Sunday, 1 July 2018
Gomnan Bauchi Zai Fito a Matsayin Dan Wasa a Wani Film din Rahama Sadau
Gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Muhammed Abubakar, zai fito a cikin wani shirin fim da Rahama Sadau zata fito a matsayin jaruma.
Ana cigaba da daukar shirin mai taken "Up North" wanda zai fito cikin harshen turanci.
Kamar yadda wanda ya tsara labarin shirin, Editi Effiong, ya bayana gwamnan ya bada gudunmawa wajen shirya fin din.
A sakon da ya wallafa a shafin sa na Twitter, Effiong, ya sanar cewa Alhaji Muhammed Abubakar, ya bada goyon baya wajen amfanin da kambun daji na Yankari wajen shirya fim din kuma ya bada motocin sa yayin da ake neman motocin ayari domin maye wani matsayi na shirin.
Bayan haka, ya kuma bayyana cewa gwamnan ya amince da fitowa a wani matsayi na shirin bayan ya nema masu dama na daukar wani yanki na shirin a fadar sarkin Bauchi.
Gwamnan dai yace ya dalilin da yasa ya taimaka wajen hasaka shirin shine domin farfado da harkar kasuwanci a jihar Bauchi.
Yace tun ba yau yake neman masu shirya fim a Nijeriya da su taho jihar domin shirya wasa.
Daga karshe gwamnan yana mai kyautata zato cewa, matsayin da ya dauka na fitowa a cikin shirin wasan kwaikwayo zai baiwa matasa karfin gwiwa wajen yin sana'ar ga masu sha'awar yin haka.
Shirin zai samu hasakawar fitattun yan wasan kamar, Rahama Sadau da TBoss,, Banky W, Michelle Dede, Ibrahim Onimisi-Suleiman, Akin Lewis, Hilda Dokubo da Kanayo O Kanayo.
Shirin wanda take bada labarin soyayya, siyasa da zamantakewa zai fito ga kasuwa cikin watan Disamba na bana.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Author Details
Ut wisi enim ad minim veniam, quis nostrud exerci tation ullamcorper suscipit lobortis nisl ut aliquip ex ea commodo consequat. Duis autem vel eum iriure dolor in hendrerit in vulputate velit esse molestie consequat.
No comments:
Post a Comment