Wata Babbar Kotu A Nijeriya ta Bada Umarnin a Cire "Shugaba Muhammadu Buhari" daga kujerar shi.
- Wata babbar kotu a Najeriya ta umarci majalisar dokokin kasar ta gaggauta fara aiwatar da bin matakan tsige Shugaba Muhammadu Buhari.
Alkalin babbar kotun da ke garin Osogbo jihar Osun ya bayar da umarnin ne a ranar Laraba bisa karar da wasu 'yan Najeriya biyu suka shigar a gaban kotun.
Wani lauya Kanmi Ajibola da Sulaiman Adiniyi wani dan rajin kare hakkin dan Adam ne suka bukaci kotun ta ba majalisa umarnin gaggauta tsige Shugaba Buhari.
Batun takardun shaidar kammala karatun sakandare na Buhari na daga cikin bukatu hudu da mutanen biyu suka gabatar a gaban kotun, inda suke zargin shugaban da saba wa kundin tsarin mulkin kasar bayan rantsar da shi da takardun da suka kira na bogi.
Sai dai tun lokacin yakin zabensa ne kwalejin gwamnati a Katsina, inda Buhari ya kammala sakandare ta fitar da takardar shaidar kammala karatun a shekarar 1961.
Zuwa yanzu gwamnatin Buhari ba ta ce komi ba game da batun, yayin da kuma take da damar daukaka kara game da umurnin na kotun.
Sannan majalisar dokokin kasar ba ta ce komai ba zuwa yanzu.
No comments:
Post a Comment