Yadda Wani Malamin Jami'ar Bayero Ya Nemi Yayi Lalata Dani.
A ziyarar da tawagar Adikon Zamani ta kai Jamai'ar Bayero da ke Kano, wasu dalibai mata da maza sun shaida wa BBC yadda wasu baragurbi daga cikin malamansu suke nemansu domin yin lalata da su.
Daya daga cikinsu ta ce "wani malaminmu ya taba cewa yana so na, amma ko da na nuna masa cewa ni ba wannan ne ya kawo ni makaranta ba sai ya yi min barazanar cewa idan dai ban ba shi hadin kai ba, to ni ma lokaci zai zo da zan fado hannunsa.
"Ganin cewa mun yi haka a dole na fasa daukar madda (course) dinsa saboda tsoron kada na fada tarkonsa, kuma Allah ya taimake ni maddar tasa ba ta dole ba ce, don haka kawai sai na ki dauka," a cewar dalibar wadda ta nemi a sakaya sunanta.
A nata bangaren, Jami'ar Bayero ta ce tana da ka'idoji masu tsauri na tunkarar irin wadannan korafe-korafe.
Shugaban sashin kula da jin dadin dalibai na jami'ar Dr Shamsudden Umar, ya shaida wa BBC cewa makarantar na daya daga cikin wuraren da ba a daurewa irin wannan dabi'a gindi, sannan ya nemi dalibai da kada su ji tsoro wurin bayyana duk wanda ya nemi cin zarafinsu.
Haka shi ma wani dalibi namiji, ya shaida wa BBC yadda ya fada tarkon wani malami kawai saboda yana da alaka da wata daliba da malamin yake nema.
"Lamarin sai da ya kai malamin da abokinsa suka kira ni har ofis suka titsiye ni kan alaka ta da ita saboda suna zargin ta gaya mana cewa yana nemanta bayan da wata kawarta ta kai mai tsegumi."
Sai da na je kare kaina, amma hakan bai yi wani tasiri ba," a cewar dalibin wanda shi ma ya nemi a boye sunansa.
Cin zarafi ta hanyar lalata laifi ne a Najeriya, amma duk da haka ana ci gaba da samun aukuwar lamura irin wannan a jami'o'in Najeriya.
A kwanan nan ne wata dalibar Jami'ar Obafemi Awolowo ta tona asirin wani malamin Jami'ar da ya nemi yin lalata da ita.
Dalibar mai suna Monica Osagie ta nadi tattaunawar da ta yi da wani malaminta da ya nemi yin lalata da ita domin ya ba ta damar cin jarabawa tare da watsa tattaunawar.
Lamatrin ya ja hankalin jama'a a ciki da wajen Najeriya.
Dalibar ta Jami'ar Obafemi Awolowo, ta watsa tattaunawar tata ne da Farfesa Richard Akindele, wanda ke koyarwa a sashin harkokin kasuwanci da hada-hadar kudi na jami'ar, a shafukan sada zumunta.
Lamarin dai ya kai ga jami'ar kafa kwamitin bincike wanda a karshe ya sami malamin da laifi kuma aka kore shi daga aiki.
Mataimakin shugaban jami'ar Farfesa Eyitope Ogunbodede, ya ce an kori Farfesa Richard Akindele ne bayan da ya amsa laifin kulla alaka da daya daga cikin dalibansa ta hanyar da ba ta dace ba.
"Farfesa Akindele ya nemi yin lalata da Monica Osagie domin sauya maki kashi 33 da ta ci zuwa adadin da zai ba ta damar tsallakewa," a cewar Ogunbodede.
Kusan wannan ne karo na farko da za a iya cewa wata makaranta ta dauki hukunci a bainar jama'a kan irin wannan aika-aika da aka dade ana zargin wasu malaman jami'a da aikata wa.
Kuma babu shakka matakin da Monica ta dauka na tona asirin malamin ya samu karbuwa a wurin daliban jami'a a sassan kasar da ma sauran jama'ar gari, saboda halayya ce da ta dade tana faruwa ba wai a Najeriya kawai ba.
Sai dai a cewar Dr Shamsudden Umar ya ce BUK ta bude wani ofis na musamman mai cin gashin kansa domin bai wa dalibai damar kai korafe-korafe masu kama da irin wadannan.
Ya kara da cewa babu wani malami da za a dagawa kafa idan aka same shi da laifi, yana mai bai wa dalibai kwarin gwiwa domin su bayyana duk wani bara-gurbin malami da suka sani.
No comments:
Post a Comment