Jeff Bezos ya kafa tarihi inda ya zama wanda ya fi kowa mallakar dukiya a tarihin Duniya. Bezos shi ne Mai kamfanin nan na Amazon. A bana dai ya kerewa Bill Gates a sahun masu kudin Duniya.
Shugaban Kamfanin na Amazon Jeff Bezos mai shekaru 54 a Duniya ya mallaki abin da ya haura Dala Biliyan 100 wanda Bill Gates ya taba mallaka a shekarar 1999. Tun wancan lokaci ake ji da Mista Bill Gates cikin Attajiran Duniya.
A kusan shekara guda dai Bezos ya samu sama da Dala Biliyan 52. Wannan makudan kudi dai sun fi gaba daya abin da mai kudin Nahiyar Asiya. A tarihin Duniya dai ba a taba ganin mutumin da ya mallaki wannan makudin kudi ba.
Mai kudin nan Bill Gates wanda shi ne Shugaban Kamfanin Microsoft ne na biyu a Duniya inda yake da kusan Dala Biliyan 100. Warren Buffet kuma ne na uku a jerin Attajiran Duniya inda shi kuma ya ba Dala Biliyan 83.
Tun shekaru 23 da suka wuce Bill Gates yake cikin Attajiran Duniya. Yanzu dai an samu wani Attajirin da ya sha gaban Mista Bill Gates. Bill Gates ya mallaki kudin sa ne ta harkar komfuta.
No comments:
Post a Comment