Tuesday, 12 June 2018
Donald Trump ya Hadawa Musulmi Shan Ruwa a Radar White House
Wannan shine karo na farko a tarihin kasar Amurka, da shugaban kasa ya kira shugabannin musulman duniya buda bakin azumi a fadar White House
Wannan shine karo na farko a tarihin kasar Amurka, da shugaban kasa ya kira shugabannin musulman duniya buda bakin azumi a fadar White House. Shugaba Donald Trump wanda ya karbi mulki shekara daya da rabi da suka gabata, ya shirya walimar buda baki a fadar White House ta kasar Amurka
Shugaban kasar na Amurka yayi watsi da al’adun fadar ta White House, inda ya aikawa shugabannin musulman duniya goron gayyata, domin su halarci buda bakin daya shirya domin su. Fadar White House din taki bayyana sunayen wadanda suka samu halartar buda bakin, amma dai wasu majiyoyi daga fadar sun tabbatar da cewa a cikin wadanda suka samu damar halartar wannan walimar shan ruwa akwai wakilan kasashen Larabawa, irin su Saudiyya, Dubai, Jordan, Turkiyya, Masar, Tunusiya, Iraki, Bahrain, Qatar, Aljeriya, Libya da kuma kasar Morocco.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Author Details
Ut wisi enim ad minim veniam, quis nostrud exerci tation ullamcorper suscipit lobortis nisl ut aliquip ex ea commodo consequat. Duis autem vel eum iriure dolor in hendrerit in vulputate velit esse molestie consequat.
No comments:
Post a Comment