Home of Hausa Novels and Arewa Hot Musics.

We rule the Arewa.

Monday, 13 August 2018

Mummunar musayar wuta da ‘yan bindiga, ‘yan sanda 4 sun rasu a Kaduna

Mummunar musayar wuta da ‘yan bindiga, ‘yan sanda 4 sun rasu a Kaduna.


- Kwanakin baya ma a birnin tarayya wasu 'yan bindigar suka harbe jami'an 'yan sanda 7 tare da yin awon gaba da bindigunsu Kwanan wasu ‘yan sanda hudu da suke kan hanyarsu ta zuwa sintiri ya kare a wata zazzafar musayar wutar da suka yi da wasu wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne a kauyen Jankasa dake yankin Rigasa na karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.



Jami'an ‘yan sandan sun hadu da ajalinsu da misalin karfe bakwai na yammacin jiya Asabar a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa sintiri. Jim kadan da yin kicibis din nasu ne suka fara musayar wuta a tsakaninsu da barayin wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan ‘yan sandan guda hudu.



 ‘yan sanda na jihar Kaduna Yakubu Sabo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce “Da misalin karfe bakwai na yammacin ranar Asabar ne, jami'an rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna, suka yi musayar wuta tsakaninsu da wasu barayi a kauyen Jankasa dake yankin Rigasa a karamar hukumar Igabi, wanda hakan ya zama silar rasa rayukan jami’ai hudu"



Sai dai har ya zuwa yanzu dai babu rahoton kamo wadannan barayin da suka tafka wannan aika-aika duk kuwa da

No comments:

Post a Comment

Pages