_69_
RUWAN KASHE GOBARA 1
Tashi yayi ya rufe laptop din ya fita, ya zama dole yaje ya samo mata makarantar da take bukata domin baya son abinda zai sa tayi kewar tsohon mijinta,
Fita yayi daga gidan ya nufi makarantar da ikhlas din ke son shiga,
Sabon foam ya siyo mata da uniform da littattafai amma kuma yanzu makarantar hutu suke yi sai nan da sati biyu sannan zasu koma,
Kayan ya diba ya nufi gida daidai kwanar da zai shiga ta sadashi da gidanshi yaga kiran baffa yana shigowa cikin wayarshi, sai da gabanshi ya fad'i domin duk azatonshi k'ararshi ikhlas ta kaiwa baffa dan haka atsure ya daga wayar,
"Lamido idan Allah ya kaimu gobe kuzo gida kaida ikhlas za ayi rabon gadon nan domin angama tattara komai, kuma yau an fitar da kudin mamacin.."
Wani sanyi lamido yaji jin cewar ba kararshi ikhlas takaiba,dan haka yayi saurin amsawa baffa,
"To baffa insha Allah zamuzo goben fata dai Allah ya jikanshi da rahama"
"Amin lamido" baffa ya fada tareda katse wayar,
Wani tausayin iyayenshi da na sauran yan uwanshi yafara ji domin yasan yanzu mutuwar dawo musu zatayi sabuwa musamman ma innah, kwalla yaji ta ciko idonshi ya goge, ahaka ya karasa gidan, kai tsaye dakin ikhlas ya shiga wanda rabonshi da shiga har ya fara mantawa,
Tana kwance ta rungume sadiq idonta yayi ja da alama kuka tayi, jin ranshi yayi ya sosu zuciyarshi tayi masa baki domin ya tsani abinda zai sakata kuka bare kuma ace shine yasata,
"Ga foam din nan na karbo miki harda littattafai da uniform amma yanzu sunce acikin hutu suke sai nan da two weeks zasu koma.."
Banza tayi mishi taki koda kallon kayan domin wani irin haushinshi take ji musamman ma maganar da ya fada mata dazu wai a makaranta yaga su ihsan har ya fara sonsu, wannan maganar tayi mutukar tsaya mata arai,
Jin taki yi masa magana ya sashi ajiye mata kayan ya dauki sadiq wanda keta faman yi mishi dariya ya juya ya fita,tun daga nan bata sake ganinshi ba saboda ko lokacin da ya dawo da sadiq ma tayi bacci,
Kusa da ita yaje ya kwantar da sadiq ya tsaya yana bin jikinta da kallo, tasha rigar bacci pink colour mai santsi wacce tsayinta bai wuce iya cinyarta ba, gashin kanta kuwa ta tufkeshi a keyarta da pink din ribbon,lips dinta ya kalla wadanda ke burgeshi akoda yaushe domin kullum kamar ta shafa musu jan baki suke, ahankali ya sunkuya yayi kissing din bakinta ya juya ya fita da sauri gabanshi sai faman faduwa yake yi ga wani irin sabon shaukin ikhlas dake fusgarshi, sam ikhlas bata sanma ya shigo dakin ba balle tasan abinda ya faru kawai dai cikin dare ta farka taga sadiq akusa da ita a kwance.
Da safe misalin karfe 9 tana zaune agaban mirror tana shiryawa ya shigo cikin dakin fuskarshi babu yabo babu fallasa yana sanye cikin sky blue din shadda da hula,
"Idan kin shirya ki sameni a falo zamuje gidan baffa yau za araba gadon nan"
Bata bashi amsa ba ya juya ya fita domin yasan ba bashi amsar zatayi ba,
Yana zaune a falon ta fito ta sameshi, tashi yayi ya fita tabi bayanshi har zuwa wurinda motarshi take, budewa tayi ta shiga ta zauna, har sukaje gidan innah babu wanda ya tankawa wani asalima radio lamido ya kunna maganin zaman kuramen da suke yi,
Sun samu gidan cike da yan uwa da malaman da zasuyi rabon gadon ga suhaimat ma kishiyar ikhlas tada da yaranta sunzo,wuri ikhlas ta nema ta zauna bayan sun gaiggaisa da mutanen wurin, take ta fara hawaye a boye batare da ta bari an ganeba, duk lamido yana kula da ita yasan kuka take shiyasa shima ya tsinci kanshi cikin bacin rai hakan tasa koda aka gama rabon gadon sai ya tafi ya barta agidan saboda yaga suhaima ma tace sai da daddare zata tafi, yasan hakan zai saka prettynshi farin ciki, zahiri kuwa taji dadi kuma tayi farin cikin zaman gidan domin wuni suka yi suna hira itada suhaimat sannan yaran suhaimat din sai daukar sadiq suke yi suna cewa ga kaninsu ga k'aninsu.
Sai da misalin karfe 8:30 sannan lamido yazo daukarsu, har dasu suhaimat ya hada ya debesu gaba daya, su suhaimat din ya fara kaiwa gida ya ajiye,
"Lamido ba zaka shiga wurin mutuniyar taka bane..?" Suhaimat tace dashi bayan ta fita daga cikin motar,
"Ki gaisheta kawai, sai wani lokacin na zo" ya bata amsa ya tada motar yayi gaba, ita dai ikhlas na jinshi amma bata san ko akan wa suke maganar ba,dan haka ta dauke kanta har suka je gida bata kalli inda yake ba.
Haka zaman nasu yaci gaba da tafiya har tafara shirye shiryen fara zuwa makaranta,ana igobe zata fara zuwa ta nufi dakin lamido domin sanar masa saboda tasan shi ya manta da maganar,
Wannan shine karo na farko da zataje dakinshi domin bata san ma ya kalar dakin takeba tunda ba taba shiga tayi ba, ahankali ta murda kofar dakin ta shiga, babu karya dakin ya tsaru yayi kyau komai ya hadu,
Yana kwance yayi rub da ciki yana daddanna laptop jikinshi ko riga babu daga shi sai gajeren wando ga ihsan kuma tana kwance a bayanshi ta rungumeshi,
Ikhlas ji tayi kamar ta juya amma sai ta daure ta tsaya,
"Abban sadiq dama zuwa nayi na fada maka gobe zan fara zuwa makarantar.." Ta fada ranta babu dadi zuciyarta kuwa tamkar zata faso kirjinta ta fito dan takaici,
"Naji" shine kawai abinda ya fada ya maida hankalinshi kan laptop dinshi da yake aiki,
Juyawa tayi ta fita wani irin haushi yana turnuke zuciyarta, zama tayi dirsham akan gado ta kasa kwanciya,domin tarasa gane kishine yake damunta ko me? Haka ta zauna tanata sake sake acikin ranta har dare yayi nisa, dakyar ta lallaba ta kwanta bacci ya saceta.
K'arfe 9 na safe ta shiga kitchen ta dora dan wake gefe kuma fadila ce itama tsaye tana soya doya da kwai, kowa aikinshi yake yi babu ruwanshi da dan uwanshi, lamido ne ya shigo kitchen din shida ihsan daidai lokacin da fadila zata fita, tare kofar yayi ya hanata fita,
"Morning my fadila.." Ya fadi yana kai mata kiss a kumatu,
"Morning my dear"
Rikota yayi yana dariya "ki tsaya mana mu gaisa"
"My lamido sauri nake yi saboda 9:30 zan shiga lecture dan Allah kabari.." Ta fadi a shagwabance,
"Allah sai na baki morning kiss sannan zaki wuce" ya fadi yana kokarin hadata da jikinshi, kiss ya manna mata a kumatunta ya saketa yana dariya,
"Me kika soya ne?"
"Doya na soya" tabashi amsa ta wuce tana murmushi, cikin kitchen din ya karasa shiga yana yiwa ihsan magana,
"My ihsan ko doyar zaki soya mana muma?"
"Nidai wallahi a'a soya doya akwai wuya gashi ni bacci nakeji, jiya ka hanani bacci kuma yanzu kazo ka nata sani aiki.." Ihsan ta fadi hakan a shagwabance,
"Sorry dear ai zakiyi baccin yanzun nan, kawo na tayaki" ta bayanta ya tsaya ya zira hannuwanshi ya amshi wukar hannunta ya fara fere mata doyar, wata wukar ta sake dauka itama tafara ferewa,
Ikhlas na tsaye tana sakin dan wakenta acikin ruwa amma duk ranta ajagule yake domin ta fara gajiya da wannan cin kashin da lamido yake yi mata, ji take kamar ta tafi tabar girkin nata inyaso idan sun gama nasu sun fita tazo ta karasa nata amma kuma shi dan wake ba irin girkin da za ayiwa haka bane, idan tayi masa haka kwabewa zaiyi dan haka ta daure ta zauna taci gaba.
WhatsApp: 08161892123
No comments:
Post a Comment