasar Israila.
A shekarar 2003 ne ya sayi kungiyar ta Chelsea akan Yuro miliyan 140 kuma kungiyar taci kofi irin su firimiya sau 5 da Champions League da Europa League da kofin F.A sau 5 a karkashin ikonshi.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Author Details
Ut wisi enim ad minim veniam, quis nostrud exerci tation ullamcorper suscipit lobortis nisl ut aliquip ex ea commodo consequat. Duis autem vel eum iriure dolor in hendrerit in vulputate velit esse molestie consequat.
No comments:
Post a Comment