Tana jinsu shida abdallah sai rangada hirarsu suke kamar dama sun san juna, itace ke yimasa kwatance har suka je gidan,
Fitowa tayi tana jiran fitowar abdallah, tare da mutumin suka fito yana mikawa abdallah turarukan da ya sai masa guda uku,
"Antyn boy baki fada min sunanki ba"
"Kaima ai baka fada min sunanka ba"
"Sunana Abubakar Sadeeq"
"Sunana ikhlas"
Murmushi yayi "ashe mai ikhlasi ce matar tawa"
Murmushin itama tayi "nifa matar wanice kaga yarona nan"
"Nima mijin watane inada yara hudu uku maza daya mace"
Murmushi ta sake yi "ka dauka wasa nake ko? Baka san dagaske nice na haifeshi ba?"
"Gaskiya ban yarda dake ba"
"Shikenan tunda baka yarda ba nagode madallah da hidimar da kayiwa abdallah"
"Babu damuwa sai gani na biyu" yafada yana yiwa abdallah bye bye, ciki suka shiga suna zuwa abdallah ya Shiga gwada kayan yana murna sai bawa ammi labari yake cewar uncle dinsa ne ya siya masa.
Acikin satin su ikhlas suka sha hidimar bikin hassan da hussain wanda zasu zauna acikin unguwar domin tsakanin gidajensu da gidansu ammi ma gida dayane atsakani.
Tunda aka kammala bikin ikhlas take ramuwar baccin da bata samu tayi ba ga gajiyar biki data kwasa,
Tana falon ammi tana gogewa abdallah kayan sawarshi wurin sha biyun rana, ahankali ya lallabo yazo ya dale bayanta ya rungumeta, ammi na kwance tana kallonsu,
"Bawan Allah bari mana kar ka karya min bayana" ikhlas tace dashi tana gyarashi a bayanta,
"Uhm uhm anty ni bacci nake ji kizo muje muyi bacci"
"Abdallah baka ga aiki nake yiba haba bawan Allah"
Kwanciya yayi abayanta taci gaba da gugar ko minti biyu ba ayiba taji alamun yafara bacci, kashe iron din tayi ta mike dashi abayanta,
"Bawan Allah ka hanani gugar nan dai"
Dariya ammi tayi "kukam ai kunji jiki kamar jika da kaka idan kukai wani abun"
Batace komai ba tawuce dashi cikin daki taje suka kwanta, rungumeshi tayi har bacci ya dauketa, bata san lokacin da abdallah yatashi yafice ba.
Tana tsaka da bacci tajiyo maganar abdallah yana tashinta,
"Anty kitashi uncle din rannan yazo"
"Bari abdallah bacci nakeyi"
"Anty uncle din rannan ne yazo, kitashi"
Irin yanda yake jijjigata yasata ta tashi dole,
"Yanzu bawan Allah kullum bazaka barni nayi bacci ba daga nafara sai ka tashe ni?"
"Anty uncle ne yazo"
Tashi tayi taje ta dauko bakin hijabinta tasa ta kama hannunshi suka fita ammi bata falon da alama tana sashen hajiya,
A kofar gida ta sameshi atsaye yasha kwalliya cikin brown din yadi,
Tun daga nesa yake kallonta har ta karaso da sallama a bakinta,
"Nazo nemanki tun dazu ban ganki ba sai karamin kaninki naga" yanuna abdallah,
Kallonsa tayi "abdallah fa ba Kanina bane wallahi dana ne"
Cikin mamaki ya kalleta "wai kina nufin ke kika haifeshi?"
"Wallahi nice na haifeshi"
Binta yayi da kallo domin babu wanda zaiyi tunanin tayi aure balle har ace ta haifi yaro,
"Kenan kin taba aure?"
Shiru tayi bata amsa masa ba, dan haka yaci gaba,
"Uhm ikhlas wallahi nidai naganki ina sonki kuma zan aureki"
"Nagode da soyayyarka amma kacire maganar aure dan bazan aureka ba?"
"Ko menene dalili?"
"Wannan nabarwa kaina ni daya"
"Bazai yiyuba, dole akwai dalili kuma yana da kyau ki sanar min"
"Gaskiya bazan sanar dakai ba amma kayi hakuri bazan iya aurenka ba"
Hannun abdallah ta kama suka shige cikin gida tana jinsa yana kiranta amma bata waiwayoshi ba, gajiya yayi da tsaiwa ya tafi.
Kwana biyu da faruwar wannan sai gashi ya dawo wannan karon har cikin gida ya shiga har falon ammi,lokacin da ikhlas tafito taganshi tayi mutukar mamaki,
Tareda ammi tasamesu yana yi mata bayanin cewa yana son ikhlas kuma aurenta zaiyi, ammi kam cewa tayi yaje su daidaita Allah ya zabi abinda yafi alheri,
Hannun abdallah ya kama yace zasuje children's park and zoo domin yayi kallo,
Ammi bata hanasu ba amma tace itama ikhlas ta shirya sutafi tare ba abar yaro shi kadai ba,
Shiryawa ikhlas tayi ta danyi kwalliya tasa bakin material da farin mayafi suka fita.
Wuri suka samu Abubakar sadeeq ya shimfida musu darduma suka zauna bayan yayi musu oder din kayan sanyaya makoshi, shi kuwa abdallah yadade da bazama wurin da ya hango yara na wasa cikin nishadi da annashuwa.
No comments:
Post a Comment