_39_
"Ikhlas meyasa bazaki aure niba, Kodai ban kasance daga cikin irin mazan da kike so ba?"
Girgiza kai tayi tana murmushi "bahaka bane"
"To yayane?"
"Ban shirya aure bane acikin rayuwata"
"Kamar ya? Bakiji dadi bane agidan mijinki nafarko ko kuma rasuwa yayi ke kuma kike tunanin ko bazaki samu wanda zai iya maye gurbinsa ba?"
Girgiza kai ta sake yi "Sam ni ban taba aure ba ma"
Kallonta yayi da mamaki "to tayaya kikace abdallah kece kika haifeshi,haba dama ina tantama, wallahi ina doubting domin duk wanda ya ganki yasan ke budurwa ce"
"Wallahi nice mahaifiyar abdallah, nice na haifeshi"
"Tayaya?"
"Na haifeshi ba tare da uba ba, ina nufin abdallah bashida uba, dan haka kaga ni ba irin matar da zaka aura bace"
Kallonta yayi har lokacin da mamaki atare dashi,
"Wannan ba shine dalilin da zaisa na fasa aurenki ba, kawai nidai ki sanar dani abinda yafaru dake har kika haifi abdallah nikuma nayi miki alqawarin zan aureki ahaka kuma zan rike ki amana zan rike abdalla kamar dan dana haifa acikina"
Zamanta ta gyara ta tankwashe kafafunta ta fuskanceshi ta fara magana,
"Ikhlas Ahmad Buzu shine asalin sunana, mahaifina dan kasar Nijar ne cikin babban birnin niyami, shi kadai iyayensa suka haifa,
Lokacin da ya zama saurayi sai ya shigo kasar Nigeria domin neman ilmi da kasuwanci, acikin garin Zaria ya zauna a hannun wani malami inda yake koyon karatun allo, to malamin nashi yana zuwa Maiduguri ta jihar Borno yawon fatauci, duk shekara tare suke zuwa da babana,
Akwana atashi har babana ya zama dan gari yana zuwa Maiduguri da kansa ya koma Zaria yawon kasuwanci, tsakaninsa da kasarsu ta nijar kuwa sai dai yaje ya gaida mahaifiyarsa ya kai mata abinda ya samu,
Lokacin da babana yafara samun budi sai yafara neman aure amma kuma ba abashi ba hakan yasashi barin Zaria ya koma Maiduguri acan ya hadu da mahaifiyata suka fara soyayya, itama mahaifinta babban malamine, ganin babana almajirin ilmine yasa mahaifinta bashi ita aka daura musu aure suka koma Zaria,
Tunda suka yi aure sai mahaifina yafara samun budi, babu dadewa ya zama hamshakin dan kasuwa wanda yayi suna a nahiyar kasar nan,
Nijar ya koma ya dauko mahaifiyarsa ya dawo da ita nan gidansa sai dai kwata kwata yakumbo mahaifiyarsa bata son mahaifiyata ta tsaneta,
Haka suke zaune tana gallaza mata, kullum maganarta bata wuce abbana ya kara aure ko yasamu magaji tunda ita ammi bata haihu ba, amma abbana baya cewa komai sai dai yace akwai sauran lokaci tunda har yanzu basuyi shekara goma da aure ba,
Ana cikin haka ammi ta samu juna biyu tunda yakumbo ta fahimta sai hankalinta ya tashi nan ta shiga makirci iri iri dan ganin ta raba ammi da cikin nan amma hakan bai samu ba, lokacin haihuwa nayi ammi ta haifo yaranta yan biyu maza murna wurin mahaifina ba acewa komai dan ba karamin dukiya ya salwantar ba awurin sha'anin bikin suna,
Ba adade da suna ba ya kwashesu zuwa kasa mai tsarki suda jariran domin gudanar da umarah, iya yakumbo kawai aka Bari agidan, hakan ya sata shiga damuwa dan haka kafin su dawo sai tatafi nijar ta dauko yar kanwarta Nafi ta kawo ta gidan koda su abba suka dawo sai ta shiga matsa masa akan lallai sai ya auri Nafi,
Dafarko ya bujire amma da ta shiga yin magani da asiri sai ya yarda aka daura auren dama bazawara ce aurenta hudu, tunda akayi auren abubuwa suka sauya,
Ammi zaman hakuri kawai take agidan domin yakumbo da Nafi sun tsaneta sun tsani yayanta, lokacin data yaye su hussain alokacin ta samu cikina ai nan jaraba ta tashi agidan saboda ita Nafi har yanzu bata samu juna biyu ba dama bata taba haihuwa ba,
Asiri babu wanda basayi har takai da abba yafara tsanar yayansa yan biyu wadanda da babu wanda yake so kamarsu, ko kusa dashi sukaje sai fada da duka da hantara gamida kwazazzaba, nan ammi ta shiga damuwa domin itama yanzu baya sassauta mata amma tasan ba yin kansa bane aikin asirine,
Cikin wannan halin ammi ta samu ta haifeni bayan tasha mutukar wuya domin ranar abba baya nan dan haka yakumbo da Nafi suka ki koda taimaka mata ne suna jinta tana kwalla musu kira babu wanda ya amsa tun safe take daki tana nakuda har dare sai sha dayan dare ta haihu alokacin ta tura hussain yaje ya kirawo mata makociyarta talatu wacce itace tazo tayi mata komai ta gyara jaririyar, duk da mahaifina yana cikin hali irin na asiri hakan bai hanashi murna da samun haihuwata ba.
No comments:
Post a Comment