Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Friday, 19 January 2018

RUWAN KASHE GOBARA! 68



_68_

RUWAN KASHE GOBARA 1

Bin bayanshi da kallo tayi tana nazarin maganganun da ya fad'a mata, wato shima yanzu laifinta yake gani kenan maimakon yaga laifin kansa, girgiza kai tayi ta yi dan karamin tsaki ta d'auki sadiq ta rungumeshi,
Kuka take son yi amma ta gagara saboda dalilin da ko ita kanta bata sani ba, tana nan rungume dashi har ya farka dan haka ta tashi zaune tayi feeding dinshi sannan ta d'aukeshi zuwa bathroom tayi mishi wanka tazo ta shiryashi tana yi tana tunanin abdallah domin kwana biyu bata samu sunyi doguwar hira dashi ba gashi kowanne lokaci sai taji ya fado cikin ranta sannan kuma sai yanzu ne take ganin matsananciyar kamar dake tsakaninshi da lamido domin hatta kwayar idon yaron irinta lamido ce sak, har yan yatsunshi da farcenshi duk irin na lamido ne, jar riga da blue din wando ta saka masa ta daukeshi ta goyashi ta fita zuwa kitchen akaro na farko,
Tunda ta fito take bin tsakar gidan da kallo domin bata san yanda yakeba, babban falo ta shiga saboda ta cikinshi kitchen din yake,fadila ce azaune taci gayu sosai cikin pink din shadda tana yin karin kumallo, babu wanda ya kula wani ikhlas ta shiga kitchen din, ganin kayanta tayi jere a gefe daya da sauran kayan amfaninta irinsu gas,fridge da makamantansu, can bari daya kuma store ne cike da kayan abinci aciki,
Gas ta kunna ta dora jalop din taliya da dankali, babu bata lokaci tayi ta gama ta sauke ta zuba acikin food flask ta dauka ta nufi dakinta, lokacin da ta fito fadila bata nan ta tashi hakan yasata tabe baki aranta tana tunanin ko wacece wannan kuma?
Daf da zata shiga dakinta ta hango ihsan itama zata fita tana rike da lecture notes da key din mota sai shan kamshi take yi,
Dakinta ta bude ta shiga ta zauna a falo ta kunna kallo wanda sam ba dadinshi take ji ba kawai dai tana yine maganin zama shiru.
Har dare yayi bata kara jin labarin lamido ba sai da ta fita zataje kitchen domin dumama taliyar da ta dafa da rana, a falo ta ganshi shida ihsan da fadila yana zaune a tsakiyarsu suna kallo, kamar ta juya ta fasa zuwa sai kawai tayi fuska taje ta wuce ta shiga cikin kitchen, tunda lamido ya ganta hankalinshi da nutsuwarshi suka tattara suka koma kanta,
"Darling baka gabatar mana da amaryar ba fa" ihsan tace dashi tana jingina ajikinshi,
"To ba gata can kun ganta ba" ya bata amsa,
"Ehh amma duk da haka ai ana gabatar da amarya kuma itama ana gabatar mata da wadanda tazo ta samu" fadila ta saka baki hannunta rike da remote tana kokarin canja channel,
"Sai kuyi kuma.." Ya basu amsa yana murmushi,
"Kenan dai nufinka ba zaka gabatar damu awurunta ba, itama ba zaka gabatar da ita awurinmu ba?" Ihsan ta sake tambayarshi tana makale hannunta cikin nashi,
Kafin ya bata amsa har ikhlas ta fito daga cikin kitchen din hannunta rike da food flask, wucesu tayi ta shige, binta da kallo lamido yayi aranshi yana yaba irin shigar da tayi domin wata bakar atamfa tasaka mai ratsin yellow ajiki dinkin doguwar rigane ta sama ya tsuke ta kasa kuma ya baje dan haka ba karamin kyau tayi ba gashi dai ba wani kwalliya tayiwa fuskarta ba amma duk da hakan tayi masa kyau,daurewa yayi ya yakice tunaninta daga ruhinshi yaci gaba da hira dasu fadila har 10 tayi sai lokacin suka yi sallama kowa ya tashi ya tafi dakinshi.
Bedroom dinshi ya shiga yayi wanka ya yi kwanciyarshi ya dauki waya ya kira Xahar, ita kanta Xahar sai da abin ya bata mamaki domin lamido bai fiya kiranta ba sai dai ita ta kirashi,
"Ranka ya dade.." Ta fadi cikin yanga,
"Yakike?" Ya tambayeta bayan ya lumshe idonshi yana hakanto kyakkyawar surarta domin itama ta hadu babu karya amma da bai gane hakan ba har sai yanzu da yafara kulata kulawa kuma wacce zata kaishi har ga aurenta, hira suka ci gaba dayi da ita sosai har 11, kashe wayar yayi bayan sunyi sallama ya juya kanshi yana kallon sama ya fara tunani kuma,yasan abinda yayiwa ikhlas abune mai ciwo amma kuma tunda har ya fito fili ya bata hakuri ai ya kamata tayi hakurin ta yafe mishi su rungumi dansu su rikeshi su zauna lafiya amma maimakon haka ma sai gaba da fushi da ta dauka dashi wanda ko kadan bai bata masa rai ba kamar yanda tabar sadiq ya fadi yaji ciwo, wannan abu yayi mutukar kular dashi shiyasa ma shima yanzu ya dauki aniyar nuna mata kuskurenta.
Ikhlas na kwance a daki bayan tayi shirin bacci, shiru shiru taji lamido bai shigoba saboda taga kwana biyun nan da suka samu sabani a falonta yake kwana domin yasan bazata bari ya kwana acikin dakinta akan gadonta ba, amma kuma yau ko falon bai zoba,
"Me wannan gayen yake nufi? Nufinshi kenan nice zan bishi dakinshi? Tab lallai ashe zamu shekara ahaka" ta fadi hakan acikin zuciyarta,
Tana nan kwance tanata sake sake acikin zuciyarta har dare yayi sosai bata san ma lokacin da bacci ya kwasheta ba sai da asuba tayi sannan ta farka,
Alwala tayi tai salla ta dauko alqur'aninta ta bude ta karanta abinda ya sawwaka sannan ta tashi ta koma ta kwanta, tunda kuma ta koma bacci ba ita ta tashi ba sai 9 nan dinma kukan sadiq ne ya tasheta, zaune ta tashi ta daukeshi,
Ta saitin window dinta ta jiyo maganar lamido shida fadila da alama duk fita zasuyi,
Wani takaicine ya lullubeta wato ma fita zaiyi amma ko yazo yaga yanda suka kwana suka tashi itada sadiq,
"Hmm yayi kyau" ta fada ahankali tareda tashi da sadiq ajikinta ta nufi bathroom.
Wuni guda gidan shiru tsit babu kowa aciki sai ita kadai hakan yasata shiga cikin damuwa,har sai da yamma tayi sannan ta fara jiyo motsin matan gidan alamun sun dawo,
Bata fita ba har magrib sai da tayi salla sannan ta fita ta nufi kitchen, lamido ta gani cikin kananan kaya riga t shirt fara da boxer baki yana kwance akan doguwar kujera ya dora kanshi akan cinyar ihsan tana wasa da sumar kanshi,
D'auke kanta tayi tai kamar bata gansu ba ta wucewarta cikin kitchen amma kuma zuciyarta jinta tayi tai mata wani irin nauyi ga zafi da ta fara,
Tana shiga cikin kitchen taga fadila tsaye tana soya cheaps, wurin kayanta ta wuce ta kunna wuta ta dora tukunya, tana tsaye tana grating din kayan miya fadila ta kammala aikinta ta wuce ta fita, kamar ikhlas zata fashe da kuka haka taji amma ta daure ta kammala dafa indomie din ta dauka ta fita,
A falon ta sake tarar dasu dukansu suna cin cheaps din da fadila ta hada musu, dauke kanta tayi ta wuce a zuciyarta tana jin ita kadai Lamido ya ware saboda yana son yayi mata rashin mutumci acikin gidanshi,
Tana shiga dakinta ta ajiye food flask din ta zauna sai hawaye sharrrr! Hawaye ne suka ci gaba sauka akan kumatunta har na tsawon wani lokaci. Dakyar ta iya cin abincin tayi salla tayi wanka tayi shirin bacci ta kwanta.
Haka suka ci gaba da zama har na tsawon wani lokaci, duk ranar girkinta lamido bama ya dawowa gidan da wuri domin ranar ne yake zuwa hira wurin xahar, idan kuma ba ranar girkinta bane to bata jin duriyarshi sai dai idan ta fita falo su hadu.
Jin zaman gidan tayi ya isheta domin kullum ita kadaice take wuni agidan sai weekend su fadila da ihsan ke zama, shi kanshi lamidon shima ba zaman yake yi ba domin sunata shirye shiryen kammala service dinsu ga ginin company dinshi wanda baffa ke gina mishi da ake son ayi agama domin fara aiki,
Tana zaune a dakinta tana kallo taji alamun ya dawo dan haka ta mike ta nufi falo, yana zaune shi kadai da laptop agabanshi yana latsawa,yayi tsananin kyau cikin farar riga jersey da dan karamin wandonta iya cinyarshi,
"Abban sadiq wurinka nazo" tace dashi fuskarta babu walwala,
"Ina jinki" yabata amsa ba tareda ya dago ya kalleta ba,
"Maganar makarantar islamiyya dinnan da muka yi dakai, ina son zan fara zuwa"
"Ba yanzu ba" ya mayar mata da amsa idonshi akan laptop dinshi,
"Wanne irin ba yanzu ba? Kullum ni kadai nake wuni agidan nan sauran matanka gasu nan ka barsu suna fita makaranta amma sai ni yanzu dan nace zan shiga islamiyya zakace bazan jeba?" Ta fada cikin bacin rai,
D'an murmushi yayi kadan sannan yace "idan akan fadila da ihsan kike magana to ni banine na nemar musu makaranta ba, asalima a makarantar na gansu har nafara sonsu na auresu, dan haka yanzu bazan hanasu karatunsu ba..."
Juyawa tayi ta tafi ba tare da ta sake magana ba amma kuma maganarshi ta yi mugun kona mata rai mussamman ma kalmar da ya fada wai asalima a makarantar ya gansu har ya fara sonsu, tsaki tayi ta gyara kwanciyarta zuciyarta na yi mata radadi, dama ko bai fadi haka ba ai tasan yana sonsu kuma dan yana sonsu ya auresu har yake zaune dasu.
Lokacin da ikhlas ta tafi lamido kasa samun nutsuwa yayi domin baya son yayi mata abinda zata rinka ganin kamar mijinta na baya yafishi sonta duk da yasan duk abubuwan da suke faruwa laifinta ne domin itace tayi mishi abinda har ya kasa hakuri ya fara fushin shima, rufe laptop dinshi yayi yai shiru, rabonshi da dakinta tun lokacin da ya mayar mata da sadiq washe garin ranar da ya fadi yayi targade yanzu kimanin wurin sati shida kenan.

WhatsApp: 08161892123

No comments:

Post a Comment

Pages