Monday, 27 August 2018
HAJJIN BANA:- Ranar Litinin Alhazan Nijeriya Zasu Fara Gida
Alhazan Nijeriya da suka samu yin aikin Hajji za su fara dawowa gida a ranar 27 ga watan Agusta insha Allah.
Wannan yana kunshe ne a wata takaddar sanarwa da hukumar Alhazan Nijeriya ta fitar. Hukumar tace kamfanin jirgin saman Saudiyya FLYNAS ne zai fara dauko Alhazan jihar Kogi zuwa filin sauka da tashin jirage na kasa da kasa dake Abuja. Daga Bisani Kamfanonin Jiragen Medview da Maxair su biyo duka a wannan rana insha Allah.
Idan ba'a manta ba dai, Alhazan na jihar Kogi sune suka fara tafiya kasa mai tsarki cikin jerin Alhazan Nijeriya.
Rahotanni sunyi nuni da cewa dukkan Alhazan Nijeriya suna cikin koshin lafiya yayin da hukumar ta NAHCON ke kula da jindadin su.
A daya bangaren kuma, hukumar ta NAHCON ta gargadi alhazai da kada su wuce ka'idar tsaraba wanda ba'a yadda ya wuce nauyin Kilogram 32 da kuma kilogram 8 ba. Hukumar tace wannan karon ma zata tabbatar da wannan doka.
Ana sa ran jigilar dawo da alhazan zai fi tafiya da sauri fiye da zuwan su kasa mai tsarki saboda yanzu a cewar hukumar ta NAHCON, kashi 95 na alhazan sun kammala shirin dawuwa gida.
Rariya.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Author Details
Ut wisi enim ad minim veniam, quis nostrud exerci tation ullamcorper suscipit lobortis nisl ut aliquip ex ea commodo consequat. Duis autem vel eum iriure dolor in hendrerit in vulputate velit esse molestie consequat.
No comments:
Post a Comment