Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Friday, 8 December 2017

RUWAN KASHE GOBARA! 8



_8_

 Ba wata doguwar kwalliya tayi ba, mai kawai ta shafa sai farar powder da ta gogawa fuskarta amma hakan bai hana kyawun fuskarta bayyana ba,

Kayan da ni'ima ta ajiye mata ta dauka ta saka, riga da skirt ne na bakin leshi mai tsananin tsada da kyau, dinkin yayi mata kyau ajikinta domin ya bayyanar da shape dinta afili,

Sallah tayi raka'a biyu kafin ta fita zuwa falon gidan, ni'ima da elmustapha ta gani zaune suna zaman jiran fitowarta domin yin breakfast,

Ido elmustapha ya zuba mata yana kallonta domin ba karamin kyau tayi masa ba, babu wanda zai ganta yayi tsammanin ta taba samun tabin hankali, gata takai duk inda wata kyakkyawar mace takai, tausayinta yaji yana shigarsa saboda tunowa da yayi cewar yanzu ita ba budurwa bace sakamakon fyaden da wani marar tausayin yayi mata amma shi yana da yakinin cewa har yanzu ita bata da masaniyar abinda ya faru da ita,

"Ikhlas kin fito? Karaso nan muci abincin"

Muryar ni'ima ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya lula,

Anutse cikin nutsuwa ikhlas ta karasa ta zauna akusa da ni'ima amma har lokacin shi elmustapha bai bar binta da kallo ba,

Soyayyen dankali da kwai ni'ima ta shirya musu sai ko tea, zubawa ikhlas tayi ta mika mata sannan ta zubawa elmustapha nasa ta ajiye masa agabansa,

Babu wanda yayi magana sai dan lokaci zuwa lokaci da elmustapha yake dan yiwa ni'ima hira, da haka suka kammala cin abincin.

Gyaran murya elmustapha yayi ya juya yana kallon ikhlas sannan ahankali yafara magana,

"Baiwar Allah hakika ki godewa Allah da ya baki lafiya adai dai lokacin da baki sani ba kuma baki tsammata ba, kisani rayuwar da kika yi abaya lokacin da kike hali na rashin lafiya to Allah ya dauke alkaluma akanki amma ahalin yanzu andawo da alkaluman rubutu akanki za arinka rubuta dukkanin ayyukanki na alkairi ko sabanin haka, Allah yasa kaffarace sanadiyyar rashin lafiyarki, sannan idan kin kwana biyu kin nutsu kin huta zan kaiki har gaban iyayenki, yanzu nan kina cikin garin yola ne babban birnin jihar Adamawa amma ina son ki sanar dani ainihin labarinki kafin ki hadu da lalura"

Ko dagowa ikhlas ba tayi ba amma kuma da alama kuka take yi marar sauti Wanda iya hawaye ne kawai yake kwarara daga idanuwanta.


*

  Zazzabine mai mutukar zafi ya sake rufe Lamido nan ya shiga surutai marassa kan gado dama shi yana dadewa baiyi rashin lafiya ba amma duk lokacin da kuma ta kamashi to yana jigatuwa,

Kudundune yake shi kadai adakin nasa sai maganganu yake,

"Washh zazzabin nan Allah yasa iya ni kadai ne bai kama min ke ba, washh jin kaina nake kamar zai tsage, bash dan Allah kaje ka samo min ita..!, washh innah, innah, innah, Baffa wayyo baffah, inna, innah, innah..!"

Haka yayita fada har bacci ya samu nasarar daukeshi sai alokacin bakinsa yayi shiru, ya dan jima yana bacci kafin ya iya farkawa.

No comments:

Post a Comment

Pages