Yan Bindiga Sun Kashe `Yan Canjin Kudi Hudu A Fatakwal
Yan bindiga sun kashe ‘yan canjin kudi hudu a Fatakwal
Rahoton BBC Hausa
‘Yan sandan jihar Rivers na gudanar da bincike dangane da kisan gillar da ake zargin an yi ma wasu masu hada-hadar musayar kudaden waje a Fatakwal, babban birnin jihar.
Ana zargin wannan al’amarin wani cune ne, domin kisan ya biyo bayan wata takaddamar rufe wata kasuwa ne tsakanin mamatan, da wasu jam’ian gwamnatin Ribas, domin maharan ba su dauki komai ba bayan kisan da suka kaddamar.
Sai dai jami’an ma’aikatar muhallin da ake zargi ba su kai ga cewa komai ba tukunna, inda BBC ta yi kokarin tuntubarsu amma hakan bai samu ba.
Amma rundunar ‘yan sandan ta ce bincike ne kawai zai fayyace ainihin abin da ya auku.
Wadanda aka kashen sun hada da Yusuf Zaki da Muhammad Rabi’u da Ahmad A. Tukur da Abubakar Tugga.
An dai kashe mutanen ne gidansu da ke layin Orazu na karamar hukumar Obiako da ke Fatakwal, babban birnin jihar Rivers.
Tuni dai aka yi jana’izar mutanen a kauyensu da ke Jugudu a karamar hukumar Giade ta jihar Bauchi, da ke arewa maso gabashin kasar.
Adamu Usman, daya daga cikin mutanen da aka kai wa harin, wanda kuma ya tsallake rijiya baya, ya yi karin bayani, game da lamarin ya auku a daren Laraba:
Yusuf Zaki, wanda dan takarar dan majalisar jiha ne karkashin jam’iyyar APC, ya bar mata biyu da ‘ya’ya takwas,
Shi kuma Muhammad Rabi’u ya mutu ya bar matarsa daya da ‘ya’ya hudu.
Adamu A. Tukur da Abubakar Tugga kuwa kowannensu ya bar mata daya amma babu ‘ya’ya.
Amma rundunar ‘yan sandan ta ce bincike ne kawai zai fayyace ainihin abin da ya auku.
Adamu A. Tukur da Abubakar Tugga kuwa kowannensu ya bar mata daya amma babu ‘ya’ya.
No comments:
Post a Comment