_50_
Wanka yayi ya shirya yaje yayi aski sannan ya wuce gidan baffa, innah Kadai ya samu agidan, zama yayi suka gaisa suka dan taba hira kafin yayi mata sallama ya nufi gidan suhaima, yana zuwa ya samu Xarah ta shirya masa kayan tarba irinsu snacks da dambun kifi ga lemuka kala kala,
Fitowa tayi tasha kwalliya sosai cikin blue din leshi mai kyau,
Zama tayi tana murmushi tana kallonshi yana zaune akan kujera ya karkace ya rausayar da kanshi yana latsa wayarshi, ba karamin kyau taga yayi mata ba hakika lamido shine irin mijin da ta dade tana addu'ar samu domin ya hadu ba karya,
"Sannu da zuwa ranka yadade" tafada ayangance,
"Yawwa Xarah ya gida?, ina mamansu sayyid ko bata nan?" Ya tambayeta yana kallon fuskar wayarshi,
"Tana nan kabari mu gama sai na kira maka ita" tafada idonta narai narai,
"Ai Xahar sauri nake yine shiyasa, ki kirata kawai mu gaisa na wuce"
Tashi xahar tayi badan tasoba taje ta kira suhaima, nan suka shigo da yaranta suna ganin lamido suka je suka makalkaleshi,
Kallon yaran yake yi cikeda tausayawa kusan duk lokacin da yagansu sai ya rinka jin kamar zaiyi kuka,
Gaisawa sukayi da suhaima yayi mata sallama bayan ya kwashi yaran domin yana son ya kaisu supermarket ya iyo musu siyayya,
Ganin zai tafi yasa xahar binshi tana cewa "nima zanyi rakiyar"
Bai bata amsaba ta shiga gaban motarshi ta zauna sukuma yaran suna baya,
Gidan ikhlas ya nufa, acikin mota yabar su xahar itada yaran ya shiga cikin gidan shi kadai,
Lokacin da yashiga gidan ikhlas tana zaune a falo daga ita sai vest baka ta daura zani asama tasaka katon cikinta agaba tana cin shinkafa da wake ga robar yaji da ta gishiri agefe tana dandana tana sakawa acikin shinkafar tana ci, gefe kuma hajiya ce zaune sai faman mita take yi,
"Ban taba ganin yarinya mai taurin kai ba kamar ke wannan yarinyar, kullum sai nayi miki fadan cin wannan gishirin amma kin ki ji ai shikenan"
Sallama yayi ya shiga idonshi akan ikhlas,
Tana jinsa tayi wuf ta fara neman hijabi amma babu kasancewar su biyune agidan daga ita sai hajiya shiyasa take zamanta yanda take so,
"Hajiya dan Allah taimakeni da hijabina" tafada kamar zata saka kuka saboda ta kasa tashi domin cikinta yayi nauyi sosai,
Tsayawa yayi bai karasa shigaba har sai da hajiya ta dauko mata hijabin ta saka ta rufe jikinta sannan ya shiga,
"A lale lale, barka da zuwa Lamido"hajiya tafada tana gyara daurin dan kwalin kanta,
Shiru ikhlas tayi tana suraren gaisawar da hajiya suke yi da Lamido,
Ido Lamido ya zubawa ikhlas nan yaga tayi kiba tayi suntum hatta kafafunta ma kamar an hura balo,
"Hajiya meya sameta? Lafiya kuwa take? Naga tayi kiba sosai" yafada yana dauke idonshi daga kallon ikhlas,
"Hawan jinine, jininta ne yahau sosai gashi likita ya hanata cin gishiri amma taki ji ka ganta nan kullum haka take sakashi agaba tayi ta ci kuma likita yace indai jininta bai sauka ba lokacin haihuwarta yayi to ita da jaririn zasu shiga wani hali",hajiya tafada cikin fada,
Kallon ikhlas yayi duk tabashi tausayi kamar yayi mata kuka,
"Hajiya debo min duk gishirin dake gidan nan"
Har hajiya tafita babu Wanda yacewa wani uffan tsakaninsa da ikhlas, tashi yayi yaje ya dauke na gabanta wanda ta ajiye,
"Dan Allah kabar min" tafada kamar zatayi hawaye,
"Ya za ayi likita ya hanaki abu amma ki dage kan sai kinyi, wato ke baki san illarsa ba ko? To ki bari idan kika haifar min yarona lafiya sai kije kici gaba da cin gishirinki idanma buhu zaki rinka cinyewa asati ni babu ruwana"
Dagowa tayi ta kalleshi tana mai jin mamakin kalaman da suka fito daga bakinsa wato shi bata ita yake ba ta danshi yake yi,
Hajiya ce ta shigo hannunta rike da ledar gishiri yeluwa,
"Ka ganshi duk na debo maka ko cikin cokali ban rageba"
"Hajiya dan Allah da maggi kawai zaku rinka yin girki"
"Ni dama bana son gishirin nan saboda hawan jini"
Mikewa Lamido yayi ya karbi ledar gishirin ya juya zai fita,
"Dan Allah ka kawo min ice cream" ikhlas tace dashi,
Girgiza kai yayi, "babu ice cream din da zan kawo miki domin lafiyar yarona bana son sanyi Ya kamashi"
Yana gama fadin haka ya juya ya fice,
Binshi da kallo ikhlas tayi har ya fice,
"Komai kace yaronka komai kace yaronka sai kace kaine kayi cikin sai kabari ka ajiye naka gudan jinin kafin ka nuna min iko" tafada acikin zuciyarta tareda gyara zamanta bayan ta tankwashe kafafunta dakyar.
No comments:
Post a Comment