Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Friday, 15 December 2017

RUWAN KASHE GOBARA! 35



_35_

Cikin gidan ya tasamma kai tsaye ya shiga babban falon tanan yabi ya shiga bangaren Lamido, yana zuwa yafara nocking,
Lamido dake kwance yana kuka yajiyo anfara bugun kofar dakinshi duk azotanshi daya daga cikin amaren ne dan haka ya share yaci gaba da kukan da yake,ankai kusan minti biyar ana bugun kofar amma yaki tashi kamar amafarki yajiyo muryar baffanshi yana kiransa,
"Lamido, Lamido, Lamido"
Tashi yayi arazane yakarasa bakin kofar ya tsaya dan ya tabbatar ai kuwa shi dinne, cikin hanzari yakama rigarsa ya goge fuskarsa ya bude kofar,
Baffa yagani tsaye yana kallonsa, hamnunshi baffa yakama suka koma cikin dakin,
Abakin gado suka zauna baffa ya zuba masa ido cikin tausayawa domin ya fahimci kuka yake yi kai duk yanda akayi akwai yarinyar da Lamido yake mutukar so sai yanzu ya gane wannan amaren da ya aura masa basune zabinsa ba basune burinsa ba kawai yayi masa biyayya ne,
"Lamido ya zaka zo ka zauna adaki bayan an rigada an kawo maka amarenka suna can suna jiranka" baffa yafada gamida kamo hannunsa,
"Baffa kainane yake ciwo"
"A'a lamido kafada min gaskiya, daga ganin fuskarka kuka kakeyi, ko kanada wacce kake so ne??
Shiru yayi babu amsa,.
"Nace akwai wacce kake so?"
Sai alokacin ya daga kai alamar ehh,
"To ai lamido duk wannan mai saukine, shiyasa ubangiji ya Baka damar ka auri mata har guda hudu, yanzu ga biyu zabina wanda na aura maka, nan gaba kaima Kanada damar da zaka auro guda biyu wadanda suka kasance zabinka, bazan hanaka ba lamido, duk lokacin da ka shirya ka Aurota ka kawota gidan ka"
Sai alokacin lamido yaji sanyi aranshi,
"To baffa nagode"
"Yawwa yanzu katashi kaje wurin iyalanka"
"To baffa"
"Yawwa Lamido kayi hakuri kar ka sake zubar da hawayenka kaji, idan matanka suka ganka kana kuka zasu ce ragon maza suka aura"baffa yafada cikin barkwanci,murmushi lamido yayi yana shafa sajenshi batare da yace komai ba,
Mikewa baffa yayi lamido yabi bayanshi ya rakashi har inda motarsa take ya shiga ya tafi, ciki lamido ya dawo ya dauki hularshi yasa ya nufi sashen fadila.
Ahankali Ya shiga cikin falon nata duk jikinsa babu kwari kamar anyi masa duka, falon yasha kayan alatu masu aji da matsayi, tsada da kuma haduwa, komai purple aka zuba tun daga kan kujeru har labulaye kai da duk sauran kayan ciki komai kalarsa purple,
Dakinta ya bude ahankali ya shiga, can tsakiyar gadonta ya hangota tana takure da alama kuka take yi,
Sallama yayi ahankali ya karasa kusa da ita bayan ya hau kan gadon,
Mayafin datake lullube dashi ya janye ya kamo habarta ya dago fuskarta, sanye take cikin jan lace mai tsada sai kyalli yake yi yasha stones ajiki,
"Am sorry my fadila..!" Yafada cikin sigar lallashi, bude idonta tayi ta kalleshi ba karamin kyau da haduwa yayiba acikin wannan daren, sai dai amma idonsa yayi ja,
"Lamido ya naga idonka yayi ja?" Ta tambayeshi a gigice,
"Ciwon ido nake yi ai fadila, banida lafiya"
"Ayya sorry my lamido" tafada kamar zata saka kuka,yan yatsunta ya kama yana kallon fuskarta,
"Kije kiyi alwala ki fito, ki sameni a babban falo nida ihsan"
"Tom" ta amsa ciki ciki sakamakon ambatar ihsan da taji yayi, mikewa yayi ya fita ya nufi part din ihsan wacce itama yasan tana can tana baza idanuwan ganinshi.
Falon ihsan ya shiga ita kuma komai nata coffee colour ne da ratsin milk ajiki, bedroom dinta ya kama ya shiga tana zaune agefen gado ta kifa kanta ajikin pillow,
Abayanta ya zauna ya rungumeta ta baya yana cewa "my ihsan badai har kinyi bacci ba?"
"Lamido ina ka shiga?" Ta tambayeshi tana shasshekar kuka,
"Kiyi hakuri ihsan akwai abinda ya tsayar dani kinji"
"Meya tsayar dakai awannan daren bayan kasan muna nan muna jiranka" tafada cikin kuka, hannunshi ya mika ya fara share mata hawayen fuskarta, cikin sigar lallashi yafara magana,
"Kiyi hakuri my ihsan,pls daina kukan ki tashi kiyi alwala muje muyi salla"
Sakinta yayi ta tashi ta shiga toilet dinta binta da kallo yayi tasha atamfa super yar gasken green colour,hakika yasan daga fadila har ihsan duk suna sonsa to amma shi matsalar shima yana da wacce yake so sai dai kawai yasha alwashin zai zauna dasu domin yiwa mahaifinshi biyayya,
Yana nan zaune ta fito ta dauki gyalenta, hannunta ya kama suka fita zuwa babban falon gidan inda fadila ke tsaye tana jiran fitowarsu.

No comments:

Post a Comment

Pages