Maryam Both ta Jinjinawa Sojojin Nigeria a Wani Yanayi na Burgewa.
- Jarumar Fina-finan Hausa ta jinjina musu kan irin gudunmawar da suke bayarwa
Shahararriyar jarumar finafinan Hausa ta Kannywood Maryam Booth ta dauki wani sabon hoto wanda ta yi domin nuna goyon baya da kuma tunawa da sojojin kasar nan wadanda suke gumurzu domin kare kasar nan a fagen fama a sassa daban daban na kasar nan.
Sannan tayi gajeren rubutu kamar haka "Domin tunawa da sojojin da suke gwagwarmaya domin kare mu da kuma kasarmu baki daya, Allah ka albarki sojojin Najeriya".
Bayyana wannan sako nata dai ana ganin zai karawa sojin kasar nan kaimi da kwaringwuiwa musamman bayan rahotannin da suka gabata na cewar sojoji 23 sun bace a sakamakon harin yan tada kayar baya na Boko Haram suka kai musu.
No comments:
Post a Comment