Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Friday, 8 December 2017

RUWAN KASHE GOBARA! 9



_9_

Jikinsa amace ya tashi har lokacin da sauran zazzabin ajikinsa,hawaye ya fara yi yatashi ya nufi part din innah,
Yana shiga ya sameta zaune a falonta tana kallon tv,tana ganinshi ta mike taje ta rungume shi,
"Lamido jikinne? Dadina dakai rangwanta daga rashin lafiya ta kamaka sai ka zauna kayita kuka, kai dai akomai jarumi ne amma banda a bangaren jinya domin komai kankantar rashin lafiya kuka kake yi mata"
Kan doguwar kujera ta kaishi ta kwantar dashi tafara shafa sumar kanshi tana murmushi,
"Baka ci abinci ba, in kawo maka ko?"
Kai ya girgiza alamun a'a,
"Haba Lamido ka daure kaci mana sai kasha magani, kaji lamidon innah"
Juyawa yayi ya gyara kwanciyarsa, hakan ya sanya inna tashi ta shiga kitchen taje ta bararrako masa indomie ta kawo masa, har lokacin yana kwance yana kuka,
"Tashi kaci sarkin kuka"
Tayar dashi zaune inna tayi tafara bashi abaki yana ci har ya dan ci dayawa, panadol ta dauko masa tazo tabashi yasha,
Kwanciya ya sake yi har lokacin salla yayi sannan ya mike yashiga bedroom din inna ya je ya dauro alwala yafita zuwa masallaci,fitowa yayi bayan an idar da salla anan ya hadu da bash yana kokarin shiga gidan,
Packing bash yayi ya fito yana murmushi,
"On top" bash yafada gamida mika masa hannu, mika masa hannun shima Lamido yayi yana dan murmushi,
"Bash ya akayi"
"Normal, ya jikin naka? Kazo mu shiga sch mana"
"Kayi salla ne?"
Lamido ya tambayeshi,
"Muje kawai sai la'asar tayi sai nahada nayi"
Kallonshi Lamido yayi "bash baka tsoron Allah, kayi duk iskancin da zakayi agarin nan amma ya zamana tsakaninka da ubangijinka akwai alaka mai kyau,ni ka ganni nan duk iskancin da kaga ina yi to ina yin salla akan lokacinta sannan bana taba bari da ta wuceni sai dai idan acikin hali na lalura"
"Naji muje ka shirya mu fita"
Wucewa suka yi suka nufi cikin gidan Lamido sai faman yayyamutsa fuska yake yi irinta marassa lafiya,
Wanka Lamido yayi ya fito ya shirya cikin jar t shirt da bakin trouser, rigar ba karamin kamashi tayi ba,
Fita suka yi suka nufi cikin gari bash yana driving Lamido yana zaune agefenshi yana kallon gari ta cikin glass,
"Lamido ya jikinne? Wai kodai...?" Bash ya fada cikeda tsokana,
Yamutsa fuska Lamido yayi sannan ya danyi wani basaraken murmushi, "bash ban taba yin zazzabi irin na jiya ba, kai ni rabon ma da nayi zazzabi har namanta sai wanda nayi jiya"
"Shiyasa nace kodai...?"
"Bash mubi ta wannan hanyar ko Allah zai sa muga wannan yarinyar"
"Angama ranka ya dade, on top"
Murmushi Lamido yayi yaci gaba da rarraba manyan sexy eyes dinshi yana bin ko ina da kallo domin yanzu bashida burin da ya wuce na ya sake haduwa da wannan mahaukaciyar yarinyar.

WhatsApp: 08161892123

No comments:

Post a Comment

Pages