Bamu Yarda Mu Bayarda Dembele Ba Don A Bamu Hazard - Inji Barcelona.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dai ta nuna sha’awarta ta neman dan wasa Edin Hazard bayan da dan wasan ya bayyana cewa yana tunanin barin kungiyarsa ta Chelsea domin samun sabuwar kungiya.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce take zawarcin dan wasan bayan da ta siyar da dan wasanta Cristiano Ronaldo zuwa ga kungiyar Jubentus kuma take ganin Hazard ne zai iya maye mata gurbinsa.
Itama kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta nuna sha’awarta na neman dan wasan inda akayi zargin zata bayar da Dembele a matsayin aro ko kuma ta siyar dashi ga ungiyar kwallon kafa ta Chelsea.
Sai dai kungiyar ta bayyana cewa bazata yarda ta rabu da matashin dan wasan ba wanda ta siya fam miliyan 97 a kakar wasan data gabata daga kungiyar Borussia Dortmund domin yam aye mata gurbin Neymar wanda yabar kungiyar zuwa PSG.
Dembele dai bai fara kakar wasan data gabata cikin nasara ba bayan da a wasansa na biyu a kungiyar yatafi jinya ta kusan wata hudu kuma bayan yadawo yaci gaba da samun matsaloli akai-akai.
Sai dai yana daya daga cikin ‘yan wasan Faransa da suka lashe gasar cin kofin duniya da aka kammala a kasar Rasha a tsakiyar wannan watan.
Majiyarmu leadershipayau.
No comments:
Post a Comment