Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Monday, 13 August 2018

Tun da Sauran Mutunci, APC ta yi kira ga shugaban majalisar dattijai ta kasa Dr Bukola Saraki da yayi murabus daga mukaminsa

Tun da sauran mutunci, ka yi koyi da Akpabio kaima ka sauka APC ga Saraki.



- Bukola Saraki na cigaba da shan guma-guman suka daga bangarori da dama



- Reshen jam'iyyar APC na jihar Kwara yayi kira gare shi da ya sauka daga mukaminsa tun ana shaida juna



- Wanda hakan ke nufin akwai wani mataki da zasu dauka nan gaba idan yaki amsa kiran



Jam’iyyar APC reshen jihar Kwara ta yi kira ga shugaban majalisar dattijai ta kasa Dr Bukola Saraki da yayi murabus daga mukaminsa.



Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar Bashir Bolarinwa ne yayi wannan kiran a birnin Ilorin jiya Asabar.



Inda ya bayyana cewa ya kamata Bukola Sarakin yayi koyi da takwaransa shugaban marasa rinjaye Sanata Godswill Akpabio, wanda ya sauka daga mukaminsa bayan ya sauya sheka zuwa APC.



A cewarsa tunda dai har yanzu APC ce ke da rinjaye a majalisar, tabbas ya kamata ya nuna halin da’a da dattako ya sauka daga mukaminsa. Bolarinwa ya kara da cewa “Duk wani mai rike da mukamin hidimtawa al’umma ya zama dole ya rika martaba nauyin da ya rataya a kansa”.



“Mai makon koyi na kwarai da irin yadda Akpabio yayi, Saraki ya buge da kokarin tunzura mutane don bijiro da kiyayya ga gwamnatin tarayya ta hanyoyi da dama, amma duk sun gaza kaiwa ga nasara”. Daga karshe Bolarinwa ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC ta jihar na goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari dari-bisa-dari.

No comments:

Post a Comment

Pages