_12_
Cikin hanzari elmustapha yabude motarsa ya dauko ledar magungunan da likita ya hadowa ikhlas,
Afalo ya samu ni'ima tsaye tana rike da kugunta tana jiran shigowarshi, wuceta yayi ya nufi dakinta inda ikhlas take kwance yana fadin,
"Ni'ima zo muje mu kai mata maganin"
Batare da tayi magana ba tabi bayanshi cikeda kunar rai,
Agaban ikhlas ya dunkusa yana mata magana ahankali,
"Ikhlas tashi kisha maganin, meya sameki? Zazzabin ne?"
Daga kai ikhlas tayi sannan tafara kokarin tashi zaune ahankali tana ciccije llips dinta,
"Ni'ima kawo mata ruwa"
Juyawa ni'ima tayi tafita tana zancen zuci "kalli duk yanda yabi ya wani rikice sai kace wata yar uwarsa, tab impossible wlh, yarinya bazata zo har gidana ta dauke min hankalin mijina ina zaune ina kallonta ba"
Ruwan ta mika masa acikin roba, karba yayi ya mikawa ikhlas,
"Amshi kisha maganin"
Dakyar ta daure tasha tana ta faman yatsina fuska, komawa tayi ta kwanta bayan ta gama shan maganin, hakan ya sashi tashi yaja hannun ni'ima suka fita zuwa falo.
Akan kujera three sitter ya zaunar dasu yana kallon fuskar ni'ima wacce sai faman cika take tana batsewa,
"Meya faru ni'ima?" Ya tambayeta yana juyo da fuskarta gareshi,
"Magana ta gaskiya barrister gaskiya damuwarka akan yarinyar nan yayi yawa, ina son ka sanar dani menene matsayinta acikin zuciyarka?"
Murmushi yayi yaci gaba da kallonta "ni'ima ace muyita repetition magana daya? Wlhi ban dauko yarinyar nan da wata manufa ba face ta taimakonta, idanma akwai wani tunani acikin ranki to ki cireshi, kin san dai ni lawyer ne inada damar na taimaki mutane tako wacce irin hanya, so stop blaming me, there is nothing inside my heart..!"
Sai alokacin taji ta sake samun nutsuwa amma duk da haka tana dan kokwanto akanshi,
"Pls ni'ima stop doubting, trust me"
"Shikenan yawuce amma dai zaka mayar da ita ga danginta ko?"
"Insha Allahu, nima wannan shine burina naga na hadata da danginta tafita daga hannuna"
"To Allah yasaka da alkairi". Tafada tana kashe murya,
"Amin ni'ima ta"
Murmushi tayi ta narke ajikinsa tana murna.
Misalin kusan awa daya ikhlas ta dauka da zazzabi ajikinta mai mutukar zafi da kashe jiki, bacci ta dan samu tayi marar dadi wanda sam bataji dadinsa ba kasancewar tana cikin hali na rashin lafiya,
Misalin karfe 1 narana ta tashi daga barcin, toilet tashiga tayi alwala tafito tazo tayi salla,addu'a ta zauna yi tana yi tana kuka wanda ni ummi Shatu ban san dalilin kukan nata ba,
Ta jima tana addu'a kafin ta tashi tafita zuwa falo, elmustapha kadai tasamu afalon yana karanta jaridar daily trust, ita kuma ni'ima tana kitchen tana girka musu abincin rana,
Ganin ikhlas ta sanyashi ajiye jaridar dake hannunshi ya dan kalleta kadan aransa yana yaba irin kyawun halittarta domin agaskiyar magana kyakkyawa ce sosai irinsune matan da ake kirada first class,
"Ya jikin naki?" Ya tambayeta yana mai kallon jaridar hannunshi,
"Ah jiki yayi sauki alhamdulillah" tabashi amsa cikin sanyin maganarta,
"Allah yasa kaffara ne"
Ahankali ta amsa da "amin"
Shiru ne ya gifta a tsakaninsu babu wanda ya sake magana sai dai shi elmustapha acikin zuciyarshi yana son sanar da ita wata magana to amma bai san tayaya zai sanar da ita ba domin sanar mata da maganar zai iya haifar mata da tashin hankali gamida bakin ciki acikin rayuwarta.
Ajiyar zuciya mai nauyi ya ajiye sannan ya dan sake kallonta,
"Ina fata dai babu abinda yake damunki domin likita yace idan da damuwa to lallai lallai akoma wurinshi"
Dan murmushin yake tayi tace "babu komai wlhi, kalau nake jina"
"Ato Abu yayi kyau gaskiya, good"
Bata sake magana ba ta sunkuyar da kanta kasa,
"Um ikhlas ina so ki dauki duk abinda ya sameki amatsayin jarrabawa daga Allah, ki dauki duk abunda yafaru agareki a matsayin wani mataki nasamun kyakkyawan rabo acikin rayuwarki, nasan baki da masaniyar abinda ya sameki alokacin da kike hali na lalura, ba ason raina zan sanar miki ba face dan ya zame min dole, tilas kuma wajibi,
Ina ganin babu amfanin nabarki acikin duhu kici gaba da tafiya batare da na haska miki wata fitila wacce zata sanar dake halin da kike ba,
Maganar nan da zan sanar dake ahalin yanzu wallahi ko matata ni'ima ban sanarwa ba saboda sirrinkine, sirrin rayuwarki ne idan nafadawa wani tamkar naci amana ne,
Ikhlas ina son ki dauki kaddara, kisani alokacin da baki da lafiya ansamu wani marar tausayi marar imani yayi miki fyade, wannan shine abinda likita ya sanar dani bayan na mika ki asibiti, amma ki godewa Allah domin dr ya aunaki ya gwadaki bakya dauke da kowacce irin cuta,
Ina son ki dauki wannan abu a matsayin sirri dan Allah kiyi hakuri"
Tunda yafara maganar kanta yana kasa amma jin ya ambaci cewar anyi mata fyade ya sanyata dago kanta da sauri cikin razani tana dubanshi,
"Haba ashe shiyasa nake tajin radadi da zugi akasana ashe abinda yafaru dani kenan" tafadi acikin ranta, mikewa tayi zuruf tatashi tsaye kwalla fal idanuwanta.
WhatsApp: 08161892123
No comments:
Post a Comment