Friday, 29 June 2018
Muna Godiya Ga Magoya Bayan Mu Inji Mikel-Obi
Mikel Obi, kuma kyaftin din tawagar Super Eagles ta Nijeriya, John Obi Mikel ya bayyana cewa yan wasan tawagar sunyi iya yinsu domin ganin sun samu nasara a wasan da suka sha kashi a hannun kasar Argentina daci 2-1 a wasan karshe na cikin rukuni a gasar cin kofin duniya.
Obi ya bayyana hakane bayan antashi daga wasan wanda yazama dole sai Najeria tasamu nasara ko kuma ta buga canjaras idan har tanason ta tsallake zuwa mataki na gaba amma kuma tayi rashin nasara.
Dan wasa Leonel Messi ne yafara zura kwallo a ragar Nijeriya kafin daga baya kuma Nijeriya ta farke daga bugun fanareti bayan andawo daga hutun rabin lokaci ta hannun dan wasa Bictor Moses kafin kuma dan wasan Manchester United, Marcos Rojo ya kara kwallo ta biyu a ragar Nijeriya a minti na 86 da wasan.
“Haka wasan ya kasance domin munyi kokari don ganin mun samu nasara amma kuma bamu samu ba musamman bayan andawo daga hutun rabin lokaci sai dai yan wasan matasan yan wasa ne kuma nan da shekaru hudu masu zuwa zasu sake samun gogewa sosai” in ji Obi Yaci gaba da cewa “Ina alfahari da yan wasanmu domin kowa yayi kokarin ganin mun fita kunya amma duk da haka munyi kokari yadda yakamata kuma zamu cigaba daga inda muka tsaya kuma muna godiya ga ‘yan Nijeriya da suke gida suke goya mana baya”
Nijeriya zata cigaba da buga wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin nahiyar Africa a watan Satumba da kasar Sychelle.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Author Details
Ut wisi enim ad minim veniam, quis nostrud exerci tation ullamcorper suscipit lobortis nisl ut aliquip ex ea commodo consequat. Duis autem vel eum iriure dolor in hendrerit in vulputate velit esse molestie consequat.
No comments:
Post a Comment