_54_
Sai wurin sallar magrib sannan ikhlas ta sauka,
Gajiya iya gajiya ta gaji sosai, dan haka koda takarasa gida salla kawai tayi taci abinci ta kwanta,amma ko minti biyar batayi ba da kwanciyar lamido ya kirata kan ta kawo masa yaronshi zai ganshi,
Tashi tayi tana zumbura baki tasa hijab ta fita,
Wai! Ai lamido naganinta yaji ya rikice saboda kyawun da yaga tayi masa, bai jima ba ya tafi ya nufi wurin baffa anan ya tayar da darun shidai nan da wani satin yake son adaura masa aure da ikhlas nan da watanni uku masu zuwa kuma sai ta tare,
Ganin ya damu yasa baffa amincewa amma da sharadin sai yaji ta bakin ikhlas din, washe gari Baffa ya sameta adaki da maganar, bata ki ba saboda tana son ta cikawa marigayi burinshi kamar yadda yabar mata wasiyya duk da tasan zata sha fama da lamido idan ya zama mijinta saboda sunada mabanbantan ra'ayi shida marigayi,
Acikin kwanaki uku kacal aka gama shirye shiryen bikin ikhlas da lamido, amma har yau bata ga idonshi ba,
Aranar juma'a aka daura auren, sai aranar yazo gidan yasha farin yadi kanshi babu hula, yanzu kam kansa tsaye zai shiga dakin domin ta zama mallakinsa,
Abakin gado ya sameta tana zaune tana shayar da sadiq, sai da ya shiga cikin dakin sannan yayi sallama, cikin sauri ta sauke rigarta ta janye sadiq,
Amsa sallamar tayi kanta akasa, hannu ya mika ya karbi sadiq yana mai bin hannunta da kallo saboda har lokacin kunshin hannunta yana nan bai goge ba,
Fita yayi da sadiq a hannunshi ya tasamma wurin innah, ajiyar zuciya ikhlas ta ajiye tana kallon kofa,
Bai jima awurin innah ba ya fito ya koma dakinta ya mayar mata da sadiq ya tafi gida,
Afalo ya iske fadila da ihsan kowa tana harkar gabanta,
Duk wanda yaganshi yasan yana cikeda farin ciki domin hakan ya kasa boyuwa akan kyakkyawar fuskarsa,
Zama yayi a kujerar tsakiyarsu,
"My fadila my ihsan dama ina son magana daku,ina son sanar daku cewa yau nayi aure na karo muku abokiyar zama"
Kallo suka bishi dashi dukkaninsu kallo irin na mamaki,
"Aure fa? A ina?" Ihsan ta tambayeshi,
"Ehh, amma ba wata bakuwar fuska bace kun santa, ikhlas ce maman sadiq"
Shiru kowaccensu tayi domin dama sun dade da zargin sonta yake amma abin yazo musu da sauki saboda ganin yanda yaketa rawar jiki basu zaci bazawara ya aura ba har da d'a,
Jin basu yi magana ba yasashi mikewa ya wuce ciki,
Nannauyar ajiyar zuciya fadila ta ajiye ta kalli ihsan,
"To ihsan kin dai ji yanda yace so yanzu ya rage garemu musan abinyi"
"Kamar yaya fa?" Ihsan ta bukata,
"Ina nufin yanzu lokaci yayi Wanda zamu hade kanmu mubar fada mu ajiye kishi agefe mu tarairayi mijinmu cikin kissa mu rabashi da waccar tsohuwar domin idan ba haka muka yi ba to wallahi yan kallo zamu zama idan ta shigo cikin gidannan nan kuma kinga tafimu shekaru gashi ta taba aure kuma shima yana sonta domin da ace baya sonta da bazai aureta ba, dan haka muyi karatun ta nutsu mu nemi mafuta kar mu bari tafimu fada awurinsa"
Dagowa ihsan tayi ta dafa kafadar fadila "hakika wannan shawara taki tayi kuma naji dadinta, idan har tayi kuskuren shigowa gidan nan to sai tayi dana sani domin sai mun hanata sukuni sai mun hanata jin dadin zaman aure, zamu tanadi makirci da sharri kala kala agareta, hmmm balle ma abin zai zo mana da sauki tunda bazawara ce kinga ta cikin ruwan sauki zamu cinma burinmu na fitar da ita daga cikin gidan nan"
"Yawwa ihsan ashe kin fahinci inda na dosa, wallahi Lamido ya mace akanta irin mutuwar da bazai rayuba har abada, kigafa irin kulawar da yake bata sai kace ita tafi kowa" fadila tafada tana murmushin takaici,
"Kibarta zamuyi maganinta" inji ihsan, da wannan shawarar suka tsayar da matsaya,(kunji fa masu karatu fadila da ihsan yanzu an hade kai domin fitar da ikhlas).
No comments:
Post a Comment