Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Wednesday, 27 December 2017

RUWAN KASHE GOBARA! 49



_49_

Kan gadonshi ya fada ya kwanta sai da ya shafe lokuta masu yawa sannan ya tashi ya shiga wanka ya fito yasa kayan bacci ya sake kwanciya,
Tunanin ikhlas ne ya mamaye ruhinsa wanda ya hanashi bacci, ganin ya kasa bacci ya sashi mikewa ya fita zuwa dakin ihsan,
Tana kwance tana sharar baccinta, bayanta yaje ya kwanta ya rungumeta.
Washe gari bai fita daga gida da wuriba kasancewar jiya bai samu bacciba adaren jiya, sai wurin 12 sannan ya fito da niyyar tafiya wurin ikhlas,
Ihsan tana kitchen tana aiki ita kuma fadila tana zaune a falon tana goge zannuwan gadonta,
Fitowa ihsan tayi hannunta rikeda ludayin miya tana kallonsa,
"Darling ina zaka kuma"
"Ihsan zanje na gano ikhlas ne"
"Har yanzu bata warke ba?" Tafada a kufule,
Batare da yabata amsaba yasa kai yafice, takaicine ya kama ihsan da fadila domin itama fadilan ranar girkinta haka yayi mata,
"Ihsan kiyi hakuri nima haka yayi min shekaran jiya, ban san daliliba yanzu gaba daya ya dauki kulawar duniya ya dorawa ikhlas da anyi magana kuma sai kiji yace wai amana aka bashi, ai ba ita kadai bace amana tunda ga anty suhaima nan ita da aka mutuma aka barta da marayu har guda hudu"
Jiyowa ihsan tayi idonta cikeda kwalla,
"Ki barshi fadila mu yanzu ya mayar damu wasu wawaye, idan kuma mutum yayi magana yafika fushi, jiyafa tun safe ya fita daga gidan nan amma bashi ya dawo ba sai dare, nidai wallahi bazan juri irin wannan wulakancin na on top ba"
"To idan bamuyi hakuri ba ya zamuyi ihsan? Kinfi kowa sanin on top idan muka zake da yawa wallahi mamaki zai bamu"
"Fadila idan ke zaki juri wannan cin mutuncin nasa wallahi nidai yanzu bazan jura ba, idan da yayi min najure lokacin bai aureni bane amma yanzu na zama matarsa inada hakkoki akansa ciki kuwa harda zamansa agida"
"Hakane ihsan kiyi hakuri nima nasha irin wannan takaicin shekaran jiya"
Juyawa ihsan tayi takoma cikin kitchen tana share kwallar da ta fara silalowa akan kuncinta.
Lokacin da Lamido ya fita ta kasuwa ya biya ya siyawa ikhlas kayan marmari irinsu lemo da ayaba da Apple, gidan ya shiga atsakar gida ya samu hajiya tana yin wanke wanke,
Gaisawa suka yi ya shiga ciki, afalo ya iske ikhlas din zaune ta gama cin abinci, kallonta ya danyi cikin nata har ya dan fito,
"Sannu da zuwa" tafada tana mai kokarin janyo hijabinta,
Ciki ciki ya amsa suka gaisa ya mika mata ledar da ya shigo da ita ya tambayeta koda abinda take bukata tace babu,
Mikewa yayi ya fita yayiwa hajiya sallama ya tafi, gidan suhaima yaje itama ya gaisheta, Xahar kanwarta sai shisshige masa take duk da bashida ra'ayin kula mace sai da ta makale masa har ya bata phone number dinshi amma ya fada mata yanada wacce zai sake aura nan da yan watanni, cewa tayi taji tagani kuma ta yarda,
Tun daga ranar suka fara soyayya sama sama shida xahar, batun ikhlas kuwa kullum cikin zuwa ganinta yake gashi bata rabuwa da rashin lafiya kullum cikin ciwo take, tausayinta ne yake kama Lamido duk lokacin da yaje ya ganta.
Irin kulawar da yake bawa ikhlas ne yasa yanzu bashida lokacin kowa sai nata hakanne ya sake kular da fadila da ihsan har suka kasa hakuri suka tunkareshi da maganar, kaca kaca yayi musu ya balbalesu da masifa yahau fushi dasu,
Gidan innah sukaje suka kai kararsa wurin baffa, kiransa baffa yayi yai masa nasiha yace ya zauna ya kula da matanshi ita kuma ikhlas idan yaje sau daya arana ma ya isa,
Gidanshi ya koma ya samu ihsan da fadila zaune afalo suna jiran zuwansa,
Zama yayi yana kallonsu,
"Fadila, ihsan kun bani mamaki da bazaku iya tayani rike amanar da dan uwana ya bar min ba, naji abinda kukaje kuka fadawa baffa, ni kuka kai kara ko?? Nagode"
Tashi yayi yabar falon batare da ya jira abinda zasu ceba, tabe baki fadila tayi yayinda ihsan taja dan guntun tsaki.
Kulawa iya kulawa yana bawa ikhlas yanzu cikinta ya girma ya fito sosai domin watanshi bakwai, alokacin Lamido ya tafi jahar yobe domin shiga camp, damuwa iya damuwa ya shiga domin gani yake babu wanda zai kular masa da ikhlas kamar yadda zai kula da ita,
Da damuwar halin da yatafi yabarta ya tafi, ita kuma ikhlas abdallah aka kawo mata hutu shida mahaifiyarta ammi domin suyi mata sati biyu,
Tunda su ammi suka zo kullum tana makale da abdalla suna hira gashi ya girma yadan zama saurayi, satinsu uku shida ammi suka tafi aranar da suka tafi aranar Lamido ya dawo yafito daga camp.

No comments:

Post a Comment

Pages