_53_
Sai da ikhlas taji fitarsa sannan ta fito ta shirya, ganin shiru shiru bai dawo dashi ba ya sanyata dibar kayan da za asawa sadiq din tafita tabishi falo,suna zaune shida innah da sadiq akan cinyarshi yakama hannayenshi,
"Ga kayansa" ta mika masa,
"Ungo saka masa ki mikoshi" karbarsa tayi ta saka masa kayan ta mika masa shi tatafi,
Bai dawo dashi ba sai wurin 12 shidinma saboda tafiya zaiyi shiyasa,
Mika mata yaron yayi ya juya zai tafi,
"Abban sadiq.." Yaji ta kira shi, tsayawa yayi batare ya jiyo ba,
"Gobe zan kai sadiq allura a asibiti"
"Allah ya kaimu" yabata amsa tareda yin gaba sai dai har cikin ransa yana jin dadin wannan sunan da take kiranshi dashi,
Daki takoma inda su ammi suka gama shirinsu tsaf domin tafiya Maiduguri,
Lokacin da zasu tafi ikhlas harda kukanta, nan suka tafi suka barta daga ita sai hajiya kakarta.
Washe gari da safe lamido yaje daukarta domin kaita asibitin, ba karamin kyau tayi ba domin wata koriyar atamfa wax tasaka wacce tasha dinki mai kyau, farin mayafi tasaka da farin takalmi idan kaganta bata da maraba da amarya,
Gaban motar ta shiga ta zauna suka tafi, suna hanya wayarshi tafara ringing, dubawa yayi yaga xahar ce dan haka yaki picking, jin ta dameshi da kira yasashi dagawa,
"Hello zan kiraki anjima"
Taji yafada tareda katse wayar, ko wacece kuma oho ko kuma data daga cikin matanshi ne, ta raya hakan aranta, har sukaje asibitin babu wanda yayi magana acikinsu,
Bata wani jima ba tagama abinda ya kaita ta dawo wurin Lamido ya dauko hanyar dawo dasu gida, wayar ikhlas ce tafara kara dan haka ta lalubota acikin jaka, sunan elmustapha tagani nan ta dauka da fara'arta,
"Yayana nayi fushi ai tunda baka zo kaga danka ba" tafada tana murmushi,
"Yanzu gani nan ai zanzo na wanke laifina, kina gida?" Elmustapha ya bata amsa daga daya bangaren,
"Ehh, to sai kazo" tafada gamida katse wayar,
Hade rai lamido yayi, lokacin da suka karasa gida daidai lokacin elmustapha ya karaso ya fito ya tsaya ajikin motarshi,
"Bani yarona" lamido yafada gamida dauke sadiq daga kan cinyarta,
Tsayawa sororo ikhlas tayi tana kallonsa, shi wannan wai meye nufinsa ne? Yanda yake nuna mata gadara akan yaron nan ko shine ya haifeshi iyakaci kenan,
Bata gama tunanin da take yi ba taji ya balle murfin kofar yafita da sadiq akafadarsa,
Tashi tayi tafita ta nufi wurin elmustapha,
Murmushi yake aika mata yana kallonta,
"Maman boy rowar ganin boy din ake yimin ne?" Inji barrister elmustapha,
"Ni na isa? Daga asibiti muke ne kuma sadiq din muka kai"
"Ayya Allah ya bashi lafiya"
Gaisawa suka danyi suka taba yar hira sannan yayi mata sallama zai tafi, wata katuwar leda mai kyalli ya dauko wacce take cikeda kayan jariri iri iri,
Godiya sosai ikhlas tayi masa ta juya ta shiga cikin gida da ledar kayan a hannunta.
Lokacin da lamido ya shiga cikin gida duk ranshi abace yake domin yagama fuskantar inda elmustapha ya dosa yasan son ikhlas yake yi sai dai amma awannan karon shi bai shirya rabuwa da itaba shiyasa ma zaiyi duk iya yinsa naganin bata kufce masa ba,
Wurin baffa ya shiga ya sameshi shida innah zaune suna tattaunawa,
"Har kun dawo?" Inna ta tambayeshi,
"Ehh innah" yabata amsa tareda zama akan kujera,
"Baffa dama cewa nayi tunda maman yaron nan ta haihu sai ayi maganar daurin auren ko..?" Yafada cikin dakewa,
Murmushi baffa yayi yace "hakane lamido amma mu da bari mukayi har sai tayi arba'in tukunna"
"To shikenan baffa Allah ya kaimu"
"Amin amin" tashi yayi ya fita daidai lokacin ikhlas ta shigo dauke da kayan da elmustapha ya bata,
Binta yayi zuwa dakinta domin bata sadiq, ajiye kayan tayi awurin hajiya tana cewa "barrister elmustapha ne ya kawowa sadiq.."
Fita tayi domin karbo sadiq ahannun lamido, mika mata sadiq din yayi yace,
"Kar ki kuskura ki sakawa yarona wannan kayan da wancan mutumin ya kawo"
Yana gama fadin haka ya juya yayi tafiyarsa,
Tsayawa tayi tana kallonsa abin nasa ma abin dariya "lallai abban sadiq"
Tafada tareda shigewa dakinta. Haka taci gaba da kulawa da yaronta, lamido kuwa kullum yana gidan sannan duk wani nauyi na sadiq to a wuyansa yake da haka har sukayi arba'in alokacin suka fara shirye shiryen zuwa Maiduguri, kwanansu arba'in da shida suka tafi itada hajiya amma ita hajiya bazata dawoba,
Lamido bai so wannan tafiyar ba amma dolenshi babu yanda zaiyi, sai dai fa amma kullum cikin yiwa ikhlas waya yake yana tambayarta ya boy dinshi,
Tunda sukaje ammi da hajiya suka fara gyarata domin baffa yace tana komawa daura aurensu za ayi da lamido inyaso daga baya ta tare wannan shine burin lamido domin idan aka daura auren hankalinsa zai fi kwanciya ko bata tareba yasan dai mallakinsa ce,
Gyara iya gyara anyiwa ikhlas nan tayi kyau tafito fes tamkar budurwa, tunda taje kullum tana makale da abdalla wanda yanzu ya sake zama dan saurayi,
Satinta biyu ta shirya ta koma yola bayan tasha gyaran jiki dana gashi da kunshi samfarin na yan Sudan, ga wasu turarurruka da humra masu dadin kamshi da ammi ta hada mata baya ga turaren wuta mai dadi wanda yake sati kamshinsa bai fita ba.
No comments:
Post a Comment