Monday, 27 August 2018
ZARGIN NEMAN MAZA: ’Yan Sanda Sun Damke Matasa Maza 57 A Cikin Wani Otel
’Yan sanda a Jihar Lagos sun damke wasu maza 57 a cikin wani otel da ake zargin su da dabi’ar luwadi.
An kama su ne a cikin Kelly Ann Hotel, da ke cikin Unguwar Egbeda cikin Lagos a safiyar ranar Lahadi.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ne, Imohimi Edgal ya bayyana wa manema labarai haka a wani taron da ya shirya musu, yau Litinin, inda ya ce DPO na Shasha da Idimu ne ya jagoranci kamo su bayan da ya samu tabbataccen labarin cewa ga abin da ake tafkawa a cikin otal din kimanin karfe 2 na dare.
“Yayin da suka wurin, sai suka taras da matasa kimanin 80 a cikin dakin taron, sun bugu sun niske, sannan kuma sun a shan wasu kwayoyin da aka haramta ciki har da irin su Tramadol da Shisha har ma da tabar wiwi.” Inji Edgal.
“Ko da suka ga tawagar ‘yan sanda, sai suka nemi arcewa, amma ‘yan sanda sun yi kokarin damke 57 daga cikin matasan, kuma duk maza.”
Sai dai kuma daya daga cikin wadanda aka kama a wurin, mai suna Wealth Olasunkanmi, dan shekaru 25, da ya kammala digirin sa a fannin yada labarai, ya ce shi ya je wurin ne domin halartar bikin ranar haihuwar wani kawai.
“Ba wani abu muke yi ba, biki ne na murnar zagayowar ranar haihuwar abokin mu Muyiwa, kuma ba matasa maza kadai ba ne a wurin bikin, har da ‘yan mata da yawa. Sannan kuma yawancinmu ma ba mu san junan mu ba.”
“Sannan kuma sun zarge mu da cewa wai mu manema maza ne, to ni dai ba shi ba ne. Sun kuma zarge mu wai ana yi mana tsimin shiga kungiyar asiri. To mu dai babu wani wanda aka tsima don ya shiga kungiyar asiri a wurin, domin mu dai ba ‘yan kungiyar asiri ba ne, kuma ba a same mu da kayan tsima wanda za a shigar kungiyar asiri ba.”
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
Author Details
Ut wisi enim ad minim veniam, quis nostrud exerci tation ullamcorper suscipit lobortis nisl ut aliquip ex ea commodo consequat. Duis autem vel eum iriure dolor in hendrerit in vulputate velit esse molestie consequat.
No comments:
Post a Comment