_36_
Bai kula dasu ba, agaba ya tsaya sukuma suna bayanshi yajasu salla, raka'a biyu sukayi yai sallama, addu'o'i yayi musu afili da waje sannan ya jiyo yana kallonsu,
"Fadila, ihsan dan Allah na rokeku ku zauna lafiya banda tashin hankali sannan dukkaninku matana ne babu wacce tafi wata awurina, dan Allah banda fada domin bashida amfani"
Babu wacce tayi magana acikinsu dan haka yaci gaba,
"Fadila kece babba saboda kece uwar gida dan haka ki rike girmanki, ke kuma ihsan banda rashin kunya kibata girmanta, zaku rinka yin girki kwana bibbiyu, amma tare zaku rinka yi saboda bana son abinda zai rarraba kawunanku"
"Da dai kowa yayi girkinsa yafi" suka fada bakinsu har yana haduwa,
"To hakan ma babu matsala kowa ya rinka yin nashi girkin daban,yanzu dai zanyi kwana bakwai awurin fadila kafin sai nadawo dakinki ihsan kema nayi miki kwana bakwai daga nan kuma sai kufara kwana bibbiyu,akwai mai magana acikinku?"
Girgiza kai sukayi alamun babu, tashi yai yaje inda fridge yake girke ya dauko manya manyan robobin fresh milk guda uku ya kawo musu yasake komawa saman fridge din ya dauko wata leda mai kyalkyali,
Kajine duku duku guda uku aciki, anan ya baje musu suka dan tattaba domin daga shi har su babu wanda yayi wani cin kirki,
Bayan sun kammala ne suka tashi domin kowa yatafi dakinsa, tare suka jera suka fara raka ihsan dakinta sannan ya kamo hannun fadila suka wuce dakinta,
Rigar jikinshi kawai ya cire ya kwanta daga shi sai farin dogon wandon yadin dake jikinsa da farar vest, ita kam fadila wanka ta shiga ta sillo ta fito daure da towel da wani ta lullube kanta da jikinta, sai da ta zauna ta kyalkyale jikinta sannan ta dauko rigar baccinta ja tasaka taje kusa dashi ta kwanta.
Haka zamansu ya kasance har yagama yiwa fadila kwana bakwai dinta ya koma dakin ihsan nanma yayi kwana bakwai daga nan kuma suka fara rabon kwana,inda yake yiwa kowacce kwana bibbiyu.
Kasancewar hutunshi yana da dan yawa yasa zai dan jima akasar, kullum fadila da ihsan na zuwa sch kowacce a motarta take zuwa domin babu wacce ba akawota da mota daga gidansu ba,
Shikam lamido kullum ahanyar zuwa bakin kasuwa yake harma wurin ya zama wurin zuwansa domin kullum sai yaje,
Hankalinsa yanzu yadan kwanta sakamakon aurennan da yayi kuma yana kokarin bawa kowacce kulawa haka suma suna kula dashi domin dukkaninsu suna tsananin sonshi sai dai babu jituwa atsakaninsu kowacce ta tsani yar uwarta kamar zasuga hanjin cikin juna suke gashi dole sai sun hadu domin kitchen dinsu ma ahade yake guda daya ne for general.
Yanzu kam lamido ya daina shan kodin kuma ya daina neman mata domin tunda yayi aure yaji matan banza sun fita daga ransa kwata kwata, yar kulawar da yake samu tasashi yayi kalau dashi yasake yin kyau sosai amma babu wanda zai ganshi yace yanada mata biyu,
Watansu biyar da aure ya shirya komawa Kenya nan kuma baffanshi yace dole sai yatafi da daya daga cikin matansa, amma koda ya tuntubesu sai fadila tace da ita zai tafi ta yarda zata ajiye karatunta idan sun dawo sai taci gaba tunda yanzu saura shekara daya da rabi ta gama, shirye shiryen tafiya suka fara amma fa har lokacin lamido bai manta da mahaukaciyar nan ba tana nan acikin zuciyarshi kullum da ita yake kwana yake tashi.
Ranar alhamis da yamma jirginsu ya daga shida fadila suka bar Nigeria, tunda sukaje Kenya kuma suke fada da fadila saboda bata son motsa jikinta tafi son ayi mata komai tana daga kwance,
Wannan dalilinne yasa kullum basa zama lafiya da lamido domin shi mutumne mai kyankyami da tsantseni, kullum tana kwance tana bacci zai shirya ya tafi lectures yanda yatafi yabarta wani lokacin haka zai sake dawowa ya isketa ko wanka bata tashi tayi ba bare ta gyara musu dakin,
Ganin tasaba da kwanciya yasashi kullum sai yayi abubuwanshi sannan yake tafiya amma ba karamin dana sanin zuwa da ita yayiba domin da yasan haka zata yi masa to babu dalilin da zaisa ya taho da ita.
No comments:
Post a Comment