_11_
Kafin wani lokaci tuni har zazzabi ya sake rufeshi, nan da nan ya fara karkarwar sanyi kamar wanda yake cikin kankara,
"Lamido Kodai asibiti za muje?" Bash ya tambayeshi lokacin da yake bawa motar wuta,
"No basai munje ba bash kawai ka mikani gida kayi dropping dina" duk cikin karkarwar sanyi Lamido yake yin wannan maganar,
"Shiyasa nace muje asibiti, yanzu dubi yanda kake yin rawar dari"
Lamido bai sake magana ba suka tasamma barin cikin makarantar, idanuwanshi jajur jikinsa zafi rum haka bash ya kaishi gida ya ajiye shi, dakin innarshi ya nufa yana kankame da jikinshi yana karkarwa, bai sameta acikin dakin ba saboda da alama tana cikin kitchen tana girki kasancewar lokacin dora girkin dare yayi.
Kan bed dinta ya hau ya kwanta yaja bargonta ya lullube jikinsa, hawaye yafara yi domin zafin zazzabin da yake addabarshi,
"Washh, wayyo jikina, washh...!" Yafada yana hawaye, kamar wani karamin yaro haka yaci gaba da kuka har bacci ya daukeshi.
*
Kuka ikhlas taci gaba dayi tun tana marar sauti har tafara yin mai sauti, ni'ima ce ta matsa kusa da ita tafara rarrashinta tana bata baki,
Har tsawon lokaci ikhlas ba tayi shiru ba hakan ya sanya elmustapha yin magana ahankali,
"Idan maganar da nayi aciki akwai wacce ta bata miki rai to ina mai baki hakuri da kiyi hakuri hakan bazata sake faruwa ba"
Girgiza kai tayi cikin kuka tace "ni ba maganarka ce tasani kuka ba"
"To koma dai menene kiyi shiru ki daina wannan kukan haka" ni'ima tace da ita tana shafa kanta,tashi tayi daga falon ta nufi dakin ni'ima tana zuwa ta tukunkune akan carpet din dake malale acikin dakin tuni zazzabi mai zafin gaske ya rufeta,hijabin dake jikinta taja ta lullube jikinta dashi,
Ni'ima ce ta bita cikin dakin tana zuwa ta isketa cikin wannan hali, falo ta koma wurin elmustapha,
"Barrister yarinyar nan fa bata da lafiya"
Dagowa yayi da Sauri "meya sameta?" Ya tambayeta yana kallonta,
"Naji dai jikinta da zafi ina jin zazzabi ne"
Mikewa elmustapha yayi ya nufi hanyar fita yana cewa "akwai maganinta acikin mota mantawa nayi, dama dr yace da zarar mun dawo gida abata tasha, bari naje na dauko mata"
Binshi da ido ni'ima tayi acikin ranta tana tunanin tayaya ma zata bar ikhlas ta zauna mata agida, yazama dole elmustapha ya dauketa ya mayar da ita ga danginta idan kuma bata da dangi to ko hannun hukuma ne sai ya mayar da ita domin zaman ikhlas agidan tana da masaniyar cewar bazai haifar mata da d'a mai ido ba.
WhatsApp: 08161892123
No comments:
Post a Comment